Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Jihar Katsina, a yau Laraba, ya rattaba hannu kan ƙudirin kasafin kuɗin jihar na 2026 mai darajar N897.8 biliyan, yana mai mai da shi doka.
An rattaba hannun ƙudirin ne a Fadar Gwamnatin Katsina, kuma an sanya masa taken ‘Gina Makomar Ku 3’.
Gwamnan ya yaba wa Majalisar Dokokin jihar bisa amincewa da kasafin cikin kwanaki 21 kacal na aiki.
Raɗɗa ya ce kasafin kuɗin, wanda ya ƙunshi kashi 18 cikin ɗari na kuɗin gudanarwa da kashi 81 cikin ɗari na kuɗin raya ƙasa, yana daga cikin gadon marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua.
Ya ce sabon kasafin, wanda ya rage yawan kuɗin gudanarwa, ya yi daidai da tsarin marigayi shugaban, wanda shi ma tsohon gwamnan jihar ne.
Gwamnan ya gode wa ’yan majalisar bisa sadaukar da lokacin su, har da barin hutu da yin daren rashin barci domin tabbatar da an wuce da kasafin, tare da yawan ƙudirorin da suka yi aiki a kan su a ’yan shekarun nan.
Raɗɗa ya jaddada muhimmancin kyakkyawar alaƙa tsakanin ɓangaren zartarwa da Majalisar Dokoki, tare da kira da a ci gaba da yin aiki tare.
Tun da farko, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Nasir Yahya Daura, ya ce kasafin ya fito ne daga tsari mai zurfi da cikakken nazari, wanda ya haɗa da bincike da tambayoyi domin tabbatar da biyan buƙatun jama’a da cigaban jihar.
Ya tuna da cewa kasafin da ɓangaren zartarwa ya gabatar shi ne iri ɗaya da wanda aka amince da shi, wanda hakan ya sa majalisar ta yanke shawarar barin adadin kasafin yadda aka gabatar.
“Bayan nazari mai zurfi, majalisar ta gamsu cewa ƙudirin ya dace kuma yana tafiya da tsarin cigaban wannan gwamnati,” inji shi.
Kakakin ya roƙi taimakon Ubangiji wajen aiwatar da kasafin cikin nasara da kuma shawo kan matsalolin tsaro. (NAN)







