• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Mun ji daɗin sabon gyaran harajin gwamnatin Tinubu yayin da albashin su na Janairu ya ƙaru 

New Citizen Hausa by New Citizen Hausa
January 26, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Mun ji daɗin sabon gyaran harajin gwamnatin Tinubu yayin da albashin su na Janairu ya ƙaru 

 

Ma’aikata a sassa daban-daban na gwamnati da masu zaman kan su a faɗin Nijeriya sun bayyana farin ciki da kwarin gwiwa biyo bayan raguwar kuɗin harajin da ake cirewa daga albashin watan Janairu na shekarar 2026, bayan fara aiki da sabon gyaran haraji da Gwamnatin Tarayya ta aiwatar a farkon shekarar nan.

Wasu daga cikin ma’aikatan da suka wallafa ra’ayoyin su a kafafen sada zumunta sun tabbatar da cewa sabon tsarin harajin ya ƙara musu abin da suke samu na albashi, musamman ga masu ƙarami da matsakaicin albashi.

Mahmud Galadanci, ma’aikacin banki, ya ce sauyin ya bayyana a cikin takardar albashinsa na watan Janairu.

“Tabbas sabon dokar haraji ya fi tsohon. Albashina ya ƙaru da N3,500 sakamakon rage haraji. Na gode, Mallam Tinubu,” inji shi.

Shi ma Yarima Sulaiman ya bayyana sabon tsarin a matsayin babban sauƙi idan aka kwatanta da tsohon tsarin da ya ce yana da nauyi matuƙa.

“Ya fi sauƙi sosai fiye da baya. Muna fatan za a ci gaba da haka. A da ina biyan haraji kusan kashi 19.2, wanda ya kai sama da N300,000, amma yanzu ina biyan kusan N200,000,” in ji shi.

Haka nan, Hussain Spikin ya ce shi ma albashin sa ya ƙaru ƙarƙashin sabon tsarin.

“Na samu ƙarin N7,800,” inji shi.

Da yake bayani a matsayinsa na ƙwararre, Ado Mohammed Abubakar, PhD, wand ƙwararren akanta ne mai lasisi kuma masanin haraji mai lasisi daga Kano, ya ce an tsara gyaran harajin ne domin samar da adalci da rage nauyin da ke kan ma’aikata masu rauni.

“Masu ƙarancin albashi sun samu ragi, masu albashi mai tsoka kuma sun ga ƙari idan aka kwatanta da abin da suke biya a baya,” inji shi, yana mai ƙara bayyana cewa hakan na nufin an rage wa masu ƙaramin albashi haraji sosai, yayin da aka daidaita tsarin biyan haraji ga masu albashi mai yawa.

Tun da farko, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa gyaran harajin na da nufin inganta walwalar ma’aikata, ƙara bin doka wajen biyan haraji, da kuma farfaɗo da tattalin arziki ta hanyar ƙara kuɗin da jama’a ke da shi a hannu.

Yayin da ma’aikata ke fara jin tasirin gyaran, da dama sun yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da dorewar wannan tsari tare da aiwatar da shi yadda ya kamata a dukkan sassa, suna masu fatan hakan zai haifar da daidaiton tattalin arziki da ingantacciyar rayuwa ga al’umma baki ɗaya.

Previous Post

Haƙurin addini shi ne jigon zaman lafiya da haɗin kan Nijeriya – Tinubu

Next Post

CBN ya ɗaga darajar Opay, Moniepoint da su Palmpay zuwa cikakkun bankunan ƙasa baki ɗaya

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
CBN ya ɗaga darajar Opay, Moniepoint da su Palmpay zuwa cikakkun bankunan ƙasa baki ɗaya

CBN ya ɗaga darajar Opay, Moniepoint da su Palmpay zuwa cikakkun bankunan ƙasa baki ɗaya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!