Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana cewa a gobe Laraba al’ummar Musulmi za su tashi da azumin watan Ramalana mai daraja a Nijeriya sakamakon ganin jinjirin wata.
Sarkin Musulmin, wanda kuma shi ne shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a daren yau.
Sanarwar ta biyo bayan ganin jinjirin watan a wurare da dama a faɗin Nijeriya, kamar yadda Kwamitin Duban Wata na Ƙasa ya tabbatar.
Ya ce: “A madadin mu, Sarkin Musulmi na taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar tunkarar azumin Ramadan na shekarar 1447 bayan Hijira,” inji wata sanarwa daga Fadar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato.
Ya kuma roƙi Allah ya raya kowane Musulmi domin samun damar yin azumin tare da cin moriyar sa yadda ya kamata.
Tun da fari, an ga jinjirin watan Ramalana a ƙasar Saudiyya da sauran ƙasashe na duniya.
Ramadalana dai shi ne wata na tara a kalandar Musulunci, wanda Musulmi a faɗin duniya suke keɓancewa domin azumi, sallah, yin nazari da taimakon mabuƙata.
A tsawon watan, Musulmi masu azumi na kamewa daga cin abinci da shan abin sha tun kafin sallar asuba (Fajr) har zuwa faɗuwar rana (Maghrib).
Azumin ya ƙunshi ƙaurace wa ci, sha, shan taba da saduwa da iyali, domin samun ƙarin tsoron Allah (taƙawa) da kusanci gare Shi.
“Ya ku waɗanda kuka yi imani! An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi ga waɗanda suka gabace ku, domin ku samu taƙawa,” kamar yadda Alƙur’ani Mai Girma ya zo a Suratul Baƙarah aya ta 183 (2:183).
Azumi yana ɗaya daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar, tare da kalmar shahada, salloli biyar na yau da kullum, bayar da zakka, da kuma sauke farali (Hajji) zuwa Makkah – inda ake da ɗakin Ka’aba mai tsarki – ga wanda ya samu iko ta fuskar lafiya da hali.
A wannan lokaci, Musulmi na kamewa daga ci, sha da saduwa da iyali daga fitowar alfijir har zuwa faɗuwar rana na tsawon kwanaki 29 ko 30, gwargwadon yadda aka hango sabon jinjirin wata.







