Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutum goma a wani mummunan haɗari da ya faru a yau Litinin a yankin Tafa na Jihar Neja.
Muƙaddashiyar Jami’ar Wayar da Kai ta hukumar FRSC ta ƙasa da ke Abuja, Kwamanda Felicia Kalu, ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa lamarin “ya nuna irin mummunan sakamakon rashin bin dokokin tsaro, musamman wuce ƙa’idar gudu da aka ƙayyade da kuma ɗaukar fasinjoji tare da kaya a mota guda.”
A cewar ta, haɗarin dai ya faru ne da misalin ƙarfe 8:20 na safe a kan hanyar Tafa zuwa Gujeni, a ƙauyen Malam Tanko, inda wata tirela ƙirar DAF mai lambar rajista FKY136XD ta faɗi yayin da take ɗauke da mutane maza 33.
Binciken farko ya nuna cewa mutane 10 sun mutu, yayin da 20 suka samu raunuka iri-iri, sannan aka ceto uku ba tare da wani rauni ba.
Shaidu sun nuna cewa haɗarin ya faru ne sakamakon wuce ƙa’idar gudu, wanda ya janyo rashin iya sarrafa abin hawa.

Felicia Kalu ta ce: “Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda aka yi amfani da motar wajen aikata haramtacciyar hanya mai haɗari ta ɗaukar kaya da mutane a lokaci guda—abin da hukumar ke ta jan kunne a kai saboda munanan illolin sa.”
Jami’an FRSC sun kai ɗauki cikin gaggawa bayan samun kiran neman taimako, inda suka samu nasarar ceto mutane 23 da rai, tare da kawar da cunkoso domin dawo da zirga-zirgar ababen hawa yadda ya kamata.
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Umaru Musa Yar’Adua da ke Sabon Wuse domin samun kulawa, yayin da aka ajiye gawarwakin mamatan a ɗakin ajiye gawa na asibitin.
Babban Kwamandan hukumar, Shehu Mohammed, ya bayyana matuƙar damuwa kan lamarin, yana mai cewa hatsarin abin kaucewa ne kuma darasi mai raɗaɗi kan illar keta dokokin hanya.
Ya jaddada cewa babu wata tafiya da ta fi darajar rayuwar ɗan’adam, kuma ya yi Allah-wadai da yadda wasu masu amfani da hanya suke ci gaba da yin watsi da shawarwarin tsaro.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta ƙara tsaurara dokoki da kuma wayar da kan jama’a domin daƙile wuce ƙa’idar gudu da kuma kawar da matsalar haɗa fasinjoji da kaya a manyan hanyoyin ƙasar nan.
Babban Kwamandan ya miƙa ta’aziyyar sa ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa.

Kalu ta ce: “Saboda haka, ana shawartar masu harkar sufuri da direbobi da su bi dokokin tsaro, su kiyaye gudun da aka ƙayyade, kuma su guji amfani da motocin da ba su dace da ɗaukar fasinjoji ba.
“Ana kuma roƙon jama’a da su kasance masu lura da tsaro a kowane lokaci, domin tsaron hanya alhakin kowa ne.”







