• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Raddin Tinubu ga ‘yan adawa: Ku ne kuka jefa Nijeriya cikin yunwa da talauci

WAKILIN MU by WAKILIN MU
October 24, 2026
in Siyasa
A A
0
Raddin Tinubu ga ‘yan adawa: Ku ne kuka jefa Nijeriya cikin yunwa da talauci
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da mataimakin sa, Kashim Shettima, a taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027, yau a Kaduna 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da mataimakin sa, Kashim Shettima, a taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027, yau a Kaduna 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su sake ba shi damar mulki a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairu, 2027, yana mai alƙawarin cigaba da kawo wadata, daidaito da cigaba idan aka sake zaɓen sa.

Tinubu ya yi wannan kira ne yau Asabar a Kaduna, yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Shugaban ya gode wa al’ummar Jihar Kaduna bisa goyon bayan da suka ba shi a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, yana mai cewa ƙuri’un su sun taimaka masa wajen samun nasarar zama shugaban ƙasa.

“Na sake dawowa domin gode muku kan wannan goyon baya, sannan in nemi ku sake ba ni damar mulki a karo na biyu, domin cika alƙawarin samar da wadata, cigaba da samun nasara,” inji shi.

Dandazon magoya bayan APC a taron yau a Kaduna

Tinubu ya buƙaci masu kaɗa ƙuri’a da su tabbatar sun mallaki katin zaɓe (PVC), tare da shiga zaɓen da za a gudanar a shekara mai zuwa.

Shugaban ya kuma mayar da martani ga ‘yan adawa kan sukar da suke yi wa gwamnati dangane da matsalolin yunwa da talauci, inda ya zarge su da haddasa matsalolin da suke suka a yanzu.

“Ina jin ‘yan adawa suna magana kan yunwa da talauci. Wa ya haddasa su? Su ne. Su suka haddasa yunwar da talaucin. Mu kuma muna ƙoƙarin kawar da su,” inji shi.

Tinubu ya ce gwamnatin sa na ƙoƙarin magance ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta, yana mai cewa ana biyan albashi a kan lokaci, yayin da gwamnoni ke aiwatar da shirye-shiryen cigaba a jihohin su.

Tinubu ya bayyana jin daɗin sa da ayyukan gwamnonin APC, yana mai cewa yana alfahari da ƙoƙarin da suke yi wajen bunƙasa jihohin su.

Ya kuma soki ‘yan adawa, yana mai cewa fushi da sukar gwamnati ne kawai suke da shi, ba tare da wani abin kirki da za su iya gabatarwa ga al’umma ba.

Shugaban ya lissafa samar da wadata, daidaito, bunƙasa tattalin arziki, farfaɗowa da samar da damarmaki a matsayin wasu daga cikin manufofin gwamnatin sa, tare da gargaɗin jama’a da kada su yarda a yaudare su da bayanan ƙarya daga abokan hamayyar sa.

Ya kuma kare matakin cire tallafin man fetur, yana mai cewa wannan mataki ya zama tarihi.

Tinubu ya yi alƙawarin yaƙi da cin hanci da rashawa, sauya bayanan takardun kuɗaɗe da safarar kayayyaki ta haramtacciyar hanya, tare da neman ƙarin goyon bayan ‘yan Nijeriya.

Ya buƙaci masu kaɗa ƙuri’a da su fito ƙwan su da kwarkwatar su a ranar 16 ga Janairu, 2027, domin zaɓar APC a dukkan matakan zaɓe, ciki har da shugaban ƙasa, gwamnonin jihohi, Sanatoci, ‘yan Majalisar Wakilai da ‘yan majalisun dokokin jihohi.

Shugaban ya gode wa shugabannin APC, gwamnonin ta da matasa bisa goyon bayan da suke ba shi, yana mai alƙawarin samar da kyakkyawar makoma ga ‘yan Nijeriya.

“Matasan mu, na gode muku. Mun yi muku alƙawarin kyakkyawar makoma da gobe mai kyau,” inji shi.

Taron na Kaduna shi ne farkon yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Tags: APCKadunaShugaba Bola Ahmed Tinubutaroyaƙin neman zaɓezaben2027
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da tashoshin wutar lantarki huɗu a Kano

Next Post

Arewa-Maso-Yamma na tare da Tinubu don wa’adi na biyu, cewar Uba Sani

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf
Siyasa

Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf

November 23, 2026
Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa
Siyasa

Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa

November 20, 2026
Next Post
Arewa-Maso-Yamma na tare da Tinubu don wa’adi na biyu, cewar Uba Sani

Arewa-Maso-Yamma na tare da Tinubu don wa’adi na biyu, cewar Uba Sani

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!