• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Haƙurin addini shi ne jigon zaman lafiya da haɗin kan Nijeriya – Tinubu

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
January 26, 2026
in Labarai
A A
0
Tsaro: Tinubu ya kira taron Majalisar Ƙoli ta ƙasa da ta ‘yan sanda
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su rungumi haɗin kai, haƙurin addini, da zaman lafiya, yana mai bayyana su a matsayin muhimman ginshiƙan tsaron ƙasa da ci gaba mai ɗorewa.

Shugaban Ƙasar ya yi kiran ne a ranar Litinin a yayin taron ƙasa da ƙasa karo na huɗu na Cibiyar Wayewar Musulunci da Tattaunawar Addinai da aka gudanar a Jami’ar Bayero da ke Kano.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya wakilci Shugaban Ƙasa a wurin taron.

Shugaban Ƙasa Tinubu ya jinjina wa Cibiyar Wayewar Musulunci da Tattaunawar Addinai, da kuma Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, bisa ci gaba da shirya tarukan tattaunawa tsakanin addinai, waɗanda ke bunƙasa zaman lafiya da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.”

Ya ce, “Wannan taro na ci gaba da ɗaukaka manufofin zaman lafiya da haɗin kan ƙasar mu ta hanyar tattaunawa. Ina alfahari da wannan gayyata.”

Ya bayyana yadda taron ya mayar da hankali kan gadon marigayi Sheikh Mahmud Abubakar Gumi a matsayin abin da ya dace da lokaci kuma mai ilmantarwa, yana mai cewa fitaccen malamin addinin ya taka rawar gani sosai wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa a lokuta masu muhimmanci a tarihin Nijeriya.

“Sheikh Gummi ya fahimci inda addini da siyasa ke haɗuwa, kuma ya yi aiki kafaɗa da kafaɗa da mahukunta bayan samun ’yancin kai da kuma bayan yaƙin basasa domin inganta haɗin kai da zaman lafiya,” inji shi.

Tinubu ya bayyana Sheikh Gummi a matsayin fitaccen malami, mai kawo gyara, kuma jigo na ƙasa wanda tasirin sa ya wuce fagen addini kaɗai.

“Malami ne, mai gyara, mai ba da shawara, kuma marubuci ne mai hazaƙa. Ya koyar da tsararraki da dama su yi imani da rashin rarrabuwar Nijeriya, a fannin aiki da kuma a ibada,” inji Shugaban Ƙasar.

Dangane da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a yanzu, Shugaba Tinubu ya buƙaci ’yan Nijeriya da su yi watsi da labaran da ke nuna ƙasar a matsayin wadda ba ta mutunta ’yancin addini.

“Dole ne mu ƙarfafa ƙudirin mu na gina ƙasa mai haɗin kai. Dole ne mu tunkari yunƙurin kwanan nan na ɓata sunan Nijeriya a matsayin ƙasar da ke tauye ’yancin addini,” inji shi.

Shugaban Ƙasar ya jaddada cewa tsaron ƙasa yana da alaƙa kai tsaye da haɗin kai da mutunta juna a tsakanin ’yan ƙasa.

“Tsaron ƙasar mu yana da alaƙa da haɗin kanmu, zaman tare, da mutunta bambancin addini. Dole ne mu haɗa kai mu fuskanci duk waɗanda ke neman raba kan mu,” inji shi.

Ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin sa na kare rayuka da dukiyoyi tare da yaƙar laifuka a faɗin ƙasar.

“Gwamnati na na aiki tuƙuru wajen kare rayuka da dukiyoyi da kuma yaƙi da ta’addanci ta dukkan hanyoyin da muke da su,” inji Tinubu.

Ya bayyana cewa an tura sama da jami’an tsaron daji fiye da 7,000 waɗanda aka horar a faɗin ƙasar domin hana masu laifi amfani da hanyoyin dazuzzuka, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kafa rundunar ’yan sandan jihohi domin tabbatar da tsaro a matakin al’umma, bisa tanadin kundin tsarin mulki.

Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa bayan ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro a watan Nuwamba 2025, an faɗaɗa kuma an ƙarfafa ayyukan tsaro a jihohin da ke fama da ’yan fashi da ta’addanci.

“Mun inganta ayyukan tsaro ta hanyar amfani da bayanan sirri domin tarwatsa cibiyoyin ’yan ta’adda da masu laifi,” inji shi.

Shugaban Ƙasa Tinubu ya kuma bayyana haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka, yana mai jaddada cewa haɗin gwiwar na mayar da hankali ne kan yaƙi da ta’addanci da kare fararen hula tare da mutunta ikon Nijeriya.

Ya kammala da kiran ’yan Nijeriya da su ɗaukaka kyawawan ɗabi’un su da zaman lafiya, yana mai bayyana haɗin kai a matsayin ginshiƙin dauwamammen zaman lafiya.

Manyan malamai da shugabannin addinin Musulunci da suka halarci taron sun haɗa da Shugaban Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa’Ikamatul Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau; Babban Limamin Jihar Kano, Farfesa Shehu Ahmad Galadanci; Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero, Kano, Farfesa Haruna Musa; Sheikh Ahmad Mahmud Gummi; da Janar Abdulkadir Mahmud Gummi (mai ritaya), da sauran su.

Tags: addiniShugabaBolaTinubutaro
Previous Post

Yadda shirin CBN na ƙarfafa jarin bankuna zai fara samar da gagarumin tattalin arziki tun daga 2026

Next Post

Mun ji daɗin sabon gyaran harajin gwamnatin Tinubu yayin da albashin su na Janairu ya ƙaru 

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya
Labarai

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya

May 4, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja
Labarai

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
Mun ji daɗin sabon gyaran harajin gwamnatin Tinubu yayin da albashin su na Janairu ya ƙaru 

Mun ji daɗin sabon gyaran harajin gwamnatin Tinubu yayin da albashin su na Janairu ya ƙaru 

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!