Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN), tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar Kano, ta ƙaddamar da tashoshin wutar lantarki guda huɗu da za su ƙara ƙarfin isar da wutar lantarki da megawatt 544.
Tashoshin suna Walalambe, Kumbotso, Dakata da Ɗan’agundi, Kano, kuma ana sa ran za su inganta samar da wutar lantarki ga masana’antu, ’yan kasuwa da mazauna jihar.
A Walalambe, an girka tiransifoma biyu masu ƙarfin MVA 40 kowannen su, wanda ya samar da ƙarin ƙarfin megawatt 80. Kumbotso kuma ta samu ƙarin tiransfoma masu ƙarfin MVA 300 a matakin 330kV da kuma tiransifoma masu ƙarfin MVA 100. Haka kuma, Dakata da Ɗan’agundi kowannen su ya samu ƙarin tiransifoma mai ƙarfin MVA 100 a matakin 132kV. Waɗannan ayyukan za su taimaka wajen rage cinkoson kaya a wasu tashoshi tare da ba da damar samar da wutar lantarki ga buƙatun da a baya ba a iya biya ba.
A Walalambe, an samar da layukan fitar da wuta guda shida da za su taimaka wajen samar da wutar lantarki ga Masana’antar Tokarawa, hanyar Eastern Bypass, Titin Maiduguri, Titin Hadejia da yankunan da ke kewaye.
Kamfanin masana’antu na Lee Group ya koma amfani da wutar lantarkin gwamnati bayan shafe fiye da shekaru 30 yana samar da tasa wutar da kan sa.
Haka kuma, tashar Ɗan’agundi, wadda gobara ta lalata, ta samu damar dawo da wani babban ɓangare na ƙarfin ta na samar da wutar lantarki ga cikin birnin Kano, fadar Mai Martaba Sarkin Kano da sauran yankunan da ke kusa.
A cikin wata sanarwa da mai ba wa ministan wutar lantarki shawara kan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Adeola Labzy, ya sanya wa hannu, ya bayyana ayyukan a matsayin wata shaida ta ƙudirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da Ajandar Sabuwar Fata.
Sanarwar ta ce zuba jari a irin waɗannan muhimman ababen more rayuwa zai ƙarfafa masana’antu, ƙananan sana’o’i, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’umma, tare da mayar da wutar lantarki ginshiƙin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya.







