Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera, yana gaida Shugaba Bola Tinubu yayin da Gwamna Nasir Idris Ƙauran Gwandu yake kallon su a wurin bikin kamun kifi da al’adun gargajiya na Argungu karo na 61 da aka kammala a yau
A yau Asabar, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana bikin kamun kifi da al’adun gargajiya na Argungu karo na 61 a matsayin shaida ta dawowar zaman lafiya da daidaito a Jihar Kebbi da ma ƙasar nan baki ɗaya.
Da yake jawabi a wajen rufe bikin a Argungu, Shugaban ya yi alƙawarin ci gaba da ba da cikakken goyon bayan Gwamnatin Tarayya ga yawon buɗe ido, noma, tsaron abinci da bunƙasa karkara.
Ya yaba wa gwamnatin Jihar Kebbi bisa nasarar shirya wannan babban taron al’adu mai tarihi, wanda ya jawo fiye da masunta 50,000 daga sassa daban-daban na Nijeriya da ƙasashe maƙwabta.
Bikin na kwanaki huɗu ya haɗa da wasannin al’adu, gasar ruwa, damben gargajiya da raye-raye.
Tinubu ya ce: “Barka da zuwa. An yi ƙoƙari sosai. Kyakkyawan shiri. Tarihi mai armashi. Wannan biki ya shafe shekaru 83 yana gudana, kuma alama ce mai ƙarfi ta haɗin kai, juriya da zaman tare cikin lumana tsakanin al’ummarmu.”
Ya kuma yaba da tsare-tsaren tsaro da suka ba da damar gudanar da bikin cikin aminci da nasara.

Ya ce: “Tsarin shiryawa, tsaro da kuma yanayin taron sun nuna abin da zai yiwu idan shugabanci yana da manufa kuma ya haɗa kowa da kowa. Na gode, Mai Girma Gwamnan Jihar Kebbi. Kai jagora ne na ƙungiya, kuma kana nuna hakan.
“Irin wannan taron zamantakewa da al’adu zai bunƙasa ne kawai kuma ya zama abin jan hankalin yawon buɗe ido idan yanayin tsaro ya dace.
“Na yi farin ciki da ganin an samu gagarumin cigaba wajen yaƙi da rashin tsaro a Kebbi da sauran sassan ƙasar nan. Har yanzu muna aiki tuƙuru wajen haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya, gwamnatin jihohi da hukumomin tsaro. Muna da jami’an tsaro maza da mata da ke sadaukar da rayuwar su domin kare martabar ƙasa da tabbatar da zaman lafiya.
“Zaman lafiyar da muke gani a yau a wannan yanki ba haɗari ba ne. Sakamakon zuba jari ne mai ɗorewa a fannin tsaro, tattara bayanan sirri da kuma haɗa kan al’umma.
“Ina tabbatar maku da cewa za a yi nasara kan kowace irin barazana ta rashin tsaro, ciki har da fashi da makami da tayar da ƙayar baya.
“Manoman mu, ciki har da masunta, ‘yan kasuwa da iyalai, za su ci gaba da gudanar da rayuwar su ba tare da tsoro ko rauni ba. Wannan biki shaida ce ta dawowar zaman lafiya da daidaito.
“Za mu ci gaba da tallafa wa wannan biki tare da ƙarfafa shi. Sarakunan mu na gargajiya, musamman masu kula da wannan biki, suna a zuciyar ajandar mu ta ƙasa. Muna zuba jari da gangan a shirye-shiryen da ke bai wa matasa, mata da al’ummomin karkara ƙarfi.”

Da yake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya ga noma, Shugaban ya sake tabbatar da goyon baya ga manoma, masunta da al’ummomin karkara.
Ya ce: “Ta hanyar aiki tare da gwamnatin jiha, za mu ci gaba da bai wa manoman mu tallafin da ya dace. Jihar Kebbi ta shahara wajen jajircewa kan samar da abinci da noma. Za mu yi aiki tare don tabbatar da nasarar tattalin arziki mai girma.”
Ya kuma jaddada ƙarfin al’adu wajen haɗa kan jama’a, yana mai cewa: “Bikin kamun kifi na Argungu yana tara mutane masu asali, ƙasashe da addinai daban-daban cikin ruhin abota da gasa mai kyau.
“Yana nuna gadon al’adun mu tare da tallata Nijeriya a duniya cikin kyakkyawan haske. Ina yaba wa masu shirya taron, kuma ina sake tabbatar da jajircewa ta ga zaman lafiya, ƙarfafa tattalin arziki, samar da abinci da bunƙasa ababen more rayuwa a tarayya.”
Kafin halartar bikin a Argungu, Shugaban ya ƙaddamar da muhimman ayyukan more rayuwa a Birnin Kebbi, ciki har da Sabon Ginin Sakatariyar Bola Ahmed Tinubu, Sabuwar Tashar Mota ta zamani, babbar hanya mai layi uku, Kwalejin Jinya da Ungozoma ta Ƙauran Gwandu da ke Ambursa, da kuma sabuwar hanyar Old Argungu By-Pass da aka faɗaɗa.
A jawabin sa, Gwamna Nasir Idris ya gode wa Shugaban bisa karrama jihar da halartar bikin.
Ya sake jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da gudanar da bikin a matsayin dandalin kiyaye al’adu, bunƙasa yawon buɗe ido da ƙarfafa tattalin arziki.
Yayin da yake bayyana nasarorin gwamnatin sa, Gwamnan ya lissafa zuba jari a fannin ababen more rayuwa, ciki har da gina sakatariya ta zamani, faɗaɗa manyan tituna, bunƙasa hanyoyin cikin birane da sake gina hanyoyin tsakanin birane, tare da gyaran gaggawa na ababen more rayuwa da ambaliyar ruwa ta lalata.

A fannin lafiya, gwamnan ya ce an gyara tare da samar da kayan aiki ga manyan asibitoci 16, kana ana kan gina da gyara cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko sama da 120.
Ya ce an ɗauki ma’aikatan lafiya fiye da 1,800 domin ƙarfafa bayar da sabis a faɗin jihar.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta raba takin zamani, ingantattun iri, magungunan gona da kayan aiki kyauta ga manoma, lamarin da ya ƙara yawan amfanin gona tare da tallafa wa ajandar tsaron abinci ta Gwamnatin Tarayya.
Ya kuma bayyana inganta jin daɗin ma’aikatan gwamnati, ciki har da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi da ci gaba da biyan albashi, fansho, kuɗin ritaya da sauran haƙƙoƙi.
A fannin ilimi, gwamnatin ta gina tare da ƙawata dubban azuzuwa da manyan makarantun zamani a dukkan yankunan masarautu, ta ɗauki malamai, tare da ci gaba da shirye-shiryen tallafin karatu ga ɗalibai a gida da waje.
Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera, ya nuna farin ciki cewa ruwan tarihi na Matan Fada, babban wurin gasar kamun kifi, ya sake shaida harbin bindigar gargajiya bayan kusan shekaru shida na dakatawa.
“Tsawon bugu 61, wannan biki ya ci gaba ba kawai a matsayin gasa ba, amma a matsayin shaida ta yadda al’ummar mu ke zaɓar jarumtaka maimakon rikici, da abota maimakon gaba,” inji Sarkin.
Ya ƙara da cewa: “Zuwan ka nan, ya Mai Girma Shugaban Ƙasa, ba wata karramawa ta yau da kullum ba ce. Wata babbar shaida ce ta goyon baya ga waɗannan muhimman ƙimomi: jarumtaka, sulhu, zaman lafiya da abota.
“Waɗannan su ne ginshiƙan haɗin kan ƙasa, kyakkyawan shugabanci da cigaba, waɗanda su ne tubalan ajandar Sabuwar Fata ta Shugaban Ƙasa.”
Ya yaba da shirye-shiryen Shugaban, yana mai cewa: “Muna ganin wannan ajanda ta bayyana a shirin rancen karatu ga ɗalibai, samar da kiwon lafiya na matakin farko, da faɗaɗa damar samun allurar rigakafin ceton rayuka ga yaran mu.
“Muna alfahari da jagorancin ka wajen sake horas da ma’aikatan lafiya, wanda ya ba ka matsayi na Gwarzon Tarayyar Afrika a fannin Kiwon Lafiyar Al’umma.
“A ayyukan jama’a, hangen nesan ka a bayyane yake. Hanyar bakin teku da kuma hanyar Illela zuwa Badagiri, wadda Jihar Kebbi ce mafi amfana da ita, ba hanyoyi kaɗai ba ne; jijiyoyin arziki ne da ke haɗa manoman mu na karkara da kasuwannin waje.”

Da yake sanar da sakamakon gasar kamun kifi, Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, ya ce Abubakar Usman daga Ƙaramar Hukumar Maiyama ne ya zama zakara gaba ɗaya da kifi mai nauyin kilo 59.
An ba shi kyautar Naira miliyan 1 da sababbin motoci guda biyu.
Abdullahi Garba daga Argungu ya zo na biyu da kifi mai nauyin kilo 40.
Gwamnatin jihar ta ba shi Naira 750,000, sabuwar mota da kujerar zuwa aikin Hajji.
Matsayi na uku kuwa ya samu ne ga ‘yan takara biyu daga jihohin Jigawa da Kogi da kifi mai nauyin kilo 33 kowannen su.
Sun samu Naira miliyan 1 da babur guda kowannen su.
Dukkan kifayen huɗu da suka yi nasara an miƙa su ga Shugaba Tinubu a matsayin abin tunawa.




