Ministan Kuɗi kuma Ministan Daidaita Harkokin Tattalin Arziki, Mista Wale Edun, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin Tinubu na ƙarfafa fannin kiwon lafiya ta hanyar ƙara zuba jari da inganta haɗin gwiwar gwamnati da ‘yan kasuwa, yana mai cewa ƙarin kasafin kuɗi na baya-bayan nan ya nuna ƙudiri mai ƙarfi na gina tsayayyen ginshiƙin ababen more rayuwa na zamantakewa.
Ministan ya bayyana hakan ne a yayin rattaba hannu kan wata yarjejeniya a Abuja tsakanin Hukumar Zuba Jari ta Ƙasa ta Nijeriya (NSIA), da Kamfanin Ba da Lamuni na Duniya (IFC), da MedServe, wadda ke da nufin faɗaɗa samun damar ayyukan bincike na cututtuka (diagnostics), kula da cutar daji (oncology), da cututtukan zuciya (cardiology) a faɗin ƙasar.
A jawabin nasa, Edun ya bayyana faɗaɗar cibiyoyin kula da cutar daji na NSIA a matsayin hujja cewa za a iya gina ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya na duniya a cikin gida, lamarin da ke samar da ayyukan yi, jawo jarin kuɗi, da rage yawan kuɗaɗen da Nijeriya take kashewa wajen neman magani a ƙasashen waje.
Ya jaddada cewa kiwon lafiya ba wai kawai wata buƙata ta jama’a ba ce, har ila yau fanni ne na bunƙasa tattalin arziki, yana mai cewa ƙarfafa ƙarfin cikin gida yana ƙara yawan aiki, yana riƙe jarin kuɗi a cikin tattalin arzikin ƙasa, tare da tallafa wa bunƙasar jarin ɗan’adam na dogon lokaci.

Haka kuma ya yaba da rawar da IFC ta taka, yana bayyana yarjejeniyar a matsayin tsari mai faɗaɗawa wanda ya haɗa da samar da kuɗaɗe da ƙwarewar fasaha domin buɗe ƙofofin jarin ‘yan kasuwa da kuma faɗaɗa samun kulawar lafiya, tare da ƙarin tallafi daga Bankin Duniya.
Ministan ya yi kira da a kwaikwayi tsarin NSIA MedServe a sauran fannoni, yana mai bayyana shi a matsayin misali na cigaba mai haɗa kowa da kowa, ƙarfafa ayyukan jama’a, da gina juriya ta tattalin arziki na dogon lokaci.
Taron ya samu halartar Ministan Ƙasa na Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, da Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Alhaji Abubakar Atiku Bagudu.








