Haramtacciyar ƙungiyar Jama’ar Asalin Biyafra, wato Indigenous People of Biafra (IPOB), ta ce shugaban ta, Nnamdi Kanu, ya bayar da umurnin soke gaba ɗaya dokar nan da suka kafa ta zaman dirshan a gida na duk Litinin a faɗin Kudu-maso-Gabas, wanda zai fara aiki daga ranar 9 ga Fabrairu, 2026.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin kakakin IPOB, Emma Powerful, a wata sanarwar manema labarai da ya saki a yau Lahadi.
Ya ƙara da cewa umurnin ya fito ne kai-tsaye daga bakin Kanu.
Idan an tuna, ƙungiyar masu goyon bayan Biyafra ta tursasa wa jama’ar yankin dokar zama a gida tun a watan Agusta, 2021, domin nuna adawa da kama Kanu da kuma tsare shi da ake yi a Nijeriya.
A lokacin aiwatar da dokar, kasuwanni, makarantu, bankuna da ofisoshi sukan kasance a rufe.
Powerful ya ce da wannan sabon umurni, babu wata buƙata, hujja ko dalili da zai sa wani ya zauna a gida a ranar Litinin, yana mai jaddada cewa kasuwanni, makarantu, ofisoshi, harkokin sufuri da sauran ayyukan tattalin arziki dole su koma aiki gaba ɗaya kuma yadda ya kamata daga gobe Litinin.
Sanarwar ta ce: “IPOB, ƙarƙashin jagorancin ƙololuwa na Nnamdi Kanu, tana sanar da ɗaukacin duniya cewa dokar zama a gida ta Litinin a faɗin Kudu-maso-Gabas an soke ta a hukumance kuma har abada, daga gobe Litinin, 9 ga Fabrairu, 2026.
“Wannan umurni ya fito ne kai-tsaye daga Onyendu Mazi Nnamdi Kanu kan sa, wanda ya sake nuna sadaukarwar sa domin tabbatar da cewa ‘ya’yan mu suna komawa makaranta duk Litinin, kuma mutanen mu suna ci gaba da harkokin su na halal ba tare da tsoro, razana ko cin zarafi ba.
“Duk wanda ke shakka ya je Gidan Gyaran Hali na Sokoto domin tabbatarwa daga gare shi. Ba za mu ƙara ɓoyewa a ƙarƙashin uzurin ‘ba a iya tuntuɓar Onyendu domin tabbatarwa’ don ci gaba da taurin kai ko kasala ba. Zaman gida na Litinin ya ƙare. Wannan zamani ya wuce!
“Yanzu babu wata buƙata, hujja ko dalili da zai sa wani ya zauna a gida a ranar Litinin. Dole ne duk kasuwanni, makarantu, ofisoshi, harkokin sufuri da ayyukan tattalin arziki su koma aiki gaba ɗaya kuma yadda ya kamata daga gobe. Wannan shi ne bayyananne kuma tabbataccen umurnin Shugaban Ƙololuwar IPOB.”
Sanarwar ta ƙara da cewa Kanu “ya bayyana ƙarara cewa duk wani mutum ko ƙungiya da ke ƙoƙarin tilasta zama a gida daga yanzu, suna aiki ne saɓanin umarnin sa kai-tsaye. Irin waɗannan mutane maƙiyan al’ummar mu ne da kuma gwagwarmayar Biyafra. Za a bi su ko’ina suke a duniya, a tunkare su har sai an kawar da su gaba ɗaya.”
Ƙungiyar ta lura da cewa wasu mutane na ƙoƙarin haddasa tsoro, shirya hare-hare ko tsoratar da jama’a su zauna a gida ta hanyar yaudara.
“Sanin kowa ne cewa duk wani mutum ko ƙungiya da aka gano yana tilastawa ko taimakawa zama a gida za a tunkare su duk inda suke. Mutanen mu su kasance masu taka-tsantsan, cikin natsuwa kuma masu bin doka.
“A lokaci guda, IPOB tana so ta fayyace cewa babu wani gwamna da ke da ikon barazana, rusawa ko rufe kasuwancin ‘yan kasuwa da ƙarfi, idan sun zauna a gida bisa lamirin su domin nuna goyon baya ga shugaban su.
“Duk wani yunƙuri daga Gwamna Soludo ko wani gwamna na tsoratar da mutanen mu da barazanar rusawa ko rufe kasuwanni da karfi, za a yi masa tsayin daka.”
A cewar ƙungiyar, duk wani gyara, sake gina ko inganta kasuwanni da ke buƙatar matsuguni na wucin-gadi dole ne a yi shi ne kawai da amincewar dukkan masu ruwa da tsaki, tare da samar da isassun wuraren kasuwanci na wucin-gadi kafin fara irin waɗannan ayyuka.
“Maƙiyan mu sun taɓa yin nasara a baya wajen haddasa rikice-rikice da shuka saɓani a tsakanin mutanen mu. Kada mu bari su sake yin nasara. Mu al’umma ɗaya ne, da aka haɗa mu da makoma guda. Gwagwarmayar mu don ‘yanci ce, mutunci da adalci ga kowa, ba ga ‘yan Biyafra kaɗai ba.
“Saboda haka muna kiran dukkan mutanen mu a faɗin Kudu-maso-Gabas da su fito gobe, su buɗe shagunan su, su tafi aiki, su tura ‘ya’yan su makaranta ba tare da tsoro ba.
“Zaman gida na Litinin ya ƙare.”







