‘Yan sanda a Abuja sun tsunduma cikin bincike kan kisan gillar da aka yi wa wata mai gabatar da labarai a gidan talbijin na Arise TV, wato Somtochukwu Christelle Maduagwu, wadda aka kashe a gidan ta da ke unguwar Katampe, Abuja, a lokacin fashi da makami a farkon safiyar wannan rana ta Litinin, 29 ga Satumba.
Gidan talbijin na Arise sun bada sanarwar kisan a cikin wata sanarwa da Hadiza Usman-Ajayi ta rarraba wa hannu a madadin shugabannin kamfanin.
Ta ce: “Sommie ba kurum ɗaya daga cikin ma’aikatan Arise News kaɗai ba ce, amma kuma zazzaƙar murya ce wadda masu kallon mu suke matuƙar so.”
Maduagwu, wadda abokan aikin ta suke yi wa laƙabi da “Sommie”, ‘yar shekara 29 ce.
Ban da aikin jaridar da take yi, ƙwararriyar lauya ce har ila yau.
An ce takan yawan taimaka wa abokan aiki a lokacin aiki da bayan aiki.







