• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya naɗa Yakubu da ministoci shida a kwamitin warware bashin naira tiriliyan 1.5 da ‘yan kwangila ke bin gwamnati

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
December 14, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Tinubu ya naɗa Yakubu da ministoci shida a kwamitin warware bashin naira tiriliyan 1.5 da ‘yan kwangila ke bin gwamnati

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ƙaƙƙarfan kwamitin da zai warware matsayar ɗimbin bashin da ‘yan kwangila suke bin Gwamnatin Tarayya.

Yayin naɗa kwamitin a ranar Laraba, Tinubu ya bayyana rashin jin daɗi game da tarin bashin da Gwamnatin Tarayya ke bin ‘yan kwangila, tare da kafa babban kwamiti wanda ya ɗora wa gagarumin aikin magance matsalolin da ke hana biyan su, tare umurtar kwamitin ya samar da kuɗin biyan bashin.

Da yake yi wa ‘yan jarida bayani a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) a Abuja, Mashawarcin Shugaban Ƙasa na Musamman kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya ce Shugaban Ƙasar ya nuna damuwa bayan ya samu labarin cewa kusan ‘yan kwangila 2000 ne ke bin Gwamnatin Tarayya bashi.

“Ya bayyana a fili ƙwarai cewa yana so a samu mafita guda ɗaya,” inji Onanuga.

Ya ƙara da cewa, “Muhimmin abin da ya fito a taron FEC shi ne Shugaban Ƙasa ya nuna matuƙar rashin jin daɗi game da yadda ‘yan kwangila ke bin ɗimbin bashin da har yau ba a biya su ba.

“Darakta-Janar na Hukumar Kula da Sayar da Kadarorin Gwamnati (BPP) ya shaida wa Shugaban Ƙasa cewa ‘yan kwangila kusan 2000 na bin bashin kuɗaɗen ayyukan da suka yi. Don haka ministoci za su duba matsalar domin nemo mafita ta gaske da kuma kuɗin da za a yi amfani da su wajen biyan ‘yan kwangila.”

A cewar Onanuga, kwamitin ya ƙunshi Ministan Kuɗi (kuma Mai Kula da Tattalin Arziki), Wale Edun; Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu; Ministan Ayyuka, Dave Umahi; Ministan Ilimi, Olatunji Alausa; Ministan Gidaje, Ahmed Dangiwa; da Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku (Marine & Blue Economy), Gboyega Oyetola; tare da Darakta-Janar na Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya, Tanimu Yakubu; da Shugaban Hukumar Tara Harajiin Cikin Gida ta Tarayya (FIRS), Zacch Adedeji.

“Dukkan su za su zauna su tsara shiri a matsayin kwamiti, su yi taro a matsayin kwamiti, sannan su je wajen Shugaban Ƙasa su gabatar masa da mafitar da suka samo wajen ware kuɗin da za a biya ‘yan kwangila,” inji shi.

Onanuga ya ƙara da cewa Darakta-Janar na BPP ya yi wa Majalisar bayani kan yawa da adadin bashin da aka gada, lamarin da ya sa Shugaban Ƙasa ya bayar da umarni.

Onanuga ya ce: “Manufar ita ce a nemo kuɗi a gyara matsalar biyan ‘yan kwangila. Dole ne mu duba matsalolin: Me ke jawo wannan matsala? Me ya sa FIRS ke cewa ana samun ƙarin kuɗaɗe, amma duk da haka ana bin ‘yan kwangila bashi? Me zai iya zama sanadin haka?

“Shi ya sa ya kafa kwamiti mai ministoci da dama domin duba matsalar. Har ma ya ce a matsayin ƙasa mai cikakken iko, za mu iya zuwa mu karɓo bashi domin biyan ‘yan kwangila. Amma ina ganin zuwa lokacin da mambobin kwamitin suka gana da shi yau, za a samu mafita.”

Jawaban Onanuga sun biyo bayan makonni na matsin lamba daga ‘yan kwangila da suka koka kan jinkirin biyan bashin ayyukan da aka kammala tun cikin 2024.

A farkon watan Satumba, Ƙungiyar ‘Yan Kwangila ‘Yan Asalin Ƙasa ta Nijeriya ta yi zanga-zanga a Ma’aikatar Kuɗi a Abuja, tana iƙirarin cewa sama da Naira tiriliyan 4 na manyan ayyukan babban 2024 da aka tantance har yanzu ba a biya ba; adadin da aka kuma ambata yayin zanga-zangar su a Majalisar Ƙasa.

Ma’aikatar Ayyuka ta amince da tarin bashin tun da wuri, inda ta ƙaddamar da aikin tantancewa a watan Janairu 2024 domin warware kusan Naira tiriliyan 1.5 da ake bi na kwangilolin ayyukan ginin manyan titinan tarayya.

Tags: kwangilaShugaba Bola Ahmed TinubuTanimu Yakubu
Previous Post

Bankwana da 2025: Kamfanin BUA ya yi wa ma’aikata 510 watandar naira biliyan 30

Next Post

CBN ya umurci masu PoS su bi hanyoyin magance yawan tangarɗar tura kuɗaɗe nan da kwana 30

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
CBN ya umurci masu PoS su bi hanyoyin magance yawan tangarɗar tura kuɗaɗe nan da kwana 30

CBN ya umurci masu PoS su bi hanyoyin magance yawan tangarɗar tura kuɗaɗe nan da kwana 30

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!