Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ta yanke wa tsohon muƙaddashin Akanta-Janar na Tarayya, Mista Chukwunyere Anamekwe Nwabuoku, hukuncin ɗaurin shekaru 72 a gidan yari kan badaƙalar Naira miliyan 868.46.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin ta shafin ta na X (wanda a da ake kira Twitter), Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Mista Nwabuoku bisa laifin wanke kuɗaɗe, bayan kotu ta same shi da laifi a duk tuhume-tuhumen da ake masa.
“Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon muƙaddashin Akanta-Janar na Tarayya, Chukwunyere Anamekwe Nwabuoku, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan laifin wanke kuɗaɗe da ya kai Naira miliyan 868.46, inda aka same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 72 a gidan yari,” inji hukumar.
A cewar EFCC, laifin ya saɓa wa sashe na 18 na Dokar Hana Wanke Kuɗaɗe ta shekarar 2011 (wadda aka gyara da Dokar lamba ta 1 ta 2012), kuma ana hukunta shi a ƙarƙashin sashe na 15(3) na dokar.
Hukumar ta ce Mista Nwabuoku ya aikata laifukan ne yayin da yake aiki a matsayin Daraktan Kuɗi da Asusun Ma’aikatar Tsaro tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021.
Tsohon Akanta-Janar ɗin ya gabatar da buƙatar cewa babu hujjar tuhuma a kan sa, amma kotu ta yi watsi da ita a watan Nuwamba 2025.
An naɗa Mista Nwabuoku a matsayin muƙaddashin Akanta-Janar na Tarayya ne a ranar 20 ga Mayu, 2022, ta hannun marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, bayan dakatar da Mista Ahmed Idris bisa zargin badaƙalar Naira biliyan 80.
Sai dai an tsige shi daga muƙamin a watan Yuli 2022, bayan makonni kaɗan da karɓar aiki, sakamakon rahotannin cewa EFCC tana binciken sa.
Shi ne sabon fitaccen mutum a cikin manyan mutane da aka yanke wa hukunci, bayan da a makon da ya gabata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon Manajan Darakta na Bankin Fitar da Kayayyaki na Nijeriya (NEXIM), Mista Robert Orya, hukuncin ɗaurin shekaru 490 a gidan yari bayan samun sa da laifi a badaƙalar Naira biliyan 2.4.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafin ta na X a ranar Alhamis, hukumar yaƙi da cin hanci ta tabbatar da cewa Mai Shari’a F.E. Messiri na Kotun Abuja ya yanke wa tsohon shugaban NEXIM ɗin, wanda ya yi aiki daga 2011 zuwa 2016, hukuncin ɗaurin shekaru 10 kan kowanne daga cikin tuhume-tuhume 49 da ake masa a shari’ar badaƙalar Naira biliyan 2.4.







