• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci a kwantar da hankali kan dakatar da gidan rediyon Badeggi FM

ALI KANO by ALI KANO
August 3, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Ambaliyar Garin Mokwa
Alhaji Mohammed Idris, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai

Alhaji Mohammed Idris, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai

Alhaji Mohammed Idris, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalin su bayan dakatar da gidan rediyon Badeggi FM da ke Minna da Gwamnatin Jihar Neja ta yi.

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, shi ne ya bayar da umarnin rufe tashar , kamar yadda rahotanni suka nuna, a yayin wani taron faɗaɗa na tsangayar jam’iyyar APC da aka gudanar a Minna a ranar 1 ga Agusta.

Rahotanni sun ce gwamnan ya zargi rediyon da rashin bin ƙa’idar aiki a cikin shirye-shiryen sa da kuma tayar da zaune tsaye kan gwamnati.

Minista Idris ya bayyana damuwa da irin martanin da al’umma da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai suka nuna dangane da lamarin. Amma ya jaddada cewa hukumar da ke da hurumin dakatar da lasisin gidajen rediyo da talabijin ita ce Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), kamar yadda doka ta tanada.

Sanarwar da Gwamnatin Tarayya ta bayar kan lamarin ta ce: “Saboda haka, ministan yana maraba da matakin da Gwamnatin Jihar Neja ta ɗauka na kai koken da ta ke da shi kan zargin rashin ɗabi’a da Badeggi FM ta yi a hukumance zuwa ga NBC domin a warware batun.”

Idris ya roƙi dukkan ɓangarori da su kwantar da hankalin su, yana mai tabbatar da cewa NBC tana da tsarin da ya dace na warware irin waɗannan matsaloli cikin gaskiya da adalci.

Previous Post

Matakan gwamnatin Tinubu za su taimaka wajen kare haƙƙin mata da yara — Minista Imaan

Next Post

Matar Tinubu ta ƙaddamar da na’urorin musamman don gano cutar tarin fuka da magance ta

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post

Matar Tinubu ta ƙaddamar da na'urorin musamman don gano cutar tarin fuka da magance ta

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!