• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ministan Yaɗa Labarai ya yi alhinin ‘yan jarida bakwai na Gombe da suka rasu a haɗarin mota

ALI KANO by ALI KANO
December 30, 2025
in Labarai
A A
0
Ministan Yaɗa Labarai ya yi alhinin ‘yan jarida bakwai na Gombe da suka rasu a haɗarin mota
Alhaji Mohammed Idris

Alhaji Mohammed Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana matuƙar kaɗuwa da alhini kan rasuwar wasu ‘yan jarida bakwai a wani mummunan haɗarin mota guda ɗaya da ya faru a yankin Gombe ta Kudu, Jihar Gombe, a ranar Litinin.

Lamarin ya faru ne da yammacin Litinin yayin da ‘yan jaridar suke dawowa daga bikin aure a Mazaɓar Sanatan Gombe ta Kudu.

Rahotanni sun nuna cewa sun yi tafiyar ne domin halartar bikin auren wani abokin aikin su daga Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA).

A cewar bayanan farko daga Kwamandan Sashen Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya (FRSC) a Jihar Gombe, Samson Kaura, haɗarin ya kasance mai muni kuma ya yi sanadin mutuwar mutanen.

Ministan ya bayyana wannan ibtila’i a matsayin babban rashi mai ratsa zuciya ga al’ummar kafafen yaɗa labarai da kuma ƙasa baki ɗaya, inda ya ce ‘yan jaridar sun kasance muryoyi masu jajircewa da ke wayar da kan jama’a cikin jarumtaka, gaskiya da ƙwarewa.

Ya ce: “Wannan lokaci ne mai raɗaɗi ƙwarai. Nijeriya ta rasa muryoyi masu sadaukarwa da suka riƙa sanarwa, ilimantarwa da tsayawa kan gaskiya. Rashin su babban koma-baya ne gare mu duka.”

Idris ya miƙa ta’aziyyar sa ga Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), Majalisar ‘Yan Jarida ta Jihar Gombe, da kuma musamman iyalai, abokai da abokan aikin mamatan.

Ya yi addu’ar Allah ya ba su ƙarfin jure wannan babban rashi, yana cewa, “Tunanin mu da addu’o’in mu suna tare da iyalan su da masoyan su.

“Allah Maɗaukakin Sarki ya ba su haƙuri, ya kuma jiƙan su da rahama, ya sa sun huta.

“Mun tsaya tsayin daka tare da NUJ da dukkan al’ummar kafafen yaɗa labarai a wannan lokaci mai wahala. Dole ne mu ci gaba da aiki tare domin inganta matakan tsaro ga waɗanda ke hidimta wa ƙasa a kullum,” inji shi.

Ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya na tare da iyalan da abin ya shafa da kuma al’ummar kafafen yaɗa labarai a wannan lokaci na jimami.

Tags: alhiniGombehaɗarijajeMohammed Idrisrasuwata'aziyya
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da zargin kai wa ‘yan adawa hari, ta jaddada ƙudirin bin doka da oda

Next Post

Sababbin dokokin haraji za su fara aiki ranar 1 ga Janairu kamar yadda aka tsara – Tinubu

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
Sababbin dokokin haraji za su fara aiki ranar 1 ga Janairu kamar yadda aka tsara – Tinubu

Sababbin dokokin haraji za su fara aiki ranar 1 ga Janairu kamar yadda aka tsara – Tinubu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!