An haifi Daniel Olorunfemi Fagunwa (D.O. Fagunwa) a shekarar 1903 a garin Oke-Igbo, Jihar Ondo, Nijeriya.
A matsayin sa na ɗaya daga cikin fitattun marubutan farko na Nijeriya da suka riƙa rubuta littattafai da harshen Yarbanci, Fagunwa ya bayar da gagarumar gudunmawa ga bunƙasar adabin Afrika. Ba wai saboda iya ba da labari kaɗai ba, har ma saboda ya taimaka wajen gina tubalin adabin da ake rubutawa cikin harsunan gargajiya na Afrika.
Ayyukan sa sun haɗa tatsuniyoyi, al’adun ruhaniya da kuma tunanin falsafa na Yarabawa cikin hikima, lamarin da ya nuna yalwar al’adu da rayuwar al’ummar Yarabawa.
An fi sanin sa da littattafai irin su Ògbójú Ọdẹ nínú Igbó Irúnmọlẹ̀ da Igbó Olódùmarè, waɗanda suka ƙunshi tatsuniyoyi masu ban al’ajabi da darussa na ɗabi’a, tare da haɗa al’adun Yarabawa, koyarwar Kiristanci da karin maganganu masu hikima.
Gadon da ya bari a fagen ba da labari ya ci gaba da rayuwa ta hanyar fassarorin da fitaccen marubuci Wole Soyinka da wasu suka yi, kuma har yanzu yana ci gaba da zaburar da marubutan Afrika.
Fagunwa ya rubuta littafin Ogboju Ode ninu Igbo Irumole ne lokacin da yake shugaban makarantar St. Andrew’s Practising School da ke Oyo tsakanin shekarun 1930 zuwa 1939.
Yayin da yake rubuta littafin, Fagunwa ya kasance kamar wani mai bauta ko mai neman ilimin ruhaniya. Ya nemo wata ƙaramar hanya cikin daji daga garin Oyo zuwa hanyar Ibadan, inda ya isa wata babbar bishiya mai girman gaske, wadda hasken rana ba ya iya ratsawa ƙarƙashin ta. A can ne ya kai ƙaramin teburi, kujera da littattafai, sannan ya fara rubuta littafin sa na farko.
Daga baya ya lura da cewa a gefen hanyar dajin da ya buɗe akwai wata mata da ke sayar da doya a wata ‘yar ƙaramar rumfa. Bai san cewa matar tana zargin shi ba, tana tsammanin ba mutum ba ne. Kullum sai ya fito daga cikin daji ya sayi doya, sannan ya koma cikin dajin.
Saboda haka matar ta sanar da wasu mafarauta da mutanen ƙauye domin su bincika dajin. Sa’ar Fagunwa, lokacin da suka zo yana wajen sayen doya. Da sun same shi a cikin dajin, wataƙila da sai buzun sa. Da yake dawowa bayan ya sayi doya, sai mutanen suka tare shi.
Sun tambaye shi inda yake zuwa da kuma daga ina ya fito. Ya bayyana musu cewa shi marubuci ne kuma yana rubuta littafi. Sai suka tambaye shi, “Kana nufin marubuta suna rubutu ne a cikin daji?”
Sai suka bi shi zuwa wurin da yake aiki, inda suka ga kujera, teburi da littattafai. Daga nan suka tambaye shi asalin sa. Ya gaya musu cewa shi ne shugaban makarantar St. Andrew’s Practising School da ke Oyo. Wannan ne ya sa suka rabu da shi.
Bayan ya kammala littafin kuma ya samu mai wallafa shi, ya samu fam £25. Da wannan kuɗin ne ya shirya auren sa da matar sa ta farko, ya sayi sabon keke, garmaho da faifan waƙoƙi, gadon ƙarfe, katifa da sauran kayayyaki masu yawa. Har ma ya ɗauki shatar mota daga Legas domin ta kai shi Oyo tare da kayan sa.
Da ya isa Oyo, budurwar sa ta yi mamakin yadda ya samu kuɗin sayen waɗannan kayayyaki masu daraja. Wannan ne ya ƙara masa ƙwarin gwiwa da zaburarwa wajen ci gaba da rubuta wasu littattafai.
Mutuwar Fagunwa mai cike da ruɗani
Mutuwar D.O. Fagunwa ta kasance abin mamaki ga mutane da dama. Saboda haka, da yawa daga cikin mutanen yankin su sun ƙi yarda da cewa ya mutu ne ta hanyar haɗari kawai lokacin da ya nutse a cikin kogi a ranar 7 ga Disamba, 1963.
Wasu sun yi imanin cewa alloli ko mugayen aljannu ne suka haddasa mutuwar sa. Wasu ma sun yi zargin cewa maciji mai kan mutum da ya bayyana a cikin littafin sa Igbo Olodumare ne ya haɗiye shi.
Sai dai gaskiyar lamarin ita ce, ya nutse ne yayin da yake jiran jirgin ruwa domin ya tsallaka kogi a hanyar sa ta dawowa daga aikin tallata littattafan Heinemann ga makarantu a Arewacin Nijeriya, inda kuma ya je neman ƙwararrun marubuta irin sa.
Matar sa, Elizabeth Adebanke Fagunwa, wadda ta rasu a shekarar 2018 tana da shekaru 85, ta shaida wa jaridar Tribune a shekarar 2017 cewa: “Direban sa James ya ce kwale-kwalen ya juye ne ya rufe shi. James ya yi ihu yana neman taimako, mutane suka zo domin ceto shi, amma ba a ga Fagunwa ba. Yayin da ake ci gaba da neman sa a cikin kogin, an aika saƙo zuwa Ibadan. Ni kuwa har yanzu ina da yaƙinin cewa za a dawo da shi da rai domin ƙwararren mai iyo ne. Amma abin takaici, bai dawo da rai ba.”
A rana ta uku bayan ɓacewar sa ne aka gano gawar sa tana yawo kan ruwa a daidai wurin da ya nutse.
Matar sa ta ƙara da cewa: “Abin da ya ba mu mamaki shi ne har lokacin da aka gano gawar sa yana sanye da takalman sa, tufafin sa ba su lalace ba, hular sa tana kan sa, kuma yana riƙe da tabaran sa (gilashinsa) a hannun sa.”
A lokacin mutuwar sa, matar tasa tana da kusan shekara 31 kacal, kuma ba ta sake yin aure ba.
A shekarar 1959 an ba Fagunwa lambar girmamawa ta Member of the Order of the British Empire (MBE). Bayan rasuwar sa kuma, a shekarar 1965, an ba shi lambar karramawa ta Margaret Wrong Prize.
An binne shi a maƙabartar St. Luke’s Anglican Church da ke Oke-Igbo ranar 10 ga Disamba, 1963, inda har yanzu kabarin sa yake.
Wani labarin yadda ya mutu
A cewar direban sa James, abin da ya faru shi ne Fagunwa ya zame a bakin kogi yayin da yake jiran jirgin ruwa.
An ce yana dawowa ne daga tafiyar kasuwanci a Arewacin Nijeriya. Ya kwana a Bida, sannan da safe suka ci gaba da tafiya. A kan hanyar su akwai Kogin Wuya, wanda a lokacin ba shi da gada.
Da suka isa bakin kogin, Fagunwa ya ce wa James ya jira shi, yayin da shi kuma ya bi wata hanya a gefen kogin. Ba da jimawa ba, James ya ji ƙarar ruwa, sai ya fahimci cewa Fagunwa ya zame daga bakin kogin ya faɗa cikin ruwa.
A yau dai ana kallon D.O. Fagunwa a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa tubalin adabin Afrika, musamman ta fuskar rubuce-rubuce cikin harsunan gargajiya da kuma haɗa tatsuniyoyi da rubutaccen adabi. Har yanzu tasirin sa yana ci gaba da zaburar da marubutan Afrika wajen binciko jigogin ruhaniya, asali da al’adu.
Idan ba ka iya karanta Yarbanci mai zurfi sosai, za ka iya karanta fassarar Turanci da Wole Soyinka ya yi mai taken The Forest of a Thousand Demons.
(Mun fassaro ciro daga jaridar Vanguard)






