Kwamitin zartarwa na ƙasa na Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (Arewa Consultative Forum, ACF) ya dakatar da shugaban kwamitin amintattu (BoT) na ƙungiyar, Alhaji Bashir Ɗalhatu (Wazirin Dutse), bisa zargin rashin gaskiya wajen harkokin kuɗi da kuma karya kundin tsarin mulki.
NEC ta dakatar da Ɗalhatu ne a yau Laraba yayin wani taron gaggawa da aka gudanar a Kaduna, wanda wakilai daga jihohin arewa 18 da Babban Birnin Tarayya (FCT) suka halarta.
Da yake magana da manema labarai bayan taron, kakakin ACF, Tukur Muhammad Baba, ya ce an sauya wurin taron NEC ne bayan da ‘yan sanda suka rufe sakatariyar ƙungiyar da ke Titin Sokoto.
Sai dai kakakin ‘yan sanda na Kaduna, Mansir Hassan, ya ce an rufe sakatariyar ne domin hana yiwuwar rikicewar doka da oda.
Rikicin da ke cikin ƙungiyar ya biyo bayan saɓani kan wa’adin mulkin wasu jami’ai.
Matsalar ta fara ne lokacin da Ɗalhatu ya nuna damuwa kan ƙarewar wa’adin wasu masu riƙe da muƙamai, ciki har da Babban Sakataren ACF, Alhaji Murtala Aliyu (Matawallen Gombe).
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ɗalhatu ya ambaci tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ACF, wanda ya tanadi wa’adi guda ɗaya na shekaru shida ga membobin BoT, yayin da membobin NEC ke da wa’adin shekaru uku wanda za a iya sabunta shi sau ɗaya.
Ya ƙara da cewa BoT ta riga ta karɓi wata takarda daga “membobi da abin ya dama” wadda ke zargin karya kundin tsarin mulki.
Ɗalhatu ya ce an tattauna batun a wani taron BoT da aka gudanar ranar 23 ga Afrilu, 2026, inda aka yanke hukuncin cewa wa’adin jami’an da suka fara aiki a watan Maris na 2020 ya ƙare a ranar 10 ga Maris, 2026.
Ya lissafa waɗanda abin ya shafa da suka haɗa da F. Orti, Mataimakin Shugaban BoT, Ibrahim Sule, Mataimakin Shugaban BoT, Ibrahim Ida, Mataimakin Shugaban NEC, da Murtala Aliyu, Babban Sakatare.
A cewar Ɗalhatu, an tsawaita wa’adin Aliyu zuwa ranar 15 ga Mayu, 2026, domin ba da damar miƙa mulki cikin sauƙi, amma ya ƙi sauka daga muƙamin sa.
Ya bayyana cewa Murtala Aliyu ne kaɗai daga cikin jami’an da abin ya shafa ya ƙi amincewa da matakin.
“A wani yanayi mai ɗaure kai, Malam Murtala Aliyu, wanda yanzu yake shekarar sa ta bakwai a matsayin Babban Sakatare, ya ƙi amincewa da hukuncin kuma yana ci gaba da riƙe da muƙami,” inji Ɗalhatu.
Ya kuma ce an yi ƙoƙarin sasanta rikicin cikin lumana, ciki har da wani taron dattawa da Haliru Aƙilu da Mahmud Ahmed suka shirya ranar 21 ga Afrilu, 2026.
Ɗalhatu ya kuma zargi Aliyu da ƙara rura wutar rikicin ta hanyar kiran taron gaggawa na NEC a ranar 6 ga Mayu domin soke hukuncin BoT.
Duk da zarge-zargen da ake yi masa, Ɗalhatu ya musanta zargin karkatar da kuɗaɗe, yana mai cewa an gudanar da kuɗaɗen asusun tallafin ACF cikin gaskiya da bayyana gaskiya.
Da yake mayar da martani ga zargin, Malam Murtala Aliyu, wanda tsohon Ƙaramin Ministan Wutar Lantarki da Ƙarafa ne, ya ce har yanzu wa’adin sa yana nan daram, yana mai dogaro da bin ƙa’ida da kuma takardun sake naɗa shi.
Ya ce: “An naɗa ni a matsayin Sakatare a watan Maris na 2020, aka rantsar da ni a watan Agusta na 2020, aka sake zaɓe na a watan Yuli na 2023, sannan aka sake rantsar da ni a watan Disamba na 2023. Ina da takardun da ke tabbatar da duk waɗannan.”
Ya ƙara da cewa sake zaɓen sa a shekarar 2023 ya sabunta wa’adin sa, wanda ya sa zargin cewa wa’adin sa ya ƙare bai dace ba.







