• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Abubakar Malami ya musanta zargin tallafa wa ta’addanci, ya yi tir da ‘shari’a a kafafen yaɗa labarai’

ALI KANO by ALI KANO
January 21, 2026
in Tsaro
A A
0
Abubakar Malami ya musanta zargin tallafa wa ta’addanci, ya yi tir da ‘shari’a a kafafen yaɗa labarai’
Alhaji Abubakar Malami, SAN

Alhaji Abubakar Malami, SAN

Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Alhaji Abubakar Malami, SAN, ya musanta zargin da ke yawo a kafafen yaɗa labarai cewa yana ɗaukar nauyin ta’addanci ko kuma an gano makamai a ofishin sa.

A cikin wata sanarwar manema labarai da hadimin sa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka, ya fitar, tsohon ministan ya bayyana rahotannin a matsayin “zarge-zargen da ba a tantance ba da ake gabatarwa kamar gaskiya.”

Sanarwar ta ce: “Ba a taɓa samun hukunci a kan Abubakar Malami, SAN, kan kowane laifi ba. Duk da haka, wasu sassan kafafen yaɗa labarai na ci gaba da gabatar da zarge-zarge, bincike da hasashe a matsayin hujjar laifi, wanda hakan ya saɓa wa ƙa’idar ɗaukar mutum a matsayin marar laifi da kuma bin ƙa’ida kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanada.”

Doka ya rubuta cewa: “Muna ƙin yarda gaba ɗaya da iƙirarin cewa an gano wani tarin makamai ko harsasai a kowane gida da ke da alaƙa da Abubakar Malami, SAN.

“Wannan iƙirarin ƙarya ne, bai da tushe, kuma bai da goyon bayan kowace hukuma, takardar kotu ko sanarwar doka. Ba a taɓa sanar da iyalin sa ko lauyoyin sa a hukumance game da irin wannan bincike ba.

“Haka nan, mun ƙin yarda da duk wani zargi ko shaguɓe da ke danganta Abubakar Malami, SAN, da ta’addanci, ɗaukar nauyin ta’addanci ko wasu ayyuka masu alaƙa da hakan.

“An gabatar da irin waɗannan iƙirarin ba tare da ambaton ko mutum ɗaya ba, ko ƙungiya, ko mu’amala, ko kwanan wata, ko wata hujja mai tabbaci ba, lamarin da ya sa suke hasashe marasa ma’ana.”

A cewar sanarwar, “Tun bayan kama shi da DSS ta yi a ranar Litinin, an hana Abubakar Malami, SAN, samun damar ganawa da iyalin sa, tawagar lauyoyin sa da abokan hulɗar sa.

“Wannan tsawaita keɓancewa na tayar da sahihiyar damuwa game da lafiyar sa, walwalar sa da haƙƙoƙin sa da Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar, ciki har da samun lauya da kuma hulɗa da iyali.

“Muna kuma nuna damuwa kan wahala da nauyin damuwa da aka jefa iyalin sa da ma’aikatan sa ciki sakamakon rahotannin da ke tayar da hankali da labaran da ba a tantance ba.

“Ya dace a lura cewa Abubakar Malami, SAN, babban jigo ne a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), kuma ya bayyana a fili aniyar sa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar Kebbi a zaɓen 2027.

“Bisa wannan tushe, ba za a iya yin watsi da alamar siyasa da ke kewaye da wannan batu ba. Dole ne hanyoyin shari’a su kasance masu zaman kan su daga tasirin siyasa.

“Abubakar Malami, SAN, na nan daram kan bin doka da oda da kuma ƙa’idojin shari’a. Muna kira ga kafafen yaɗa labarai da su dakatar da shari’ar kanun labarai, su bambanta zargi da gaskiya a sarari, kuma su bar hanyoyin shari’a su yi aikin su ba tare da son zuciya ba.”

Tags: AbubakarMalamiEFCCshari'azargi
Previous Post

Yadda Al-Barnawi ya sa na shiga Boko Haram — Wanda ake zargi

Next Post

Bikin Argungu alama ce ta haɗin kan ƙasa da samun karɓuwa a idon duniya – Gwamnatin Tarayya

Related Posts

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma
Tsaro

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma

April 25, 2026
Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos
Tsaro

Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos

April 17, 2026
‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya
Tsaro

‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya

April 16, 2026
Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su
Tsaro

Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su

April 15, 2026
Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba – Gwamnatin Tarayya
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta kare harin jirgin sama a Jilli, ta ba da umurnin bincike

April 14, 2026
An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno
Tsaro

An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno

April 13, 2026
Next Post
Bikin Argungu alama ce ta haɗin kan ƙasa da samun karɓuwa a idon duniya – Gwamnatin Tarayya

Bikin Argungu alama ce ta haɗin kan ƙasa da samun karɓuwa a idon duniya – Gwamnatin Tarayya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!