• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 61 a Borno

Wakilin Mu by Wakilin Mu
March 18, 2026
in Tsaro
A A
0
Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 61 a Borno
Sojojin Nijeriya

Sojojin Nijeriya

Dakarun Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 61 a Malam Fatori da ke da ke Ƙaramar Hukumar Abadam a Jihar Borno.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da ‘yan ta’addan suka yi ƙoƙarin kutsa kai cikin sansanin sojin da ke garin Malam Fatori.

Wani rahoton da Zagazola Makama ya fitar wanda babban mai bai wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan dabaru da watsa labarai, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafin sa na X, ya ce lamarin ya auku ne a lokacin da ‘yan ta’addan suka nemi kutsawa cikin sansanin soji a Malam Fatori.

Rahoton ya ambato majiyoyin tsaro suna cewa ‘yan ta’addan sun ƙaddamar da harin da sanyin safiyar yau Laraba ne inda suka nufi sansanin sojin da ƙafa kuma suka yi amfani da jirage mara matuƙa a wani yunƙuri na karya katangar sansanin sojin da ƙarfin hali.

Sai dai martani mai ƙarfi na haɗin gwiwa da dakarun ƙasa da na sama suka yi ya fi ƙarfin ‘yan ta’addan.

Kazalika wata sanarwar da daraktan hulɗa da jama’a da watsa labarai na rundunar sojin saman Nijeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar kuma Usman Kukasheka, tsohon kakakin sojin Nijeriya ya wallafa a shafin sa na Facebook, ta tabbatar da aikin da sojin saman ta yi a Malam Fatori.

“Aikin na haɗin gwiwa ya yi nasarar hana masu tayar da ƙayar bayan karya katangun tsaro, lamarin da ya ƙarfafa ƙoƙarin da ake yi na daidaita lamurra a garuruwan da ke kan iyakoki,“ inji sanarwar.

Tags: BokoHaramBornoMalamFatorisojojita'addanci
Previous Post

CAF ta ƙwace kofin zakarun AFCON na 2025 daga Senegal, ta bai wa Morokko

Next Post

Kamfanin MTN ya biya Sarkin Kano Lamiɗo Sanusi naira miliyan 442 ladar matsayin darakta

Related Posts

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma
Tsaro

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma

April 25, 2026
Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos
Tsaro

Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos

April 17, 2026
‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya
Tsaro

‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya

April 16, 2026
Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su
Tsaro

Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su

April 15, 2026
Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba – Gwamnatin Tarayya
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta kare harin jirgin sama a Jilli, ta ba da umurnin bincike

April 14, 2026
An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno
Tsaro

An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno

April 13, 2026
Next Post
Kamfanin MTN ya biya Sarkin Kano Lamiɗo Sanusi naira miliyan 442 ladar matsayin darakta

Kamfanin MTN ya biya Sarkin Kano Lamiɗo Sanusi naira miliyan 442 ladar matsayin darakta

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!