• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Ministan Abuja, Wike ya kafa gidan rediyo domin yaƙin neman zaɓen Tinubu a Jihar Ribas

New Citizen Hausa by New Citizen Hausa
February 8, 2026
in Siyasa
A A
0
Ministan Abuja, Wike ya kafa gidan rediyo domin yaƙin neman zaɓen Tinubu a Jihar Ribas
Wike a cikin situdiyon gidan rediyon Majority FM a Fatakwal a ranar ƙaddamar da shi

Wike a cikin situdiyon gidan rediyon Majority FM a Fatakwal a ranar ƙaddamar da shi

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya kafa sabon gidan rediyo mai suna Majority FM 89.5 domin yaƙin neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

Gidan rediyon yana cikin ofishin ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors da ke Fatakwal, Jihar Ribas.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara ƙaimi wajen shirye-shiryen siyasa domin yaƙin neman sake zaɓen Shugaba Tinubu a shekarar 2027 a yankin Kudu-maso-kudu.

A cikin wani bidiyo da ke yawo a intanet, an ga Wike yana duba sabon gidan rediyon, yana zagaya cikin situdiyo tare da ganawa da ma’aikata.

Ɗakin gabatar da shirye-shirye na Majority FM a Fatakwal

Majiyoyi sun bayyana wa Leadership cewa an tsara tashar ne domin ta zama wata muhimmiyar kafar yaɗa saƙonni ga ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors, wadda aka fi sani da goyon bayan ta ga gwamnatin Tinubu.

“Wannan tashar za ta riƙa karɓar saƙonni daga dukkanin unguwanni 666 na Jihar Ribas. Mun shirya domin wannan aiki, mun shirya domin 2027,” inji Wike yayin ƙaddamar da tashar.

Jaridar ta ce masu sa ido kan harkokin siyasa sun ce kafa Majority FM na ƙara tabbatar da tasirin Wike a sabuwar tafiyar siyasar jihar gabanin babban zaɓen 2027.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Wike da ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan yadda za a tafiyar da tashar rediyon.

Jami’ai a cikin situdiyon gidan rediyon Majority FM
Tags: JiharRibasMajorityFMNyesomWikeRenewedHopeAmbassadors
Previous Post

Bayan shekaru 37, Tinubu zai kai ziyarar musamman zuwa Birtaniya

Next Post

IPOB ta soke umurnin zama a gida na duk Litinin a Kudu-maso-Gabas

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci
Siyasa

Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci

April 28, 2026
A taron Ibadan, ‘yan adawa sun haɗa kai, sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027
Siyasa

A taron Ibadan, ‘yan adawa sun haɗa kai, sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027

April 25, 2026
Next Post
Kada ka damu, za mu sa a sake ka, Gwamnan Abiya ya faɗa wa Nnamdi Kanu 

IPOB ta soke umurnin zama a gida na duk Litinin a Kudu-maso-Gabas

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!