Taro kan tarihi da waƙoƙin Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan’anace
A jiya Asabar, 4 ga Afrilu, aka yi bikin buɗe taron ƙasa kan tarihin rayuwa da waƙoƙin Makaɗa Alhaji Muhammadu Bawa Ɗan'anace 'Yartsakkuwa Gandi Sakkwato wanda Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto, ta shirya a Zauren Taro na Dakta Zayyanu Abdullahi na jami'ar. Ga hotunan taron da muka samu daga Alhaji Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji), wanda shi ne Shugaban Kwamitin Shirya Taron.
Makaɗa Yahaya Ɗan’anace ‘Yartsakkuwa (mai ɗanyen hakin rawani) a lokacin da yake jagorantar ƙungiyar kiɗa ta gidan su a taron.Hajiya Luba Muhammadu Bawa Ɗan’anace ‘Yartsakkuwa Gandi Sakkwato, ‘ya ga Makaɗa Ɗan’anace a bakin aiki a lokacin bikin buɗe taronShugaban taron, Alhaji Abubakar Sadik Yelwa (Katukan Yauri), Manajan Darakta na N-HYPPADEC (a dama), tare da Alhaji Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji) a wajen bikin buɗe taron.Malam Buhari, ɗa ga ɗan dambe Malam Muhammad Umar Labbo da aka fi sani da suna Ango Ɗangiye ‘Yartsakkuwa wanda waƙar sa ce ta farko da Ɗan’anace ya fara rerawa a lokacin da ya fara shiga fagen waƙoƙin dambe. An ɗauki hoton a lokacin bikin buɗe taron.Wakilin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji (Dakta) Muhammad Sa’ad Abubakar III, wato Mai Martaba Sarkin Mafara, Talata Mafara Alhaji (Dakta) Bello Muhammad Barmo (a dama), tare da Ministan Ayyuka, Barista Bello Muhammad Goronyo, wanda shi ne babban baƙo na musamman a wajen bikin buɗe taron.Mataimakin Shugaban Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto, Farfesa Bashir Garba (Tafidan Minannata) (tsaye a tsakiya), yana gaisawa da babban baƙo mai jawabi (na farko daga gefen dama), Alhaji Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji), yayin da Daraktan Cibiyar Nazarin Hausa ta jami’ar, Farfesa Salisu Ahmad Yakasai (na farko daga hagu) yake tofa albarkacin bakin sa a wajen taron. A hagu, Farfesa Aliyah Adamu Ahmad ta Jami’ar Jihar Sokoto ce.Shugaban Ƙaramar Hukumar Talata Mafara, Jihar Zamfara, Alhaji Yahaya Yari Abubakar (Mabuɗin Mafara) (na farko daga dama) yake tattaunawa da Shugaban Kamfanin Ɗanfaƙo Media Services, Gusau, Malam Ɗahiru Sama’ila Mafara, a taron.Farfesa Ibrahim Garba Satatima (Talban Bunun Kano) yana gabatar da jagorar maƙala ta ɗaya a bikin buɗe taron.Farfesa Bashir Aliyu Sallau (Sarkin Askar Yariman Katsina Hakimin Safana, riƙe da makirfo), a lokacin da yake gabatar da jagorar maƙala ta biyu a taron.Mataimakin Shugaban Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto, Farfesa Bashir Garba (Tafidan Minannata), yake gabatar da jawabin sa a taron.Makaɗin dambe, Sarki Muhammadu Ɗanmoyi, yana baje kolin sa a taron.
Hotuna daga: Alhaji Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji