• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Friday, May 15, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda CBN ya lashe lambar yabo ta Gwarzon Babban Bankin Shekara na Duniya

Rahoton Musamman

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
March 24, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki, Rahoton Musamman
A A
0
Kamfanonin ‘yan canji 82 kaɗai CBN ya ba lasin canjin kuɗin ƙasashen waje
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, tare da bankin

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, tare da bankin

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya lashe lambar yabo ta duniya a matsayin “Babban Bankin Shekara” a Gasar Bankunan Ƙasashen Duniya ta shekarar 2026, sakamakon manyan sauye-sauyen manufofin kuɗi da tsarin tattalin arziki da suka taimaka wajen daidaita tattalin arzikin ƙasar bayan shafe shekaru a baya ana fama da matsalolin manufofi kuɗi, kafin hawan Gwamnan CBN Olayemi Cardoso.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa daga Kwamitin Kyaututtukan Bankunan Tsakiya, wadda wakilin mu ya samu kwafen takardar a ranar Lahadi.

Sanarwar ta yaba da sake fasalin manufofi da gyare-gyaren hukumomi da suka dawo da amincewa a tsarin kuɗi na Nijeriya.

A cewar sanarwar, wannan lambar yabo na nuna komawar CBN zuwa tsarin manufofin kuɗi na zamani, ingantaccen shugabanci, da gyare-gyaren da suka ƙarfafa amincewar masu zuba jari tare da tabbatar da daidaiton kasuwa.

Kafin waɗannan gyare-gyare, tattalin arzikin Nijeriya na cikin mawuyacin hali, inda hauhawar farashi ke ƙaruwa, ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje ke raguwa, sannan kuma akwai wawakeken bambanci tsakanin farashin dala na hukuma da na kasuwar bayan fage.

Kwamitin ya nuna cewa zuwa shekarar 2023, hauhawar farashi ya kai kashi 22.4 cikin ɗari, yayin da wadatar musayar kuɗin waje ta ragu sosai, tare da tara bashin kusan dala biliyan 7 na buƙatun da ba a biya ba, da kuma bambancin sama da kashi 60 cikin ɗari tsakanin farashin hukuma da na kasuwar bayan fage.

Haka nan kuma, takardar na dauke da shaida da hujjojin yadda a baya aka fuskanci raguwar ci gaban tattalin arziki da rashin daidaiton manufofi, lamarin da ya sa Nijeriya ta sauka daga matsayi na farko a Afrika a 2014 zuwa matsayi na huɗu, bayan Afrika ta Kudu, Masar, da Aljeriya.

Haka kuma, bayar da kuɗi kai tsaye daga banki da tallafin gwamnati sun sanya manufofin cikin wani yanayi mara ɗorewa a wancan lokacin a baya.

Wani tsohon babban jami’in CBN, wanda ba a ambaci sunan sa ba, ya ce a wancan lokaci ƙasar na dab da faɗawa cikin halin da ƙasashe irin su Venezuela da Zimbabwe suka shiga, sakamakon matsalolin rashin daidaiton kuɗi, faɗuwar darajar kuɗi, da kuma raguwar ‘yancin babban banki.

Sai dai bayan naɗa Olayemi Cardoso a matsayin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya a watan Oktoba 2023, bankin ya fara aiwatar da manyan gyare-gyare domin dawo da daidaiton tattalin arziki da kuma sake gina amincewa.

Kwamitin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shugabancin Cardoso, CBN ya mayar da hankali wajen dakatar da tsoma bakin kuɗi kai tsaye, tsaurara manufofin kuɗi, biyan basussukan musayar kuɗin waje, da kuma dawo da ‘yancin bankin, wanda ya zama ginshiƙin shirin gyare-gyare mai zurfi bisa gaskiya da tsari.

Babban ɓangare na gyare-gyaren shi ne sauya tsarin kasuwar musayar kuɗin waje. CBN ya soke tsarin farashi da dama, ya koma tsarin kasuwa mai bin ka’idar mai saye da mai sayarwa, tare da ƙaddamar da tsarin zamani na hada-hadar musayar kuɗi domin ƙara gaskiya.

Cardoso ya ce, “Yanzu naira tana canzawa cikin daidaitaccen yanayi, kuma bambancin da ke tsakanin kasuwar hukuma da ta bayan fage ya ragu zuwa kasa da kashi 2 cikin ɗari daga sama da kashi 60.”

Sanarwar ta kuma nuna cewa bankin ya biya dukkan basussukan musayar kuɗin waje da ake bin sa, musamman ga sassa kamar jiragen sama da masana’antu, wanda ya taimaka wajen dawo da amincewar ‘yan kasuwa.

Sakamakon karuwar wadatar kuɗin waje, shigowar jarin waje, da kuma ƙarin fitar da kayayyakin da ba man fetur ba, ajiyar kuɗin waje na Nijeriya ya kai dala biliyan 46.7 zuwa watan Nuwamba 2025, mafi girma cikin kusan shekaru bakwai, tare da wadatar shigo da kayayyaki na fiye da watanni 10.

A rahoton sa na watan Yuli 2025, Asusun Lamuni na Duniya (IMF), ya yaba da gyare-gyaren, yana cewa sun ƙara amincewar kasuwa tare da inganta wadatar kuɗin waje.

Game da hauhawar farashi, kwamitin ya ce CBN ya tsaurara manufofi sosai, inda ya daga ribar ruwa daga kashi 18.75 cikin ɗari a 2023 zuwa kashi 27.5 cikin ɗari zuwa Nuwamba 2024. Duk da cewa hauhawar farashi ta kai kashi 34.80 a Disamba 2024, daga baya ya ragu zuwa kashi 15.10 a Janairu 2026.

Hauhawar farashin abinci ma ya ragu zuwa kashi 8.9, alamar samun daidaito a farashi.

Wannan raguwar ta bai wa bankin damar fara sassauta manufofi a hankali, inda ya rage ribar zuwa kashi 26.5 zuwa Fabrairu 2026.

Cardoso ya jaddada ƙudirin bankin na rage hauhawar farashi, yana cewa wannan matakin na yanzu ba abin karɓa ba ne, tare da ƙoƙarin komawa tsarin da ke sa ido kai tsaye kan hauhawar farashi.

Baya ga manufofin kuɗi, kwamitin ya nuna gyare-gyare a ɓangaren bankuna, ciki har da shirin ƙara jarin bankuna da aka fara a 2024.

Fiye da bankuna 33 sun ƙarfafa jari, yayin da akalla 20 suka riga suka cika sharuɗɗan kafin ranar ƙarshe ta 31 ga Maris, 2026.

Waɗanda ba su cika ba na iya fuskantar rage izini ko haɗewa da wasu ko ma rufewa.

Haka kuma, bankin ya ƙarfafa sa ido ta hanyar komawa tsarin Basel III domin inganta kula da haɗari da ruwa.

A ɓangaren hada-hadar kuɗi na ƙanana, rance ya karu da sama da kashi 14, yayin da fiye da ƙananan ‘yan kasuwa miliyan 1.2 suka amfana da lamunin dijital a 2025.

A ɓangaren biyan kuɗi da fasahar zamani, CBN ya inganta tsarin sarrafa kuɗi, ya ƙara ingancin ATM, tare da ƙarfafa sa ido kan wakilan biyan kuɗi a faɗin ƙasar nan.

Fiye da katunan biyan kuɗi miliyan 12 marasa lamba suna yawo, yayin da kusan kamfanonin fintech 40 ke samun tallafi ta hanyar tsarin gwaji na bankin.

Haka kuma an samu ci gaba a bangaren bin doka da ƙa’ida, ciki har da kafa sashen bin doka na musamman da ƙarfafa yaƙi da wanke kuɗi, wanda ya taimaka wajen cire Nijeriya daga jerin sa ido na FATF a 2025.

Hukumomin kimanta ƙasashe ma sun yaba da gyare-gyaren. Fitch ta daga darajar Nijeriya daga B- zuwa B, yayin da Moody’s ta daga daga Caa1 zuwa B3.

Komawar Nijeriya kasuwar lamuni ta duniya ta kuma tabbata da fitar da Eurobond na dala biliyan 2.35 a 2025, wanda aka nemi fiye da sau biyar.

Duk da wannan ci gaba, kwamitin ya ce har yanzu akwai ƙalubale, ciki har da ci gaba da rage hauhawar farashi, kammala shirin ƙara jarin bankuna, da ƙarfafa hukumomi.

Sai dai ya kammala da cewa irin wannan gyare-gyare da CBN ya aiwatar abin yabawa ne ƙwarai, inda wani tsohon jami’i ya ce, “Abin da bankin ya cimma abin ban mamaki ne ƙwarai.”

Tags: CBNOlayemi Cardoso
Previous Post

Kafafen yaɗa labarai babban makami ne na isar da saƙo da shafar tunanin al’umma kan alƙibla – Idris

Next Post

Dalla-Dalla: Abubuwan da Suka Kamata a Sani Dangane da Shirin Ƙarfafa Jarin Bankuna na 2026

Related Posts

Abin Da Sauyin Talbijin Zuwa Tsarin Dijital A Nijeriya Yake Nufi
Rahoton Musamman

Abin Da Sauyin Talbijin Zuwa Tsarin Dijital A Nijeriya Yake Nufi

May 14, 2026
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Nagartattun sauye-sauyen CBN kan manufofin tattalin arziki sun haddasa ambaliyar masu sha’awar zuba jari daga ƙasashen waje

May 14, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai

May 12, 2026
Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

May 12, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna suka bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba

May 8, 2026
Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya

May 7, 2026
Next Post
Dalla-Dalla: Abubuwan da Suka Kamata a Sani Dangane da Shirin Ƙarfafa Jarin Bankuna na 2026

Dalla-Dalla: Abubuwan da Suka Kamata a Sani Dangane da Shirin Ƙarfafa Jarin Bankuna na 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!