• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Cikar Neja shekara 50: Minista ya yi kira da a sabunta ƙudiri don samun makoma mai ƙarfi

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
February 3, 2026
in Labarai
A A
0
Cikar Neja shekara 50: Minista ya yi kira da a sabunta ƙudiri don samun makoma mai ƙarfi
Daga hagu: Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da Gwamna Mohammed Bago

Daga hagu: Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da Gwamna Mohammed Bago

Jihar Neja ta cika shekara 50 da kafuwa a ranar Talata, inda aka yi kiran a sabunta ƙudirin haɗin kai da tabbatar da cigaba mai ɗorewa domin gina makoma mai ƙarfi ga jihar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ta taya murna a ranar Talata, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa wannan biki shaida ce ta juriya, sadaukarwa, da ɗorewar fata ta mutanen jihar waɗanda suka himmatu wajen samun cigaba.

Idris, wanda ɗan asalin Neja ne, ya ce bikin ba wai na tunawa da wucewar shekarun da suka shuɗe kawai ba ne, dama ce ta waiwayen tafiyar da mutanen Jihar Neja suka yi, nasarorin da aka samu, ƙalubalen da aka fuskanta, da kuma alƙawarin neman kyakkyawar makoma da ke gaba.

Ministan ya tunatar da cewa an ƙirƙiri Jihar Neja ne a cikin 1976 tare da jihohin Imo, Binuwai, Ogun, Ondo da Osun, kuma tun daga sannan ta samu matsayi na musamman a tarihin Nijeriya.

Ya bayyana cewa a matsayin ta na jiha mafi girma a ƙasar nan ta fuskar faɗin ƙasa, tare da bayar da gagarumar gudunmawa da take yi ga Gundumar Babban Birnin Tarayya (FCT), Jihar Neja na da yalwar ƙasa mai amfani ga noma da kuma muhimman albarkatu.

A cewar sa, jihar wata matattarar muhimman madatsun ruwa ce wadda ke samar da lantarki kamar dam ɗin Kainji, Jebba da Shiroro, waɗanda ke taka rawar gani wajen cigaban Nijeriya ta hanyar bai wa masana’antu wuta, tallafa wa noma, da kuma samar da hanyoyin dogaro da kai a faɗin ƙasar nan.

Yayin da ya amince cewa Jihar Neja, kamar sauran jihohi, ta ɗore a tafarkin mulkin dimokiraɗiyya duk da sauye-sauyen zamani, Ministan ya jaddada cewa ya kamata bikin ya zama wata dama ta tsara kyakkyawar hanya zuwa ga cigaba mai haɗa kowa da kowa da sauyi mai ɗorewa.

Ya ce rarraba jihar zuwa yankunan Neja ta Gabas, Neja ta Arewa da Neja ta Kudu ya ƙara jaddada muhimmancin haɗin kai, shugabanci nagari, haɗewar al’adu, da kuma manufofi masu ma’ana.

Idris ya ce tafiyar gina Jihar Neja mai cikakken haɗin kai da wadata yana ci gaba da gudana, inda ya ƙara da cewa a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ana aiwatar da tsare-tsare na farfaɗo da tattalin arziki a faɗin ƙasa, inda Jihar Neja ke ci gaba da cin gajiyar shirye-shiryen bunƙasa tattalin arziki, sabunta ababen more rayuwa, da gyaran cibiyoyi.

Ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su fuskanci halin da ake ciki a yanzu, su ƙarfafa cibiyoyi, sannan su himmatu wajen samar da shugabanci mai amfani ga jama’a.

Ya kuma jaddada muhimmancin karrama waɗanda suka kafa Jihar Neja da sauran masu kishin ƙasa da suka shimfiɗa tubalin dimokiraɗiyya shekaru 50 da suka gabata.

A cewar Ministan, Jihar Neja tana kan wani muhimmin mataki yayin da ta kai shekara 50, inda ta hanyar rungumar wannan labari na bai ɗaya na fata, sanin ya-kamata da haɗin kai, za a iya sabunta ƙudiri na gina makomar da za ta cika burin al’ummar jihar.

Ya yi kira ga al’ummar Jihar Neja da su ba Gwamnan Jihar, Umaru Mohammed Bago, cikakken goyon bayan da yake buƙata wajen ciyar da jihar gaba.

Tags: MohammedBagoMohammedIdrisNejashekaru50
Previous Post

Sojojin Amurka sun ce an turo wasu dakarun su zuwa Nijeriya

Next Post

Na samu naira miliyan 958 ne a matsayin kyaututtuka, naira miliyan 374 kuma albashi da alawus – Malami ya shaida wa kotu

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Kotu ta tsare Malami, matar sa da ɗan sa a Gidan Gyaran Hali na Kuje

Na samu naira miliyan 958 ne a matsayin kyaututtuka, naira miliyan 374 kuma albashi da alawus – Malami ya shaida wa kotu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!