Dakarun rundunar Operation Haɗin Kai sun kama wasu mutane biyar da ake zargi da aikata garkuwa da mutane tare da ƙwato bindigogi ƙirar gida a wani samame da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri a Jihar Yobe.
An gudanar da samamen ne a jiya Alhamis, 23 ga Yuli, inda dakarun Bataliya ta 233 na Sector 2 Operation Haɗin Kai, tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Maharba ta Jihar Yobe, suka kai farmaki a ƙauyen Jegalari da ke Ƙaramar Hukumar Fune ta jihar.
A wata sanarwa da Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labaran Soji na Operation Haɗin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce an ƙaddamar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan wasu da ake zargin masu aikata laifuffuka ne da ke addabar yankin.
A yayin samamen, dakarun sun kama mutane biyar da ake zargi da garkuwa da mutane, sannan suka ƙwato bindigogi uku ƙirar gida masu kama da AK-47, bindiga ƙirar gida guda ɗaya, harsasai iri-iri, da kuma wayoyin hannu huɗu da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan laifuffukan waɗanda aka kama.
Sanarwar ta ce waɗanda ake zargin suna tsare a hannun sojoji tare da kayan da aka ƙwato, kuma ana ci gaba da bincike domin tantance rawar da suka taka a laifukan garkuwa da mutane da sauran laifuffuka masu alaƙa da hakan.

Rundunar Operation Haɗin Kai ta sake jaddada aniyar ta ta ci gaba da gudanar da ayyukan soji bisa bayanan sirri domin hana ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuffuka samun damar gudanar da ayyukan su a yankin Arewa-maso-gabas.
Har ila yau, rundunar sojin ta buƙaci al’umma su kasance masu sa ido tare da gaggauta kai rahoton duk wani mutum, motsi ko aiki da ke tayar da zargi ga jami’an tsaro mafi kusa da su.
Ta bayyana cewa sahihan bayanai da jama’a ke bayarwa a kan lokaci suna da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin yankin.






