Tsohon Babban Lauyan Tarayya (AGF) Kuma Ministan Shari’a a zamanin gwamnatin Buhari, Abubakar Malami, SAN, ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar umurnin wucin-gadi da kotu ta bayar na a ƙwace wasu kadarorin sa kamar yadda Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta yi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar 6 ga Janairu ce Mai Shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umurnin wucin-gadi na ƙwace kadarori 57 da ake zargin an same su ne ta hanyoyin da ba su halatta ba.
An ce kadarorin suna da alaƙa da Malami da ’ya’yan sa biyu, Abdul’aziz Malami da Abdur Rahman Malami.
Yayin yanke hukunci kan buƙatar gaggawa (ex parte) da EFCC ta shigar, Mai Shari’a Nwite ya ce akwai hujjojin farko da ke nuna an samu kadarorin ne ta hanyoyin haram, don haka a ƙwace su na ɗan lokaci zuwa ga Gwamnatin Tarayya.
Alƙalin ya kuma umurci EFCC da ta wallafa umurnin ƙwace kadarorin a jarida ta ƙasa, tare da gayyatar duk masu ruwa da tsaki su bayyana a gaban kotu cikin kwanaki 14 domin nuna dalilin da ya sa bai kamata a bayar da umurnin ƙwace na ƙarshe ba.
Sai dai a cikin wata ƙara ta sanarwa (motion on notice), Malami ta hannun lauyoyin sa ƙarƙashin jagorancin Joseph Daudu, ya yi zargin cewa EFCC ta samu umurnin wucin-gadin ne ta hanyar ɓoye muhimman bayanai da bayar da bayanan ƙarya.
Malami ya roƙi kotu da ta yi watsi da shari’ar domin kauce wa “sakamako masu karo da juna da maimaita shari’a”, yana mai cewa shari’ar ta saɓa masa ’yancin mallaka, ƙa’idar rashin laifi har sai an tabbatar, da kuma ’yancin rayuwar iyali.
A cikin takardar ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/20/2026 da aka shigar a ranar 27 ga Janairu, tsohon AGF ɗin ya ƙalubalanci ƙwace kadarori uku musamman, waɗanda aka lissafa a matsayin lambobi 9, 18 da 48 a cikin buƙatar gaggawar EFCC.
Kadarorin sun haɗa da fili mai lamba 157, Lamiɗo Crescent, Nasarawa GRA, Kano, wanda aka saya a ranar 31 ga Yuli, 2019; da wani bene mai ɗaki da yawa tare da sashen ma’aikata da ke Lamba 12, Titin Yalinga, kusa da Adetokunbo Ademola Crescent, Wuse II, Abuja, wanda aka saya a Oktoba 2018 kan naira miliyan 150; da kuma Ginin ADC Kadi Malami Foundation, da aka saya kan naira miliyan 56.
Malami yana roƙon kotu da ta soke umurnin wucin-gadi na ƙwace kadarorin yadda ya shafi waɗannan kadarori uku, tare da hana EFCC tsoma baki a ikon mallaka, riƙewa da amfani da su.
Ya kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin kadarorin ana riƙe da ita ne a amana (trust) domin gadon marigayi mahaifin sa, Kadi Malami.
A cikin hujjoji 14, Lauya Daudu ya ce ba a gabatar da wata hujjar farko (prima facie) da ke danganta kadarorin da wani laifi ko aikin haram ba.
Ya ce Malami ya bayyana kadarorin da aka lissafa a matsayin lambobi 9 da 18 a cikin takardun bayyana kadarori da ya miƙa wa Hukumar Ka’idojin Halayen Ma’aikata (CCB) a shekarun 2019 da 2023, yayin da kadara ta 48 kuma ana riƙe da ita a amana domin gadon mahaifin sa.
“An bayyana waɗannan kadarori, ƙimar su da tushen mallakar su a fili a cikin takardun bayyana kadarori daga shekarar 2019 zuwa 2023,” inji Daudu.
Babban lauyan ya kuma lissafa hanyoyin samun kuɗin da Malami ya bayyana, ciki har da albashi, alawus, zama memba a kwamitoci da hukuma, sayar da kadarori, ribar kasuwanci, rancen kuɗi ga kasuwanci, kyaututtukan gargajiya daga abokai, da kuma kuɗin da aka samu daga ƙaddamar da littafin da tsohon AGF ya wallafa.
Ya ce Malami ya bayyana hanyoyin samun kuɗin sa a cikin takardun CCB da suka haɗa da:
Ya ce: “Naira 374,630,900 daga albashi, estacode, alawus na barin aiki da sauran su;
“Alawus na zama memba a kwamitoci/hukumomi kamar Hukumar Kula da Ayyukan Shari’a ta Tarayya, Hukumar Kula da Ayyukan Shari’a ta Babban Birnin Tarayya, Kwamitin Izinin Lauyoyi, da wani babban kwamitin shugaban ƙasa,” inji takardar.
“Naira 574,073,000 daga sayar da kadarori; Naira 10,017,382,684 juyin kasuwanci; Naira 2,522,000,000 rance ga kasuwanci; Naira 958,000,000 a matsayin kyaututtukan gargajiya daga abokai na kusa.”
Daudu ya kuma bayyana cewa an samu jimillar Naira 509,880,000 daga taron ƙaddamarwa da gabatar da littafin Malami mai taken ‘Contemporary Issues on Nigerian Law and Practice, Thorny Terrains in Traversing the Nigerian Justice Sector: My Travails and Triumphs’.
“Waɗannan hanyoyin samun kuɗi, tare da ribar kasuwanci da ake ci gaba da samu tsawon shekaru, sun nuna a sarari cewa an samu kadarorin da ake son ƙwacewa ta halattattun hanyoyi, kamar yadda aka bayyana a takardun bayyana kadarori,” inji shi.
“An samu umurnin wucin-gadi ne ta hanyar ɓoye muhimman bayanai da bayar da bayanan ƙarya.
“Babu wata hujjar farko da aka gabatar wa wannan kotu mai girma daga mai nema/mai ƙara (EFCC) da ke tabbatar da cewa kadarorin da ake danganta wa mai amsa/mai nema (Malami) sun cancanci a ƙwace su a miƙa su ga Gwamnatin Tarayya.”
Sai dai shari’ar ba ta ci gaba ba domin ba a saka ta a jerin shari’o’in ranar ba. An saurari shari’ar ne a lokacin hutun kotu, kuma bayan kammala shari’o’in hutun, alƙalin da ke sauraron shari’ar ya mayar da kundin shari’ar ga Babban Alƙalin kotu domin sake rabawa.
An kuma lura cewa lauyoyi da dama sun hallara a kotu a ranar 27 ga Janairu, bayan sun shigar da takardu a madadin abokan hulɗar su domin dakatar da ci gaba da shari’ar ƙwace kadarorin na ƙarshe.
Malami, wanda EFCC ke tuhuma da laifin wanke kuɗi, a halin yanzu yana tsare a ofishin Hukumar Tsaro ta Farar Hula (DSS) bisa wata tuhuma daban da ta shafi tallafa wa ta’addanci.
Karɓar kyauta ga jami’an gwamnati haramun ne – Lauyoyi
Lauyoyi sun bayyana cewa doka ba ta halatta wa ma’aikatan gwamnati karɓar kyaututtuka ko alfarma yayin da suke kan aiki ba.
Tsohon shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA), reshen Garki, Obioma Ezenwobodo, Esq, ya ce: “Akwai dokoki da ke hana jami’in gwamnati karɓar kyauta domin bayar da alfarma ko kuma abin da zai haifar da rikicin amfani.”
Ya ƙara da cewa idan masu gabatar da ƙara suka tabbatar da zarge-zargen nan a kan Malami, zai yi masa wahala ya kare kan sa.
Ya ce akwai muhimman dokoki da ke haramta wa jami’in gwamnati karɓar kyauta a Nijeriya—musamman idan kyautar na iya shafar aikin sa ko ta zama cin hanci.
Haka nan, Nnamdi Ahaaiwe, Esq ya ce bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999 (da aka yi wa gyara), Jadawali na Biyar, Sashe na I – Ka’idojin Halayen Ma’aikatan Gwamnati, sakin layi na 6 ya ce:
“Jami’in gwamnati ba zai nemi ko karɓi wata dukiya ko fa’ida domin kan sa ko wani ba saboda wani abu da ya aikata ko ya ƙi aikatawa yayin gudanar da aikin sa.
“Karɓar kyaututtuka ko fa’ida daga kamfanoni, ’yan kasuwa, ko mutanen da ke da kwangila da gwamnati ana ɗaukar sa a matsayin saɓa wa doka, sai dai in an tabbatar da akasin haka.”
Ya ƙara da cewa akwai wasu ƙananan keɓantattu. “Jami’in gwamnati na iya karɓar kyaututtuka na kai daga dangi ko abokai na kusa gwargwadon al’ada da lokutan da aka amince da su. Kyaututtuka a lokutan bukukuwa na jama’a ana ɗaukar su a matsayin kyauta ga hukuma, ba ga mutum ba. Hukumar CCB da Kotun Code of Conduct ne ke kula da karya doka.”
Ya kuma ambaci Dokar Hana Cin Hanci da Laifuka Masu Alaƙa ta 2000 (ICPC Act) wadda ke haramta karɓar kyauta ko alfarma ta cin hanci (wadda ta haɗa da kuɗi, kyauta, rance, lada, dukiya ko wata fa’ida da ake nufi da shafar aiki). Muhimman sassa sun haɗa da:
– Sashe na 8: Ya haramta wa jami’in gwamnati neman ko karɓar duk wata alfarma a matsayin dalili ko lada saboda aikin sa ko nuna alfarma/ƙyama. Hukunci: ɗaurin shekaru har bakwai.
– Sashe na 18: Ya shafi cin hancin jami’an gwamnati, ciki har da karɓar alfarma don aiwatar da aiki, bayar da kwangila ko nuna alfarma. Hukunci: ɗaurin shekaru biyar tare da aikin wahala.
– Sashe na 19: Duk jami’in da ya yi amfani da muƙamin sa wajen amfanar da kan sa, ’yan’uwan sa ko abokan hulɗar sa ta hanyar cin hanci ya aikata laifi (hukunci: ɗaurin shekaru biyar ba tare da tara ba). Dokar ta fayyace “alfarma” da ta haɗa da kyaututtuka da gudunmawa da aka bayar ko aka yi alƙawari domin shafar aiki.
Kungiyar Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC) ta yi kira da a sanya iyaka ga adadin kyaututtukan da jami’in gwamnati zai iya karɓa yayin aiki.
Da yake martani kan bayanan Malami, Daraktan Zartarwa na ƙungiyar, Auwal Rafsanjani, ya ce kyaututtuka da alfarma a yayin aikin jami’in gwamnati cin hanci ne.
“Akwai iyaka ga irin kyaututtukan da jami’in gwamnati zai iya karɓa, domin hakan na iya zama cin hanci. A matsayi na na ɗan ƙasa, dole mu ɗauki matsaya,” inji shi.
Wani ɗan fafutukar ƙungiyoyin farar hula daga Kano, Kwamared Akibu Hamisu, ya bayyana iƙirarin Malami a matsayin yunƙurin halatta tara dukiya ta haramtacciyar hanya.
Hamisu, wanda shi ne wanda ya kafa kuma daraktan Resource Management for Accountability and Development Centre, ya yi wannan jawabi a ranar Lahadi yayin da yake martani kan shaidar Malami a gaban kotu, inda aka ce tsohon AGF ya bayyana cewa ya karɓi kyaututtuka da suka kai kusan Naira biliyan ɗaya, kuma yana samun albashi har Naira miliyan 300 a wata yayin da yake kan aiki.
A cewar Hamisu, waɗannan iƙirari—idan gaskiya ne—suna tayar da manyan tambayoyi game da gaskiya da bin dokokin hana cin hanci na Najeriya.
“Abin mamaki ne kuma abin damuwa ga tsohon Babban Lauyan Tarayya ya bayyana a kotu ya yi irin waɗannan iƙirari,” inji shi. “Faɗin cewa ana samun kusan Naira miliyan 300 a wata a matsayin albashi na buƙatar bincike, domin babu tsarin albashi ko alawus da ya dace da irin waɗannan adadi ga masu riƙe da muƙaman gwamnati.”
Ya jaddada cewa ko da an ƙara alawus, adadin bai dace da abin da aka amince da shi ga masu muƙaman siyasa a Nijeriya ba, yana mai cewa, “Har ma ana shakka ko Shugaban Ƙasa yana samun irin wannan adadi a wata.”
Hamisu ya kuma soki hujjar kiran manyan kuɗaɗe a matsayin “kyaututtuka”, yana mai cewa dokokin hana cin hanci sun fayyace kyaututtukan da jami’an gwamnati ke karɓa a yayin aiki a matsayin abin da zai iya zama cin hanci.
“Duk wata kyauta ko alfarma da aka ba jami’in gwamnati yayin da yake kan aiki an haramta ta a ƙarƙashin dokokin hana cin hanci,” inji shi. “Tambayar ita ce: wa ya ba da waɗannan kyaututtuka, bisa wane dalili, kuma me ya sa ba a karɓe su kafin ɗaukar muƙamin gwamnati ba?”
Ya ƙara da cewa waɗannan ikirari, maimakon su zama kariya, na iya ƙara haifar da shakku game da amincin tsohon ministan da bin ƙa’idojin aikin gwamnati.
Hamisu ya buƙaci kotu da hukumomin yaƙi da cin hanci su zurfafa bincike kan batutuwan da aka bijiro da su, yana mai cewa gaskiya da riƙon amana su ne mabuɗan dawo da amincewar jama’a ga shugabanci.







