• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

ICPC ta ƙalubalanci sabuwar buƙatar beli da El-Rufai ya gabatar yayin da kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 13 ga Mayu

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
May 5, 2026
in Labarai
A A
0
ICPC ta ƙalubalanci sabuwar buƙatar beli da El-Rufai ya gabatar yayin da kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 13 ga Mayu
Malam Nasir El-Rufa'i

Malam Nasir El-Rufa'i

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta, wato ICPC, ta shigar da wata takardar martani domin ƙalubalantar sabuwar buƙatar beli da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya gabatar a shari’ar da ake yi a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna.

A zaman sauraron ƙarar da aka ci gaba da yi a yau Talata, lauyan wanda ake ƙara, Mista Ubong Akpang, ya sanar da kotun cewa akwai wata buƙatar beli da aka gabatar, yana mai jaddada cewa batun ya shafi ‘yancin wanda ake ƙara.

Ya ƙara da cewa an kammala gabatar da dukkan takardun da ake buƙata tare da miƙa su yadda ya dace, yana mai bayyana shirin su na ci gaba da sauraron ƙarar.

Sai dai lauyan ICPC, Mista Ibrahim Mukhtar, ya shaida wa kotun cewa yanzu ne kawai aka ba shi ƙarin takardar rantsuwar da wanda ake ƙarar ya gabatar don goyon bayan buƙatar belin, kuma zai buƙaci lokaci domin nazarin sababbin takardun.

Bayan wannan matsayar, sai kotun mai girma ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 13 ga Mayu, 2026 domin sauraron buƙatar belin.

Idan kun tuna, kotun ta riga ta ƙi bai wa El-Rufai beli a wata buƙatar da aka gabatar a baya.

Mai Shari’a D.H. Khobo ya bayyana cewa wanda ake ƙarar bai gabatar da ƙarin takardar rantsuwa ba domin ƙalubalantar martanin ICPC, wadda ta ƙunshi wasu sababbin bayanai.

Waɗannan bayanai sun haɗa da yiwuwar tserewa saboda tasirin sa da albarkatun da yake da su, zargin hana jami’ai gudanar da kamar sa a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, ƙin miƙa takardun tafiyar sa da na’urorin sa domin bincike, da kuma damuwa kan yiwuwar katsalandan ga shaidu da hujjoji.

A hukuncin da ta yanke, kotun ta jaddada cewa bayar da beli yana ƙarƙashin ikon kotu ne kuma dole ne ya kasance cikin muradun adalci.

Mai Shari’a Khobo ya ce matsayin wanda ake ƙarar a cikin al’umma na iya ba shi damar yin katsalandan ga binciken da ake yi, musamman ganin cewa har yanzu akwai wasu da ake zargi da ba a kama ba.

Kotun ta lura cewa wanda ake ƙarar bai ƙalubalanci manyan zarge-zargen da ke cikin takardar martanin masu gabatar da ƙara ba, saboda haka aka ɗauke su a matsayin amintattu. Haka kuma kotun ta yi watsi da iƙirarin rashin lafiya da aka gabatar ba tare da hujjoji ba.

Saboda haka, kotun ta ƙi bai wa wanda ake ƙarar beli, tare da umurtar a ci gaba da tsare shi a hannun ICPC har zuwa lokacin da za a fara shari’ar, sannan ta bayar da umurnin gaggauta sauraron ƙarar.

Duk da haka, lauyoyin masu kare El-Rufai sun ci gaba da gabatar da sabuwar buƙatar beli.

Tun daga lokacin, ICPC ta shigar da martanin ta na adawa da sabuwar buƙatar belin, tana mai jaddada aniyar ta ta tabbatar da an yi adalci bisa tanadin doka.

Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ICPC, J. Okor Odey, ya bayyana a cikin wata sanarwar manema labarai cewa hukumar tana tabbatar wa da jama’a da ci gaba da jajircewar ta wajen gurfanar da masu laifin cin hanci cikin ƙwarewa tare da tabbatar da bin doka da ƙa’ida.

Tags: El-RufaiICPCshari'a
Previous Post

Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris

Next Post

ACF ta dakatar da shugaban kwamitin amintattu, Bashir Ɗalhatu bisa zargin rashin gaskiya

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
ACF ta dakatar da shugaban kwamitin amintattu, Bashir Ɗalhatu bisa zargin rashin gaskiya

ACF ta dakatar da shugaban kwamitin amintattu, Bashir Ɗalhatu bisa zargin rashin gaskiya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!