Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa yankin Arewa maso Yamma na goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai bayyana tabbacin cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na Janairu 2027.
Uba Sani ya bayyana hakan ne bayan ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC cikin nasara a Kaduna, ranar Asabar, 24 ga Oktoba, 2026.
A cikin wata sanarwa da ya fitar bayan taron, gwamnan ya ce ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ya nuna ƙarfin jam’iyyar, haɗin kan shugabannin ta da kuma ƙudirin mambobin ta na ganin Tinubu ya samu wa’adi na biyu.
Ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin tarihi ga Jihar Kaduna, yana mai cewa halartar gwamnonin jihohi, shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki da magoya baya ya ƙara nuna muhimmancin taron.
Gwamnan ya kuma nuna godiyar sa ga dubban al’ummar da suka yi jerin gwano a kan tituna tun daga filin jirgin sama zuwa filin wasa domin tarbar shugaban ƙasa, yana mai bayyana liyafar a matsayin alamar ci gaba da amincewar da suke da ita ga shugabancin Tinubu.
A cewar sa, tarbar da al’ummar suka yi wa shugaban ƙasar ta isar da saƙo karara cewa alaƙar da ke tsakanin Tinubu da al’ummar yankin na nan daram.
Uba Sani ya ce shirin Ajandar Sabunta Fata Renewed Hope Agenda na gwamnatin Tinubu ya haifar da zuba jari a fannonin gine-ginen ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, noma, sufuri da sauran muhimman sassa a Jihar Kaduna da ma faɗin yankin Arewa maso Yamma.

Ya bayyana cewa waɗannan ayyuka suna taimakawa wajen magance matsalolin yau da kullum da al’umma ke fuskanta tare da biyan wasu buƙatu da muradun al’ummomin yankin.
Ya ƙara da cewa nasarorin da aka samu sun ƙara ƙarfafa amincewar jama’a da gwamnatin, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da ayyukan da ake yi domin samun ƙarin nasarori.
Sai dai gwamnan ya jaddada cewa neman ci gaba da mulki yana tattare da alhakin gina kan nasarorin da aka riga aka samu, da kuma ƙara himma wajen inganta walwalar ’yan Nijeriya.
Ya ce ya zama wajibi a mayar da haɗin kan da aka nuna a wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen zuwa ayyukan haɗin gwiwa domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.
“Daga Kaduna, saƙon mu a bayyane yake kuma babu ja da baya: Arewa na tsaye tsayin daka tare da Shugaba Tinubu,” in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa shugabannin siyasa da magoya bayan jam’iyyar a yankin a shirye suke su yi gangamin wayar da kan jama’a da kuma tattara ƙuri’u domin samun gagarumar nasara a zaɓen Janairu 2027.
Gwamnan ya sake tabbatar da aniyar sa ta yin aiki tare da sauran shugabannin APC da magoya bayan ta domin tabbatar da sake zaɓen Tinubu da kuma ciyar da manufar samar da Nijeriya mai ƙarfi da wadata gaba.







