• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Rahoton Musamman

Nau’o’in Kama Mutane Ba Bisa Ƙa’ida Ba Guda 5 a Nijeriya

Law Parlour by Law Parlour
June 11, 2026
in Rahoton Musamman
A A
0
Nau’o’in Kama Mutane Ba Bisa Ƙa’ida Ba Guda 5 a Nijeriya
Jami'an tsaro sun kama wani mutum

Jami'an tsaro sun kama wani mutum

Ana ɗaukar kama mutum a matsayin haramtacce idan har jami’an tsaro sun karya ƙa’idojin da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya da Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuka (ACJA) suka tanada. Ga wasu daga cikin nau’o’in kama mutane ba bisa ƙa’ida ba da suka fi yawa, waɗanda ya kamata ku sani:

1. Kama Ka Saboda Laifin Wani (Arrest in Lieu)

Idan ‘yan sanda suna neman wanda ake zargi da aikata laifi amma ba su same shi ba, ba su da ikon kama mahaifin sa, mahaifiyar sa, matar sa ko abokin sa a madadin sa.

Abin da doka ta ce: Sashe na 7 na ACJA ya tanadi cewa: “Ba za a kama wani mutum a madadin wani wanda ake zargi da laifi ba.”

2. Kama Ka Saboda Bashi Ko Kwangila (Civil Debt)

Idan kana bin wani kuɗi, ko ka kasa biyan rance, ko kuma ka karya yarjejeniyar kasuwanci, wannan al’amari ne na shari’ar farar hula. Haramun ne ga ‘yan sanda ko EFCC su kama ka domin tilasta maka biyan bashi.

Abin da doka ta ce: Sashe na 8(2) na ACJA ya bayyana cewa ba za a kama wanda ake zargi ba kawai saboda wata matsalar farar hula ko karya yarjejeniyar kwangila.

3. Kama Ka Bisa Zato Kawai (Ba Tare da Gamsasshen Dalili Ba)

Jami’in tsaro ba zai iya kama ka kawai saboda bai ji daɗin salon gashin ka ba, ko tufafin ka, ko kwamfutar ka, ko motar da kake hawa ba. Dole ne a samu hujja mai ma’ana da ke danganta ka da wani takamaiman laifi kafin a kama ka.

4. Kama Ka Ba Tare da Bayyana Dalili Ba

Jami’an tsaro ba za su iya saka ka a mota su tafi da kai ba tare da sun gaya maka ƙarara dalilin da ya sa aka kama ka ba.

Abin da doka ta ce: Sashe na 35 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanadi cewa dole ne a sanar da kai nan take, cikin harshen da kake fahimta, dalilin kama ka.

5. Tsare Ka Fiye da Lokacin da Doka Ta Amince (Over-Detention)

‘Yan sanda ba za su iya tsare ka a kurkuku na dogon lokaci ba da hujjar cewa wai “har yanzu muna bincike.”

Abin da doka ta ce: Kundin Tsarin Mulki ya tanadi cewa dole ne a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu cikin sa’o’i 24 zuwa 48. Duk wata tsarewa da ta wuce wannan wa’adin ba tare da izinin kotu ba, tsarewa ce ba bisa ƙa’ida ba.

Me Doka Ta Tanada Idan Hakan Ta Faru da Kai?

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya bayyana a fili cewa idan aka kama ka ko aka tsare ka ba bisa ƙa’ida ba, kana da haƙƙin neman a ba ka haƙuri a bainar jama’a tare da biyan ka diyya daga hukumar da ta aikata hakan.

Kada Ka Bari Wani Ya Tsorata Ka Ko Ya Yi Maka Wata Barazana!

Ka san haƙƙoƙin ka, ka kare kan ka, kuma ka nemi taimakon lauya idan aka tauye maka su.

(Daga shafin Law Parlor da ke Facebook)

Tags: 'yan sandadokajami'an tsarokama mutum
Previous Post

Asusun IMF ya jinjina wa manufofin kuɗi na CBN, ya yaba da shirin ƙarfafa jarin bankuna

Next Post

Tinubu ya ƙaddamar da titin Kuje da aka daɗe da watsi da shi, ya ce gwamnati tana magance matsalolin da ta gada

Related Posts

Rahoton Musamman

Taƙaitaccen Tarihin Ɗanwaire Da Ƙasar Ruma

September 16, 2026
D.O. Fagunwa: Gogaggen Jigo A Adabin Afrika
Rahoton Musamman

D.O. Fagunwa: Gogaggen Jigo A Adabin Afrika

July 3, 2026
Ziyarar Aminci da Sadaukarwa: Tsokaci kan Gaisuwar Sallah da Matawalle Ya Kai wa Shugaba Tinubu a Legas
Rahoton Musamman

Ziyarar Aminci da Sadaukarwa: Tsokaci kan Gaisuwar Sallah da Matawalle Ya Kai wa Shugaba Tinubu a Legas

May 26, 2026
Abin Da Sauyin Talbijin Zuwa Tsarin Dijital A Nijeriya Yake Nufi
Rahoton Musamman

Abin Da Sauyin Talbijin Zuwa Tsarin Dijital A Nijeriya Yake Nufi

May 14, 2026
Kamfanonin ‘yan canji 82 kaɗai CBN ya ba lasin canjin kuɗin ƙasashen waje
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda CBN ya lashe lambar yabo ta Gwarzon Babban Bankin Shekara na Duniya

March 24, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya umurci bankuna su yi gwajin ƙarfin jure matsin tattalin arziki

March 8, 2026
Next Post
Tinubu ya ƙaddamar da titin Kuje da aka daɗe da watsi da shi, ya ce gwamnati tana magance matsalolin da ta gada

Tinubu ya ƙaddamar da titin Kuje da aka daɗe da watsi da shi, ya ce gwamnati tana magance matsalolin da ta gada

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!