• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Rahoton Musamman

Taƙaitaccen Tarihin Ɗanwaire Da Ƙasar Ruma

DAKTA SADA SALISU RUMAH Ɗanwairen Katsina by DAKTA SADA SALISU RUMAH Ɗanwairen Katsina
September 16, 2026
in Rahoton Musamman
A A
0

 

Gabatarwa

Tarihin Ɗanwaire da Ƙasar Ruma yana daga cikin muhimman sassa na tarihin Katsina da tarihin yaƙe-yaƙe da sarautun ƙarni na goma sha tara. Ɗanwaire, wanda aka fi sani da Muhammadu Sani Gurshe, ya shahara a matsayin fitaccen jarumi kuma jagoran mayaƙa, musamman a yaƙe-yaƙen da suka shafi Katsina da Daular Sakkwato.

Haka kuma, tarihin Ruma yana da alaƙa ta ƙut-da-ƙut da tarihin Ɗanwaire, domin bayan watsewar mazaunan Ruma sakamakon hare-hare, an danganta sake taruwar su da komawar su Ruma ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Sani Ɗanwaire. Daga baya, Ruma ta ci gaba da kasancewa muhimmiyar cibiyar sarauta da tarihi a yankin Katsina.

Wannan rubutu zai yi ƙoƙarin haskaka asalin Ɗanwaire, tarihin Ƙasar Ruma, rawar da ya taka a yaƙe-yaƙe da sarautu, da kuma gadon tarihi da ya bari ga zuriyar sa da al’ummar Ruma, tare da bambance abin da rubuce-rubucen tarihi suka tabbatar da kuma abin da ya dogara da ruwayar baka.

ƊANWAIRE DA KASAR RUMA

Masana daga wurare da dama sun bayar da labarai iri-iri game da tarihin Ɗanwaire da Ƙasar Ruma. Mafi akasarin labarun na kama da juna, wasu kuma sun yi saɓani da juna. Sai dai, labarun da suka fito daga taskokin Rumawa ne ya kamata su fi sahihanci tun da Muhammadu Sani Gurshe (Ɗanwaire) Barumaye ne, ɗan asalin Ruma, iyaye da kakanni.

Masarautar Ruma, tsohuwar masarauta ce mai muhimmin tarihi a Ƙasar Katsina. Ta ƙunshi wasu garuruwa da ke ƙarƙashin ta. Don haka, Ƙasar Ruma ta daɗe da matsayi na musamman a tsarin sarautar gargajiya da na yaƙi. A tarihi, sarautar Ruma ta kasance ƙarƙashin sarakuna masu taken Gatari, kafin daga bisani a sake kafa garin da tsarin sarautar irin na yanzu, wato Sarkin Ruma, a farkon ƙarni na ashirin. Akwai yankuna na magaddai da dama a ƙarƙashin Ruma. Sarakuna biyar ne suka mulki Ƙasar Ruma a zango na farko, wato 1724–1842. Tarihi ya raba wanzuwar Ruma gida biyu saboda akwai lokacin da babu ita (1843–1900).

SARAKUNAN ƘASAR RUMA 1700–1800

  1. Sarkin Ruma Ahmad — (1724–1762)
  2. Sarkin Ruma Gatari Hussaini — (1762–1774)
  3. Sarkin Ruma Gatari Muhammad Jitau — (1774–1799)
  4. Sarkin Ruma Gatari Faskari — (1799–1829)
  5. Sarkin Ruma Gatari Abdullahi Faskari — (1829–1842)

A shekarar 1842, zamanin mulkin Gatari Abdullahi Faskari, tsohuwar Ruma ta faɗa cikin ɗimbin rikici da yaƙe-yaƙe tsakanin daular Maraɗi da ta Katsina. A lokacin ne Sarkin Maraɗi Ummaru Ɗan Mari Ɗan Gwozo da dakarun sa suka kai wa Ruma hari, suka kuwa taki sa’a Gatari Abdullahi da iyalan sa da mafi akasarin dakarun Ruma ba sa garin Ruma. Samun wannan dama sai maharan daular Maraɗi suka far wa garin na Ruma, suka kuma ƙone shi ƙurmus. Wannan hari ne ya haddasa faɗuwar Ruma tsohuwa. Mazauna wannan gari mai tarihi da yankunan da ke ƙarƙashin sa suka watse zuwa wasu garuruwa daban-daban na Ƙasar Hausa.

Bayan faɗuwar Ruma, zuriyar ta ta ci gaba da rayuwa da yawo a wurare da dama. A shekarar 1900 ne Muhammadu Sani Gurshe, Ɗanwaire, ɗan Gatari Abdullahi Faskari, saboda kishin ƙwazon sa ya dawo yankin tare da tattaro dangin sa masu dama suka sake kafa ƙasar da kakannin sa suka assasa. Tarihi ya nuna cewa a shekarar 1900 ne Ɗanwaire ya sake gina sabon garin Ruma, wanda ya saka wa suna Makururuta. A shekarar 1901, aka naɗa shi Sarkin Ruma, sannan ya ci gaba da ginawa da raya Sabon garin Ruma. Wannan ya ba da damar Rumawa da yawa suka sake komawa yankin. Sun gina yankin ta hanyar gina garin na Ruma sabuwa da wasu ƙauyuka da dama da ke ƙarƙashin mulkin Ruma, tare da bunƙasa tattalin arziki da zamantakewa a tsakanin al’ummar su.

SARAKUNAN RUMA SABUWA 1900–YAU

  1. Sarkin Ruma, Sarkin Yaƙi Muhammadu Sani Gurshe (Ɗanwaire) — (1901–1915)
  2. Sarkin Ruma Abubakar Dandu, babban ɗan Ɗanwaire — (1915–1945)
  3. Sarkin Ruma Mu’azu Abubakar Dandu — (1945–1983)
  4. Sarkin Ruma Tukur Mu’azu — (1983–2025)
  5. Sarkin Ruma Muhammadu Sani Tukur — (29/08/2026–zuwa yau)

A taƙaice, tarihin sarautar Ruma ya kasu zuwa manyan matakai guda biyu:

A. tsohuwar Ruma, wadda jerin sarakunan ta ya fara daga Ahmad (1724) har zuwa Gatari Abdullahi Faskari (1842). Waɗannan sarakuna ne na kafin Jihadi da lokacin Jihadi.

B. Sannan kuma sabuwar Ruma, wadda Sarkin Yaƙi Muhammadu Sani Gurshe (Ɗanwaire) ya sake kafawa a farkon ƙarni na ashirin.

A yanzu dai masarautar Ruma tana ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Batsari, hedikwatar kuma ita ce Batsari, inda fadar Sarkin Ruma take. Tarihi ya nuna cewa Muhammadu Sani Gurshe, Ɗanwaire ya yi sarautar Mashi (1888) da kuma Kankiya (1892) a lokacin rayuwar sa. Kafin nan, ya riƙe sarautar garin Waire, a yankin Bichi ta yanzu, ta Jihar Kano, a zamanin yaƙe-yaƙen masarautun Ƙasar Hausa.

Domin tunatarwa, an haifi Muhammadu Sani Gurshe a garin Fototuwa, ta Ƙaramar Maraɗi na Jamhuriyar Nijar, a shekarar 1856, daga zuriyar Ruma ta daular Katsina. Tun lokacin ƙuruciyar sa, an lura da haziƙancin sa da jarumtar sa wajen farauta da noma da kiwo. Tun yana matashi, ya nuna matuƙar ƙwarewa wajen sarrafa kowane irin doki da makami. Muhammadu Sani, mai biyayya da amfanawa da dangi ne matuƙa. Jarumtar sa ta yi fice a farauta da yaƙe-yaƙe na Ƙasar Hausa. Ya fara fita yaƙi tare da mahaifin sa Gatari Abdullahi a shekarar 1873, yana da shekaru 17.

Mutane da dama na alaƙanta Ɗanwaire da Kano ta fuskar asali, amma ba haka ba ne. Muhammadu Sani Gurshe ɗan Katsina ne. A lokacin Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi (1800–1882) da kuma lokacin Sarkin Kano Muhammadu Bello (1882–1893), Daular Sakkwato ta ba da aron Muhammadu Sani Gurshe ga Masarautar Kano a shekarar 1880 domin taimaka mata wajen yaƙe-yaƙe da suka addabe ta. A wajen waɗannan yaƙe-yaƙe ne aka samu gagarumar nasara da ta sa Sarkin Kano Maje-Karofi ya naɗa shi sarautar Dagacin Waire da ke arewacin Kano.

A wannan lokaci an riƙa kiran sa da sunan “Mai Waire”, wato, Mai Shugabancin Garin Waire.

 

Tags: KatsinaRumaTarihiyaƙe-yaƙeƊanwaireƙasar Hausa
Previous Post

Cewar Sarkin Zazzau: An yi wa rawar da El-Rufai ya taka wajen naɗa ni sarauta gurguwar fahimta

Next Post

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

Related Posts

D.O. Fagunwa: Gogaggen Jigo A Adabin Afrika
Rahoton Musamman

D.O. Fagunwa: Gogaggen Jigo A Adabin Afrika

July 3, 2026
Nau’o’in Kama Mutane Ba Bisa Ƙa’ida Ba Guda 5 a Nijeriya
Rahoton Musamman

Nau’o’in Kama Mutane Ba Bisa Ƙa’ida Ba Guda 5 a Nijeriya

June 11, 2026
Ziyarar Aminci da Sadaukarwa: Tsokaci kan Gaisuwar Sallah da Matawalle Ya Kai wa Shugaba Tinubu a Legas
Rahoton Musamman

Ziyarar Aminci da Sadaukarwa: Tsokaci kan Gaisuwar Sallah da Matawalle Ya Kai wa Shugaba Tinubu a Legas

May 26, 2026
Abin Da Sauyin Talbijin Zuwa Tsarin Dijital A Nijeriya Yake Nufi
Rahoton Musamman

Abin Da Sauyin Talbijin Zuwa Tsarin Dijital A Nijeriya Yake Nufi

May 14, 2026
Kamfanonin ‘yan canji 82 kaɗai CBN ya ba lasin canjin kuɗin ƙasashen waje
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda CBN ya lashe lambar yabo ta Gwarzon Babban Bankin Shekara na Duniya

March 24, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya umurci bankuna su yi gwajin ƙarfin jure matsin tattalin arziki

March 8, 2026
Next Post
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma'aikatan banki ba

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!