An kashe jagoran koli na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a wani hari da Isra’ila da Amurka suka kai. Ya rasu yana da shekaru 86.
Kafofin watsa labaran gwamnatin Iran sun tabbatar da mutuwar sa da sanyin safiyar yau Lahadi, bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa an kashe Khamenei ne a wani harin sama na haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila da ya auka gidan sa a jiya Asabar.
“An sanar da al’ummar Iran cewa Mai Girma Babban Ayatollah Imam Sayyid Ali Khamenei, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, ya yi shahada a harin haɗin gwiwa da Amurka da gwamnatin Sahyoniyawa suka kai da safiyar Asabar, 28 ga Fabrairu,” inji kamfanin dillancin labarai na Tasnim mai alaƙa da gwamnati.
Kafofin gwamnati sun kuma ce an kashe ɗiyar sa, surukin sa da jikan sa a harin.
Tun da fari, Trump ya ce Khamenei da wasu jami’an Iran “ba su iya tserewa daga bayanan sirrin Amurka da ingantattun na’urorin bibiyar diddigi ba.”
Shi dai Khamenei, ya karɓi ragamar mulki a Iran ne a 1989 bayan rasuwar Ayatollah Ruhollah Khomeini, jagoran da ya jagoranci juyin juya halin Musulunci shekaru goma kafin haka.
Duk da cewa Khomeini shi ne ginshiƙin aƙidar juyin juya halin da ya kawo ƙarshen mulkin sarautar Pahlavi, Khamenei ne ya gina ƙarfin soja da na rundunonin sa-kai da suka zama ginshiƙin tsaron Iran da kuma tasirin ta a waje.
Kafin ya zama jagoran ƙoli, sai da ya shugabanci Iran a matsayin shugaban ƙasa a lokacin yaƙin zubar da jini da Iraƙi a shekarun 1980. Wannan yaƙi mai tsawo, tare da jin kaɗaici da dama daga cikin ‘yan Iran suka ji yayin da ƙasashen Yamma ke goyon bayan Saddam Hussein, ya ƙara zurfafa rashin yarda da ƙasashen Yamma da Amurka a zuciyar sa, inji masana.
Wannan ra’ayi ne ya zama ginshiƙin mulkin sa na tsawon shekaru da ya tabbatar da cewa Iran dole ta kasance cikin shiri na kare kan ta daga barazanar waje da cikin gida.
Wasu na kallon Iran a matsayin mai mulkin addini kawai, amma a zahiri Khamenei shugaba ne da ya fito daga yanayin yaƙi, wanda ya ɗauki cewa Iran na cikin haɗari kuma tana buƙatar tsaro mai ƙarfi.
A ƙarƙashin wannan hangen nesa, Rundunar Kare Juyin Juya Hali ta Musulunci (IRGC) ta zama babbar cibiyar tsaro, siyasa da tattalin arziki, tare da faɗaɗa tasirin Iran a yankin.
Mulkin sa ya fuskanci manyan ƙalubale, ciki har da zanga-zangar 2009 bayan zaɓen da aka ce an tafka maguɗi, da kuma zanga-zangar 2022 kan haƙƙoƙin mata. A lokuta da dama, hukumomi sun murƙushe masu zanga-zanga da ƙarfi.
An haifi Khamenei a 1939 a birnin Mashhad mai tsarki a arewa maso gabashin Iran. Ya yi karatun addini tun yana ƙarami, kuma daga bisani ya shiga gwagwarmayar adawa da sarautar Pahlavi. An kama shi sau da dama tare da tura shi gudun hijira kafin juyin juya halin 1979.
Bayan kifar da mulkin sarauta, ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa sabuwar Iran, inda ya riƙe muƙaman ministan tsaro da kuma jagoran sallar Juma’a a Tehran. A 1981, ya tsira daga yunƙurin kashe shi, amma ya rasa yin amfani da hannun sa na dama. A wannan shekarar ne kuma ya zama shugaban ƙasa.

Bayan rasuwar Khomeini a 1989, majalisa ta naɗa shi jagoran ƙoli, duk da cewa bai cika sharuɗɗan addini mafi girma ba a lokacin. Duk da haka, jagorancin sa bai kasance na alama kawai ba.
Ya mayar da hankali wajen gina ƙarfin soja da tsarin “tsayin daka” ga Yamma, tare da haɗa kai da ƙungiyoyin ƙawance a yankin wanda ake kira “axis of resistance”. Wannan ya hada da ƙungiyoyi a Lebanon, Syria, Falasdinu da Yemen.
A 2015, ya amince da yarjejeniyar nukiliya da ƙasashen duniya (JCPOA) domin rage takunkumi, amma Amurka ta fice daga yarjejeniyar a 2018 a ƙarƙashin Trump, lamarin da ya sake tsananta rikici.
A cikin shekarun baya-bayan nan, takunkumi mai tsanani da hauhawar farashi sun haddasa zanga-zanga a faɗin ƙasar, wacce aka murƙushe da ƙarfi.

A ranar 28 ga Fabrairu, Trump ya ba da sanarwar fara “babban aikin soji” a Iran, yana mai kira ga canjin gwamnati.
“Lokacin ‘yancin ku ya zo,” inji Trump lokacin da yake jawabi ga al’ummar Iran. “Idan muka gama, ku karɓi mulkin ku — naku ne.”
Mun fassaro daga rahoton Al Jazeera







