• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Aiki Da Kasafin 2025 Cikin Satumba – Yakubu

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
September 14, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Aiki Da Kasafin 2025 Cikin Satumba – Yakubu
Dakta Tanimu Yakubu

Dakta Tanimu Yakubu

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za a fara aiki da kasafin kuɗi na 2025 a cikin watan Satumba.

Babban Darakta na Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya, Dakta Tanimu Yakubu, shi ne ya tabbatar da haka, yana mai cewa a ƙarshen wannan watan na Satumba za a fara aiki da kasafin, yayin da aka kawo ƙarshen aiki na tsare-tsaren kasafin kuɗin 2024.

Yakubu ya yi wannan ƙarin haske ne lokacin da yake jawabi a taron ganawa da masu ruwa da tsaki kan kasafi da kuma jama’a da ƙungiyoyi, wanda Ma’aikatar Kasafin Kuɗaɗe da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta Kasa ta shirya, ranar Alhamis a Abuja.

Babban daraktan ya ci gaba da cewa an tsara kasafin 2025 na naira tiriliyan 54.99, wanda aka yi wa take da “Kasafin Farfaɗo da Tattalin Arziki,” domin a zaburar da harkokin tattalin arziki, ayyuka sannan kuma da jawo ɗimbin masu zuba jari a fannoni daban-daban.

Ya ce: “Za a fara aiki da kasafin kuɗaɗe na 2025 a ƙarshen Satumba. An tsara kasafin domin ya magance muhimman ɓangarori, inganta tattalin arziki da kuma ƙarfafa ayyukan gwamnati.

“Za a riƙa aiwatar da ayyukan kashe kuɗaɗe bisa taka-tsantsan, domin tabbatar da samun nasarar da ake buƙatar samu.”

Daga nan ya yi magana kan muhimmancin ‘yan Nijeriya su riƙa shiga a harkokin ayyukan kasafin kuɗaɗe, yana mai cewa a ƙarshe dai ‘yan Nijeriya ɗin ne za su moriyar duk wasu albarkatun ayyukan da gwamnati ta samar.

Ya ce ana nan ana ƙoƙarin ganin an fassara dukkan bayanan kasafin kuɗaɗe zuwa yarukan cikin gida, ta yadda za a sauƙaƙa wa jama’a fahimtar kalmomi masu sarƙaƙiya.

Ya ce yin hakan zai sa jama’a su fahimci gundarin abin da kasafin ya ƙunsa ɗungurugum, tare sa-ido sosai kan yadda gwamnati ke aiwatar da ayyukan da ke ƙarƙashin kasafin.

Yakubu ya bayyana irin ƙalubalen da suka dabaibaye tsare-tsaren gudanarwar kuɗaɗen gwamnati a Nijeriya, waɗanda ya ce sun haɗa da matsalar kasa daidaita takamaiman hasashen kuɗaɗen shigar da gwamnati za ta samu daga man fetur da dangogin sa, matsalar da ke tattare da aiwatar da Dokar Man Fetur ta Petroleum Industry Act, inganta sahihancin hanyoyin tara kuɗaɗen haraji da tsarin biyan kuɗaɗen kwangiloli, sai kuma ɗimbin kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa wajen biyan basussuka.

Ya yi nuni da cewa aƙalla Naira tiriliyan 14.3 duk wajen biyan basussuka za ta tafi daga cikin kasafin 2025.

A ƙarshe ya bayyana matakan da za a ɗauka domin mara wa gwamnati baya, ta yadda za ta bunƙasa tattalin arzikin Najeriya har ya kai gejin dala tiriliyan ɗaya, nan da zuwa shekarar 2030.

Ya ce cikin matakan da za a ɗauka har da tsare-tsaren ciyar da mazaɓun faɗin ƙasar nan su 8,809 gaba, gyaran tsarin haraji, taka-tsantsan da sa-ido wajen kashe kuɗaɗe, sai kuma haɗin gwiwar bunƙasa tattalin arziki, kamar irin shirin haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Japan na dalar Amurka miliyan 30.9.

A jawabin sa, Ministan Kasafin Kuɗi, Alhaji Abubakar Bagudu, ya tabbatar tare da jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da aiki da gaskiya tare da amfani da bayyanannun hujjojin ƙididdiga, ba shaci-faɗi ba.

Ya ce tuni an fara aiki da kuɗaɗen kasafin 2025 a ɓangaren ayyukan gudanarwar gwamnati, irin su biyan albashi da kuma biyan basussuka da ake kan yi.

Tags: Abubakar BaguduKasafin KuɗiTanimu Yakubu
Previous Post

Rikici Ya Turnuƙe Bayan Sanata Ta Zargi Matar Gwamna Da Haifa Masa ‘Ya’yan Shegu

Next Post

Gargaɗi: An Hango Bala’in Ambaliyar Ruwan Sama A Jihohi 11 Ran Alhamis

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Gargaɗi: An Hango Bala’in Ambaliyar Ruwan Sama A Jihohi 11 Ran Alhamis

Gargaɗi: An Hango Bala'in Ambaliyar Ruwan Sama A Jihohi 11 Ran Alhamis

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!