Gwamnatin Tarayya ta bayyana Bikin Kamun Kifi da Bajekolin Al’adu na Duniya na Argungu a matsayin wata babbar alama ta haɗin kan Nijeriya, gadon al’adu, da kuma karɓuwar al’adun ƙasar nan a idon duniya, yayin da ta jaddada muhimmancin sa wajen bunƙasa tattalin arziki ta hanyar yawon buɗe ido.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar buɗe taron bikin Argungu karo na 61, wanda aka gudanar a ranar Laraba, 21 ga Janairu, 2026, a dandalin hedikwatar Hukumar Talbijin na Ƙasa (NTA) da ke Abuja.
Daraktan Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar, Dakta Suleiman Haruna, shi ne ya wakilci Ministan a wurin taron.
A cewar Ministan, bikin Argungu na ɗaya daga cikin tsofaffin bukukuwan al’adun gargajiya mafi daɗewa a Nijeriya, wanda tun farkon kafuwar sa a shekarar 1934 yake haɗa kan al’umma cikin zaman lafiya da manufa ɗaya.
Ya bayyana cewa bikin yana bajekolin ɗimbin gadon al’adun ƙasar nan ta hanyar gasar kamun kifi, tseren kwale-kwale, kaɗe-kaɗe, raye-raye, da sauran al’adun gargajiya.
Haka kuma, ya bayyana cewa sanya bikin a cikin jerin fitattun abubuwan gadon al’adun ɗan’adam na hukumar UNESCO, ya nuna muhimmancin sa a duniya sannan ya haɓaka martabar al’adun Nijeriya a matakin ƙasa da ƙasa.
Ministan ya bayyana cewa bukukuwan al’adu ba dandali ba ne kawai na nuna al’ada ba, har ma su ne ƙashin bayan bunƙasa tattalin arziki.
Ya bayyana cewa ana sa ran sashen zirga-zirga da yawon buɗe ido na Nijeriya zai samar wa tattalin arzikin ƙasar nan kusan naira tiriliyan 9.55 (kimanin dala biliyan 14.8), wanda ya kai kashi 3.9 na jimillar arzikin ƙasar nan (GDP), tare da samar da ayyukan yi fiye da miliyan 2.7.
Ya ce: “Bukukuwa irin na Argungu suna tayar da harkokin tattalin arziki ta hanyar bunƙasa karɓar baƙi, sufuri, kasuwanci, da fasaha, yayin da suke samar da damarmaki ga masunta, manoma, masu aikin hannu, da ’yan kasuwa a cikin al’ummar da ke karɓar baƙuncin bikin”.
Ministan ya ƙara da cewa Nijeriya ta samu tafiye-tafiyen yawon buɗe ido na cikin gida kusan miliyan uku a shekarar 2023, baya ga baƙi fiye da miliyan 1.2 daga ƙasashen waje, abin da ke nuna ƙaruwar sha’awar al’adu, gadon tarihi da wuraren nishaɗi na ƙasar nan.
Ya jinjina wa Gwamnatin Jihar Kebbi bisa hangen nesa da jajircewar sa wajen shirya bikin karo na 61, sannan ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a gwamnati, kamfanoni masu zaman kan su, da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa da su tallafa wa shirye-shiryen da za su ƙarfafa yawon buɗe ido na al’adu da kuma samar da fa’idar tattalin arziki mai ɗorewa ga ’yan Nijeriya.
Ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen yaɗa labarai masu kyau game da ƙasar nan, da zurfafa yawon buɗe ido na cikin gida, da kuma sanya gadon al’adun Nijeriya a matsayin muhimmin ginshiƙi na bunƙasa tattalin arziki da haɗin kan ƙasa.
Daga ƙarshe, Ministan ya bayyana kyakkyawar fata cewa bikin Argungu zai ci gaba da bunƙasa, da wanzar da haɗin kai, da jawo baƙi, tare da ba da gagarumar gudunmawa ga cigaban al’umma da arzikin ƙasa.




