Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa da ’yan Nijeriya cewa sauye-sauyen da gwamnatin sa take aiwatarwa za su samar da wutar lantarki mai ɗorewa.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da shirin horas da matasa 5,000 kan saka mitocin zamani a ƙarƙashin shirin “Presidential Metering Initiative” (PMI), wanda aka yi a Cibiyar Horar da Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Nijeriya (NAPTIN) da ke Abuja.
Ministan Wutar Lantarki, Mista Joseph Tegbe, shi ne ya wakilci Shugaban Ƙasar a taron.
Tinubu ya ce shirin zai taimaka wajen cike giɓin mitoci a ƙasar nan, ƙarfafa fannin wutar lantarki da kuma samar da ayyukan yi ga matasa masu ƙwarewa.
Ya ce hakan na nuna ƙudirin gwamnatin sa na gina muhimman ababen more rayuwa tare da bunƙasa jarin ɗan’adam, yana mai cewa za a ci gaba da faɗaɗa shirin domin bai wa wasu ƙarin matasa dama.
Ya ce, “Sauya fasalin fannin wutar lantarki na Nijeriya ba zai faru cikin dare ɗaya ba. Yana buƙatar daidaito, haɗin gwiwa, ƙwarewar fasaha da jajircewa wajen aiwatar da sauye-sauye.”
Tinubu ya ce gwamnati ba za ta tsaya kan mutum 5,000 ba, domin za a ƙara yawan waɗanda za su ci gajiyar shirin zuwa 10,000, 15,000, har ma da yiwuwar kaiwa 500,000.
“Bayan ƙarfafa fannin wutar lantarki, shirin na PMI yana samar da ayyukan yi masu ma’ana tare da bai wa matasa ƙwarewar fasahar zamani,” inji shi.
Ya jaddada ƙudirin gwamnati na tabbatar da adalci wajen biyan kuɗin wuta da kyautata ayyukan samar da ita.
A cewar sa, kowane ɗan Nijeriya ya cancanci ya biya kuɗin wutar da ya yi amfani da ita kawai, yayin da masu samar da wutar lantarki su ma su samu haƙƙin su.
Shugaban ya ce rukunin farko na waɗanda za a horas zai zama ginshiƙin shirin mitocin zamani na ƙasar nan, domin tabbatar da cewa gidaje da kasuwanni sun samu mitocin da aka girka bisa ƙa’idojin fasaha da tsaro.
Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin makamashi kuma sakatariyar zartarwa ta PMI, Hajiya Olu Verheijen, ta ce gwamnati za ta rarraba mitocin zamani sama da miliyan bakwai, wanda zai kasance mafi girman shirin samar da mitoci a tarihin Nijeriya.
Ta ce, “Mita miliyan bakwai na buƙatar dubban ’yan Nijeriya masu ƙwarewa. Ana iya samun jari da kayan aiki, amma babu ƙasar da ke ci gaba ba tare da ƙwararrun mutane ba.”
Verheijen ta ce duk da wurare 5,000 kacal da aka ware, an karɓi kusan masu neman shiga 220,000 daga matasa a faɗin ƙasar nan.
Ta ce hakan ya nuna cewa akwai ɗimbin matasa da ke shirye su yi aiki idan aka ba su dama.
Ta ƙara da cewa duk wanda ya yi nasarar kammala shirin zai samu horo daga NAPTIN, takardar shaidar ƙwarewa daga Hukumar Kula da Tsaron Ayyukan Wutar Lantarki ta Najeriya (NEMSA), tare da damar samun aiki a kamfanonin rarraba wutar lantarki da masu samar da mitoci.
Shugaban kwamitin PMI kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, wanda Mista Edmund Nnaji ya wakilta, ya buƙaci gwamnatocin jihohi da su mara wa shirin baya.
Babban daraktan NAPTIN, Mista Ahmed Nagode, ya ce manhajar horon ta ƙunshi darussa a aji da horaswa ta aiki, waɗanda Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta amince da su.
Shi ma Ministan Raya Matasa, Mista Ayodele Olawande, ya ce shirin ya dace da manufar ma’aikatar sa ta “Matashi Ɗaya, Ƙwarewa Biyu”, domin yana bai wa matasa dabarun da za su taimaka musu wajen samun aiki, kafa sana’a da dogaro da kai.
Abokan hulɗa da ke tallafa wa PMI sun haɗa da NEMSA, NAPTIN, Bankin Duniya da sauran masu ruwa da tsaki a fannin wutar lantarki.






