Shugabannin yankin Arewa-maso-gabas sun ƙara bayyana goyon bayan su ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sake tsayawa takara a zaɓen 2027, tare da alƙawarin tattara ƙuri’un yankin ga jam’iyyar APC.
Gwamnoni, ministoci, ’yan majalisa, sarakuna da dattawan jihohin Borno, Adamawa, Bauchi, Gombe, Taraba da Yobe ne suka kai wa Tinubu ziyarar godiya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ziyarar ta biyo bayan matakin Tinubu na sake zaɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takarar sa.
Gwamnan Borno kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa-maso-gabas, Farfesa Babagana Zulum, ya ce matakin ya nuna yadda Shugaban Ƙasa yake daraja biyayya, ƙwarewa da sadaukarwa.
Ya ce ci gaba da barin Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa ya ƙara wa yankin ƙwarin gwiwa.
Zulum ya yaba wa gwamnatin Tinubu kan ayyukan hanyoyi, noma, ilimi, tallafa wa matasa da kula da ’yan gudun hijira da take yi a yankin.
Ya tabbatar wa Shugaban Ƙasa cewa shugabanni da magoya bayan APC a Arewa-maso-mabas za su haɗa kai domin tabbatar da nasarar Tinubu da sauran ’yan takarar jam’iyyar a 2027.
Da yake mayar da martani, Tinubu ya ce goyon bayan da yankin ya nuna abin faranta rai ne, yana mai jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da inganta tattalin arziki, tsaro da hanyoyin mota.
Ya ce haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya da jihohi yana da muhimmanci wajen yaƙi da ta’addanci da fashi da makami, tare da tabbatar da zaman lafiya da walwalar ’yan Nijeriya.







