• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci

ALI KANO by ALI KANO
April 28, 2026
in Siyasa
A A
0
Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci
Tambarin ADC

Tambarin ADC

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta roƙi Babbar Alƙaliyar Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, da a gaggauta fitar da hukunci kan rikicin shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa.

Ɓangaren ADC na David Mark ne ya yi wannan roƙo a cikin wata wasiƙa da babban lauyan su kuma Babban Lauyan Nijeriya (SAN), Shu’aibu Aruwa, ya sanya wa hannu.

Wasiƙar mai ɗauke da kwanan wata 28 ga Afrilu, an karɓe ta a ofishin CJN.

Sun yi roƙon cewa jam’iyyar ba za ta iya taka rawa a babban zaɓen 2027 ba sai an fitar da hukuncin cikin kwanaki uku daga yau.

Jam’iyyar ta ce za ta fuskanci mummunar illa da ba za a iya gyarawa ba idan har Kotun Ƙoli ba ta yanke hukunci a wannan doguwar taƙaddama ba a wa’adin da Dokar Zaɓe ta tanada domin tsayar da ‘yan takara a zaɓen 2027.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Kotun Ƙoli ta ajiye yanke hukunci kan rikicin ADC tun ranar 22 ga Afrilu, zuwa ranar da za a sanar da ɓangarorin da ke taƙaddamar.

Kwamitin alƙalai biyar na Kotun Ƙoli, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Lawal Garba, shi ne ya jingine hukuncin bayan lauyoyin ɓangarorin sun gabatar da hujjojin su na goyon baya da adawa da ƙarar.

Sai dai saboda fargabar ƙarin jinkiri wajen fitar da hukuncin, jam’iyyar ta nuna matuƙar damuwa cewa ba za ta iya shiga zaɓen gama-gari mai zuwa ba.

Ta ce ikon ADC na cika dukkan sharuɗɗan doka domin shiga zaɓen 2027 ya ta’allaƙa ne kacokam kan gaggauta fitar da hukunci a wannan ƙara.

Ta jaddada cewa idan ba a fitar da hukuncin cikin kwanaki uku masu zuwa daga ranar wasiƙar ba, ADC za ta fuskanci babban haɗari marar gyaruwa na a cire ta daga shiga babban zaɓen na 2027.

Ta ce hakan zai hana miliyoyin ‘yan Nijeriya da suka rungumi manufofin ADC haƙƙin su da kundin tsarin mulki ya ba su na yin tarayya da kuma tsayawa takara ta jam’iyyar siyasa da suka zaɓa.

Jam’iyyar ta tunatar da CJN cewa jinkirta adalci, a wannan yanayi na musamman, tamkar hana adalci ne. Makomar siyasar abokin hulɗar mu da kuma halastattun tsammanin membobin ta a faɗin ƙasa yanzu suna rataye ne a mizani, inji ta.

Tags: adawaADCCJNhukuncizaben2027
Previous Post

Gargaɗi, sharuɗɗa da wa’adin da CBN ya gindaya kan BVN don tsaurara matakan tsare kuɗaɗen kwastomomi a bankuna

Next Post

Yadda CBN ke ta ƙoƙarin daƙile malejin hauhawar farashi zuwa ƙasa da kashi 10 bisa 100

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

September 10, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Next Post
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa

Yadda CBN ke ta ƙoƙarin daƙile malejin hauhawar farashi zuwa ƙasa da kashi 10 bisa 100

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!