Shugaba Donald Trump na Amurka ya shafe sa’o’i uku yana ganawa da takwaran sa Vladimir Putin na Rasha, yayin wata ziyara da Putin ɗin ya kai Amurka, a ranar Juma’a.
An yi wannan ganawa ce a Sansanin Sojojin Musamman na Amurka da ke Barikin J.B.E Richardson, a Anchorage, babban birnin Jihar Alaska.
Wannan ne karo na farko da Putin ya kai ziyara Amurka, wadda ya je ne bisa gayyatar Trump, kuma babban dalilin shi ne domin ganawar ido-da-ido don kawo ƙarshen yaƙin Rasha da maƙwabciyar ta Ukraniya.
Yaƙin, wanda ya ɓarke tun cikin 2022, ya zama alaƙaƙai wajen kawo naƙasu ga tattalin arzikin ƙasashen Turai da wasu sassa na duniya. Kuma ya yi wa Ukraniya mummunar illar da za ta shafe tsawon shekaru masu yawa kafin ta dawo hayyacin ta.
Bayan shafe sa’o’i uku, shugabannin biyu sun tashi daga taron, wanda tun da farko an tsara cewa za su shafe tsawon sa’o’i bakwai suna tattauna.
Tashin su ke da wuya sun fuskanci taron manema labarai, inda kowanen su ya jinjina wa kowa, tare da cewa sun ci nasara sosai a ganawar, wadda ba su bayyana irin takamaimai ɗin nasarar ba, wadda kowa ke jiran ya ji sun yi bayani kan tsagaita wuta ko sulhu tsakanin Rasha da Ukraniya.
A nasa jawabin, Putin ya ce ya yi amanna da iƙirarin da Trump ya yi cewa da shi ya ci zaɓen Amurka a 2020, ba Joe Biden ba, to da ya yi ƙoƙarin ganin yaƙi bai ɓarke tsakanin Rasha da Ukraniya ba.
Sai dai kuma ya ce sulhu tsakanin ƙasar sa da Ukraniya ba zai yi wani tasiri ba, har sai an kawo ƙarshen musabbabin dalilin da ya sa ya mamaye Ukraniya.
Putin a gaban ‘yan jaridu ya gargaɗi gwamnatin Ukraniya da Tarayyar Turai cewa kada su kuskura su yi wa ƙoƙarin sulhun da ake yi zagon-ƙasa.
A nasa ɓangaren, Trump ya ce tabbas sun samu ci gaba da kuma fahimtar juna a zaman su na tsawon sa’o’i uku.
“Yanzu aka fara wannan ganawa ido-da-ido, kuma mun fahimci juna cikin kyawawan zukata. Ƙoƙarin shiga tsakani ne na mu. Saura kuma ya rage wa tsakanin ƙasashen su biyu a yi sulhu na dindindin, mai ɗorewa, ba wai tsagaita wuta ba.” Inji Trump, yayin da yake ƙara cewa ya fahimci dalilan da ya sa Putin ya mamaye Ukraniya, domin kare muradun ƙasar sa daga katsalandan ɗin barazanar tsaro da zai iya fuskanta daga wasu ƙasashe.
Ya faɗi hakan ne bayan da Putin ya shaida wa manema labarai cewa ya afka wa Ukraniya da yaƙi ne domin ta tattago ƙungiyar Ƙawancen Taron-dangi ta NATO, wato Turawan Yamma, ta nemi ta shiga cikin su, domin su kafa sansani a Ukraniya, mai maƙautaka da Rasha, a yankin su na Turai ta Gabas.
Har aka kammala ganawa da manema labaran dai shugabannin biyu ba su bari an yi masu tambayoyi ba.
Kafin su bar wurin, su biyun sun ƙara gaisawa da juna, inda Putin ya dubi Trump ya ce masa, “tattauna ta kai ta gaba kuma a Moscow za mu yi ta.”
Trump ya dube shi ya ce, “abu ya yi kyau, amma zan duba na yi nazarin wannan ziyara tawa. Tabɗijan!”
A ƙarshe Trump ya ce zai so a yi ganawa tsakanin su uku, wato a gayyaci har da shugaban Ukraniya Vilodimir Zelensky.





