Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sauya sunan Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Azare, Jihar Bauchi, zuwa Jami’ar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi (Federal University of Medical Sciences) zuwa Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi University of Medical Sciences, domin girmama fitaccen malami kuma dattijo a Nijeriya, marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi.
Sanarwar sauya sunan ta zo ne a matsayin girmamawa ga irin rawar da marigayin ya taka wajen yaɗa ilimin addini, tarbiyya da zaman lafiya a Nijeriya da ma ƙasashen waje.
Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya shahara wajen koyar da ilimi, da’awa da kuma tsayawa kan gaskiya da haɗin kan al’umma.
A cewar Shugaban Ƙasa, wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na karrama manyan ’yan Nijeriya da suka sadaukar da rayuwar su wajen hidimar al’umma da cigaban ƙasa, musamman a fannonin ilimi da tarbiyya.
Sauya sunan jami’ar ba zai shafi tsari da ayyukan karatu da koyarwa ba, sai dai zai ƙara wa cibiyar daraja tare da ɗora mata nauyin ci gaba da riko da kyawawan halayen da marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya tsaya a kai.







