Kamfanin BUA ya karrama ma’aikatan sa 510 da kyautar kuɗi har sama da Naira biliyan 30. An yi wannan watanda ce a bikin karrama ma’aikatan da suka fi daɗewa suna aiki, wato Night of Excellence and Long Service Awards na 2025, wanda ke ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen bayar da kyaututtuka lada karramawa ga ma’aikata da kamfani mai zaman kan sa a Nijeriya ya taɓa yi.
Bikin ya karrama ma’aikata masu dogon lokaci, aminci da waɗanda suka fi bayar da gagarumar gudunmawa, inda wasu suka shafe shekaru biyar, wasu kuma sama da shekaru arba’in suna aiki da kamfanin.
Wannan ya nuna aƙidar da ta jagoranci BUA tun kafuwar kamfanin, cewa manyan kasuwanci masu ɗorewa ana gina su ne ta hannun mutane.
Da yake jawabi a wajen taron, wanda ya kafa kuma Babban Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabi’u, ya bayyana daren a matsayin lokaci na godiya ga aminci, juriya, da haɗin gwiwar da aka yi a tafiyar BUA.
Ya tuna cewa daga ƙaramin mataki a shekaru 36 da suka wuce, BUA ta bunƙasa ta zama ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da aka jera a kasuwar hannayen jari a Nijeriya, inda haɗaɗɗen jarin kasuwancin kamfanin yanzu ya kai tiriliyoyin naira.
Sai dai ya jaddada cewa wannan nasara ba ta kasance ta mutum ɗaya, ko hukumar gudanarwa kaɗai, ko kuɗi kaɗai ba.
A cewar sa, “Kowace masana’anta da aka gina, kowanne tsari da aka ƙarfafa, kowane ƙalubale da aka shawo kan sa, da kowanne mataki na nasara, duk suna ɗauke da gudunmawar ma’aikatan da suka yi imani da hangen nesa tun kafin sakamako ya bayyana.”
Ya sake tabbatar da cewa BUA kullum yana ɗaukar ma’aikatanta a matsayin abokan tafiya a tarihin kamfanin, ba wai ma’aikata kawai ba, yana mai cewa aminci da ƙwarewa dole ne a karrama su ta hanyoyi na zahiri.
A cikin kyaututtukan shekarar 2025, an raba naira biliyan 30 ga mutane 510 a rukuni daban-daban na waɗanda suka daɗe suna aiki da jajircewa wajen hidimtawa da kuma nuna nagartar aiki.
Saboda ƙarancin lokaci a wajen taron, mutane 41 ne kawai suka karɓi kyaututtukan su kai tsaye daga Shugaban Kamfanin a dandali. Waɗannan su ne masu rukunin kyauta mafi girma, daga naira miliyan 100 zuwa naira biliyan 1.
Masu karɓar kyautar a dandali sun haɗa da: mutane 16 da suka karɓi naira 100 miliyan kowanne, 9 da suka karɓi naira miliyan 200 kowanne, 7 da suka karɓi naira miliyan 250 kowanne, 3 da suka karɓi aira miliyan 500 kowanne, 5 da suka karɓi naira 1 biliyan kowanne, da kuma wanda ya samu kyauta ta musamman wanda ba a bayyana adadin kuɗin sa a wajen taron ba.
An bai wa Kabiru Rabi’u wannan kyauta ta musamman saboda aminci, jagoranci da tsawon gudunmawar sa wajen bunƙasa da daidaita BUA Group.
Duk sauran waɗanda aka karrama sun riga sun karɓi faranti da takardun kuɗin su tun kafin bikin ko kuma za su karɓa a masana’antu da wuraren ayyukan su daban-daban a faɗin ƙasar.
Rabi’u ya bayyana kyaututtukan kuɗin a matsayin alamar godiya, yana mai cewa babu wani adadin kuɗi da zai iya biyan shekarun sadaukarwa, ƙoƙari da imani da manufar kamfanin.
Dangane da nan gaba, ya ce BUA zai ci gaba da faɗaɗa ƙarfin samarwa, zuba jari a sabbin fasahohi na zamani, da ƙarfafa ayyuka a ɓangarorin siminti, abinci, sukari da gine-ginen more rayuwa, yana mai cewa mutanen da suka gina kamfanin za su ci gaba da bunƙasa tare da shi.
Bikin Night of Excellence and Long Service Awards na BUA wani muhimmin ɓangare ne na al’adar kamfanin, wanda ke nuna ginin kamfani bisa wadatar juna, tunani na dogon lokaci, da girmama mutane.
Baya ga ma’aikata, abokan hulɗa, da kwastomomi, taron ya samu halartar manyan shugabannin masana’antu ciki har da Alhaji Aliko Dangote, abokai da masu fatan alheri, tare da Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, Ƙaramar Ministar Kuɗi, Doris Aikeime da Ministar Al’adu, Yawon Buɗe Ido da Tattalin Arzikin Ƙirƙire-ƙirƙire, Hannatu Musawa.







