• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Hotuna

Cika shekaru 50: Hanya mafi ma’ana ta girmama tarihin Janar Murtala ita ce ci gaba da aiki domin gina ƙasa bisa aƙidun sa – Gwamnan Legas

* Taron tunawa da Janar Murtala shekaru 50 bayan rasuwa

Fatima Abdullahi by Fatima Abdullahi
February 6, 2026
in Hotuna
A A
0
Cika shekaru 50: Hanya mafi ma’ana ta girmama tarihin Janar Murtala ita ce ci gaba da aiki domin gina ƙasa bisa aƙidun sa – Gwamnan Legas

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa hanya mafi ma’ana ta girmama tarihin tsohon Shugaban Ƙasa Janar Murtala Ramat Muhammed ita ce ci gaba da aiki domin gina ƙasa da za ta rayu bisa aƙidun da ya ginu a kan su.

Sanwo-Olu ya faɗi haka ne a wajen taron tunawa da Janar Murtala shekaru 50 bayan rasuwar sa.

Shi dai Janar Murtala, an kashe shi ne a yunƙurin juyin mulkin da wasu sojoji ‘yan tawaye suka yi a ranar 13 ga Fabrairu, 1976.

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ɗauko gammon fulawa zai aje a wajen karrama Janar Murtala Ramat Muhammed a taron

A taron da aka yi yau a Legas, gwamnan ya ce: “Shekaru hamsin bayan rasuwar Janar Murtala Muhammed, misalin sa har yanzu yana da nauyi a zukatan mu wajen fahimtar nauyin da ke kan mu a matsayin ma’aikatan gwamnati.

“Ya jagoranci ƙasa da tsafta da tsayin daka. Ya buƙaci ladabi da bin ƙa’ida daga ma’aikatan gwamnati, kuma ya ɗauki muryar Nijeriya da ƙwarin gwiwa zuwa ƙasashen waje, musamman a batutuwan adalci da haɗin kan Afrika.

Gwamna Sanwo-Olu da iyalan Janar Murtala a taron

“Rayuwar sa tana ci gaba da zama tunatarwa cewa shugabanci ba wai tsawon lokacin zama a ofis ba ne, amma game da ƙudiri da jarumtakar ɗaukar mataki idan an kira mutum.

“A yau, a wannan gagarumin bikin cika shekaru, ina tunawa da ma’aunin da ya kafa. Dole ne gwamnati ta kasance mai ƙa’ida, mai mayar da hankali kan manufa, kuma haɗaɗɗiya wajen cimma buri guda.

“Hanya mafi ma’ana ta girmama tarihin sa ita ce ci gaba da aiki domin gina ƙasa da za ta rayu bisa waɗannan ƙimomi.”

Gwamna Babajide Sanwo-Olu yana jawabi a taron
Gwamna Sanwo-Olu tare da iyalin Murtala
Sojoji a taron
Tags: BabajideSanwo-OluJanarMurtalaRamatMuhammedLegasshekaru50tunawa
Previous Post

Limamin Abuja ya yi Allah-sambarka da mulkin Tinubu yayin da Matawalle ya aurar da ‘ya’ya goma

Next Post

Ɗan Lamiɗo a garin Lamiɗo

Related Posts

Taro kan tarihi da waƙoƙin Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan’anace
Hotuna

Taro kan tarihi da waƙoƙin Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan’anace

April 5, 2026
Hotuna: Minista Idris a Babban Taron APC
Hotuna

Hotuna: Minista Idris a Babban Taron APC

March 27, 2026
Hotuna: Babban taron APC na 2026
Hotuna

Hotuna: Babban taron APC na 2026

March 27, 2026
Tawagar Google ta ziyarci Minista Idris a ofis
Hotuna

Tawagar Google ta ziyarci Minista Idris a ofis

February 25, 2026
Ɗan Lamiɗo a garin Lamiɗo
Hotuna

Ɗan Lamiɗo a garin Lamiɗo

February 6, 2026
Hotuna: Ziyarar shugabannin kamfanin MTN zuwa hedikwatar CBN ta yi armashi
Hotuna

Hotuna: Ziyarar shugabannin kamfanin MTN zuwa hedikwatar CBN ta yi armashi

January 30, 2026
Next Post
Ɗan Lamiɗo a garin Lamiɗo

Ɗan Lamiɗo a garin Lamiɗo

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!