Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya gana da malaman addinin Musulunci sama da 2,000 daga ƙananan hukumomi 13 na Kano ta Arewa, inda ya buƙace su da su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran ’yan takarar jam’iyyar APC baya a zaɓen 2027.
A taron da aka gudanar a Kano ranar Litinin, Barau ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana da kyakkyawar niyya ga Jihar Kano, Arewa maso Yamma da Arewacin Nijeriya baki ɗaya.
Ya buƙaci malaman da su taimaka wajen wayar da kan al’umma game da ayyukan raya ƙasa da gwamnatin tarayya ke gudanarwa, yana mai cewa ya kamata a sanar da jama’a irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin gwamnatin.
Sanata Barau ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta amince da sauya matsayin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Kabo zuwa jami’a, tare da ɗaukaka matsayin Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano zuwa jami’a.
Ya kuma ambaci kafa makarantun horas da jami’an ’yan sanda, Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) da Hukumar Shige da Fice a matsayin wasu daga cikin cibiyoyin da aka samar wa jihar.

Haka kuma, ya ce kafa Hukumar Raya Arewa maso Yamma (NWDC) na daga cikin matakan da Shugaba Tinubu ya ɗauka domin inganta ci gaban yankin.
Sanatan ya ƙara da cewa an samu nasarar jawo ayyukan raya ƙasa da darajar su ta kai kusan naira tiriliyan biyu zuwa Kano bayan komawar Gwamna Abba Kabir Yusuf cikin jam’iyyar APC.
A wani ɓangare na taron, Sanata Barau ya sanar da shirin raba babura 390 ga malamai a ƙananan hukumomi 13 na Kano ta Arewa, a matsayin wani mataki na tallafa musu.
Ya ce za a fara da raba babura 15 ga kowace ƙaramar hukuma, wanda zai kai jimillar babura 195, sannan bayan watanni uku a sake raba wasu 195.
Baya ga baburan, Sanatan ya kuma yi alƙawarin ba kowane malami tallafin kuɗi naira 50,000.
Dangane da matsin tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasar, Sanatan ya amince cewa akwai ƙalubale, amma ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu tana ƙoƙarin shawo kan su, yana mai danganta wasu daga cikin matsalolin da yanayin tattalin arzikin duniya.

Ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ayyukan raya ƙasa da yake gudanarwa a Jihar Kano.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Malamai ta Kano ta Arewa, Malam Lawal Imam, ya yaba wa Sanata Barau bisa gudunmawar da yake bayarwa, musamman wajen gina masallatai da tallafa wa al’ummar yankin.
Ya kuma tabbatar da cewa malaman za su ci gaba da gudanar da addu’o’i domin samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban ƙasa.
Shi ma Shugaban Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC na Kano ta Arewa, Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, tare da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa, sun yaba da taron da kuma ƙoƙarin da ake yi na haɗa kan malaman addini.
A nasa jawabin na godiya, Sanata Barau Jibrin ya jinjina wa malaman bisa addu’o’in su da gudunmawar da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano.







