Al’ummar Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara sun yi alkawarin goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Dauda Lawal da sauran ’yan takarar jam’iyyar APC a babban zaɓen 2027.
Wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa da na Gwamnan Jihar Zamfara na APC, Dakta Sani Ahmed Sambo, ya sanya wa hannu a ranar Asabar, ta bayyana cewa an yi wannan alƙawari ne a jiya, yayin wani gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na APC a Shinkafi, inda magoya bayan jam’iyyar da mazauna yankin suka fito ƙwan su da kwarkwatar su domin tarbar tawagar yaƙin neman zaɓen.
Al’ummar yankin, waɗanda suka yaba wa gwamnatin Dauda Lawal kan ayyukan cigaban da take gudanarwa, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, ƙarfafa mata da matasa, sun bayyana cewa gwamnan ya cancanci sake samun wa’adi na biyu domin ƙarfafa nasarorin da gwamnatin sa ta samu.
Da yake magana a madadin al’ummar yankin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Shinkafi, Hon. Ibrahim Musa, tare da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Mahmud Aliyu Shinkafi, da Hon. Bello Hassan Shinkafi, sun yaba wa gwamnatin jihar kan abin da suka bayyana a matsayin jajircewar ta wajen inganta rayuwar al’umma.

Sun bayyana gamsuwar su da shirye-shiryen ci gaban da gwamnatin ke aiwatarwa, tare da yin alƙawarin tattara gagarumin goyon baya ga Tinubu, Lawal da dukkan ’yan takarar APC a zaɓe mai zuwa.
Da yake jawabi ga mahalarta taron, Gwamna Lawal ya buƙaci al’ummar Shinkafi da sauran sassan jihar da su kaɗa ƙuri’un su ga APC baki ɗaya a zaɓen 2027, domin ci gaba da ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa.
Ya ce sake ba shi wa’adi zai bai wa gwamnatin sa damar ƙarfafa nasarorin da ta samu da kuma faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi, ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya, shirye-shiryen ƙarfafa mata da matasa, da sauran muhimman fannoni.
Gwamnan ya sake jaddada aniyar sa ta aiwatar da Ajandar Ceto Zamfara mai Shikashikai Shida (Six-Point Rescue Mission Agenda), yana mai cewa inganta rayuwar al’umma da samar da makoma mai albarka ga Jihar Zamfara na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sanya a gaba.
Ya kuma gode wa al’ummar Shinkafi bisa fitowar da suka yi da kuma ci gaba da goyon bayan da suke bai wa gwamnatin sa, inda ya buƙace su da su nuna irin wannan amincewa ga Shugaba Tinubu da sauran ’yan takarar APC.
Shi ma da yake jawabi, Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Abubakar Yari, ya bayyana tabbacin sa kan nasarar da jam’iyyar za ta samu a zaɓen 2027.
Yari ya ce nasarorin cigaban da gwamnatin Gwamna Lawal ta samu sun samar da ingantaccen tubali ga nasarar APC a zaɓe a faɗin jihar.
Ya buƙaci masu zaɓe da su goyi bayan Tinubu, Lawal da sauran ’yan takarar APC, yana mai cewa zaɓen jam’iyyar a dukkan matakai zai taimaka wajen tabbatar da ci gaba da manufofi, zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma samun cigaba mai ɗorewa.
Tsohon gwamnan ya yi tsokaci kan ayyukan tallafi da gwamnatin Tinubu ta aiwatar a Zamfara, musamman a fannonin samar da ababen more rayuwa, haɗin gwiwar tsaro, noma da ƙarfafa al’umma a matakin ƙananan hukumomi.
Haka kuma, Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC na jihar, Alhaji Salisu Mai Buhu, wanda Dakta Lawal M. Liman Gabɗon Ƙaura ya wakilta, ya yi kira ga al’ummar yankin da su goyi bayan dukkan ’yan takarar APC a zaɓen 2027.
Ya bayyana nasarorin da gwamnatocin APC suka samu a matakin tarayya da na jiha, yana mai jaddada cewa ci gaba da mulkin jam’iyyar ya zama wajibi domin ɗorewar shirye-shiryen cigaba da kuma inganta muradun al’umma.
Gangamin ya samu halartar shugabannin APC, masu ruwa da tsaki, mambobi da magoya bayan jam’iyyar daga dukkan ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara.






