Bahaushe ya yi gaskiya da ya ce ‘siyasa romon jaɓa – ga kitse ga wari’. Mummunan rikicin da ya kunno kai tsakanin uwargidan Gwamnan Jihar Anambara, Nonye Soludo, da Sanata Uche Ekwunife ya tabbatar da hakan, inda Ekwunife ta yi zargin cewa Gwamna Charles Soludo da matar sa Uche duk an dama da su a zamanin mulkin marigayi gwamnan Anambara, Chiwonke Mbadiniju. Ta ci gaba da zargin cewa, “Wataƙila ‘ya’yan ta ba Gwamna Soludo ne ya haife su ba.”
Wannan mummunan zargi ya biyo bayan da tun farko ita Nonye matar gwamna ta yi zargin cewa digirin dakta na Uche, ba sahihi ba ne, na bogi ne.
Wannan bahallatsa dai ta bijiro ne yayin da zaɓen gwamna a 2025 ɗin nan a Jihar Anambara ya gabato, wanda Uche ta tsaya takarar mataimakiyar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar adawa, shi kuma Soludo ya sake tsayawa takara ƙarƙashin jam’iyyar sa ta APGA. Uche ta tsaya takara a ƙarƙashin APC, a zaɓen wanda za a kafsa a ranar 8 ga Nuwamba, 2025.
Cikin wata sanarwar da Nonye ta fitar a ranar Asabar, ta ce ba za ta zubar da ajin ta tana hauragiya da Uche ba, amma za ta umurce ta da ta fito ta nemi afuwa cikin sa’o’i 72, ko ta maka ta kotu.
Ni Da Uche Kowace Ta Rantse Mana Ba Ta Taɓa Neman Maza Ba – Nonye:
Nonye matar gwamna ta kuma ƙalubalanci Sanata Uche cewa ta rantse idan ba ta taɓa neman maza sun yi lalata da ita ba.
“Ni dai na rantse da Ubangiji tun da nake shekaru 55 kenan a duniya, ban taɓa sanin ɗa namiji ba sai fa miji na Gwamna Soludo.
“Shekara 33 kenan da muka yi aure, ban aikata lalata da kowa ba tun bayan auren mu.
“Kuma ban san ɗa namiji ba kafin ya aure ni. Shi ya fara sanin budurci na, kuma har yau shi kaɗai ya san ni ‘ya mace,” inji Nonye.
“To amma ke Sanata Uche da kika zarge ni, ina ƙalubalantar ki cewa ki fito ki rantse kamar yadda na rantse cewa tun da kike jagaliya da faɗi-tashin neman muƙami a siyasa ba ki taɓa ha’intar mijin ki kin yi lalata da wasu ƙatti ba.
“Kuma ina ƙalubalantar ki cewa ni da ke kowace ta kwashi ‘ya’yan ta, mu je a yi masu awon jinin gano uban su.
“Ni zan biya kuɗin awon, wato gwajin DNA. Idan an tabbatar ‘ya’yan ki duka ba na cikin shege ba ne, zan taya ki murna kuma na yi maki kyautar maƙudan kuɗaɗe.”
Nonye ta rufe da cewa za ta so a yi masu gwajin cikin Satumba ɗin nan, ko Oktoba, wato kafin zaɓen gwamna ranar 8 ga Nuwamba.
Ba Ruwa Na Da Gwajin DNA, Matsalar Ki Ce Da Mijin Ki – Sanata Uche:
A nata martanin a ranar Asabar, Sanata Uche ta ce babu ruwan ta da batun zuwa yin gwajin DNA. Ta ce matsala ce ta Nonye tsakanin ta da mijin ta, su je can su ƙarata.
Nonye dai ta rantse ba ta ma taɓa haɗuwa ido da ido da Mbadiniju ba, wanda ya yi gwamna daga 1999 zuwa 2003.






