• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN zai haramta wa ‘yan gidoga masu rubuta cek na bogi yin hulɗa da banki tsawon shekara biyar

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
November 26, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN zai haramta wa ‘yan gidoga masu rubuta cek na bogi yin hulɗa da banki tsawon shekara biyar
Cakin banki

Cakin banki

Babban Bankin Nijeriya (CBN) zai fito shirin ƙaƙaba wa masu rubuta cek da sunan biyan kuɗi ga wani, alhali ba su da isassun kuɗi a asusun bankin su hukuncin daina hulɗa da su a bankuna har tsawon shekaru biyar. takunkumin haramta cinikayya na shekaru 5 ga masu rubuta takardun bashi (cek) na bogi

Ana wannan shirye-shiryen fara aiki da doka da ƙa’idojin kan masu rubuta cek na bogi, wanda a Turance ake kira ‘dud check’, a matsayin babban laifi a tsarin hada-hadar kuɗaɗe a bankuna.

CBN dai na shirin kafa wannan sabuwar doka da za ta hana masu maimaita rubuta cek na gidoga ci gaba da yin mu’amalar banki na tsawon shekara biyar.

A ƙarƙashin wannan ƙudirin doka, za a bayyana mutum a matsayin “mai rubuta cekin kuɗi na bogi sau da yawa”, idan ya rubuta takardun bashi sau uku kuma aka ƙi biyan su, saboda rashin isasshen kuɗi a asusun bankin sa.

CBN ta bayyana wannan a cikin daftarin ƙa’idojin da ta fitar cikin wannan mako, dangane da “Shirin Magance Rubuta Cek Na Bogi”, wanda ke bai wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi ikon sanya sunayen irin waɗannan mutane a jerin waɗanda banki ya yi nuni cewa ba a ba su amana.

Daga cikin abin da dokar za ta tanadar, an rattaba cewa waɗanda suka karya doka za a hana su karɓar lamuni, sannan a hana su samun lamuni daga kowanne banki.

Kuma za a hana su buɗe asusun ‘current account’ na tsawon shekaru biyar.

Bankuna kuma za su ƙwace ragowar littafin cekin kuɗaɗen da ke hannun sa da bai a amfani da su ba. Sannan a shigar da sunan sa da bayanan sa, a matsayin mai laifin da gangaci ne ci gaba da yin hulɗar banki da shi, wato ‘Credit Risk Management System’ (CRMS).

An tanadi takunkumi ga masu maimaita laifin, ta hanyar tsananta hukunci ga masu sake aikata laifi, inda aka tanadi cewa duk wani abokin ciniki da ya sake rubuta takardar bashi ta bogi, wato cek, bayan kammala hukuncin shekara biyar zai sake fuskantar kara wasu shekara biyar a duk lokacin da ya maimaita laifin.

Amma za a cire sunan sa daga wannan takunkumi idan lokacin hukuncin ya ƙare, ko kuma banki ya tabbatar an yi kuskuren shigar da sunan mutum.

Dole ne bankuna su sabunta bayanan mutum a cibiyoyin bayanan masu rubuta cek na gidoga, tare da sanar da shi a rubuce bayan ya ƙare wa’adin hukuncin.

Ƙudirin ya kuma tanadi hukunci kan bankunan da suka gaza aiwatar da ƙa’idojin, inda za su fuskanci tarar

Naira biliyan 5 idan ba su aiwatar da takunkumin ba.

Sai tarar Naira miliyan 3 idan suka buɗe ‘current account’, ba tare da binciken CRMS ba.

Tags: Babban Bankin Nijeriyabankunacakin bankiCBNcek
Previous Post

CBN ya bar adadin kashi 27% matsayin kuɗin ruwa ga masu ka karɓar rance a bankuna

Next Post

Gwamna Raɗɗa ya rattaba hannu kan ƙudirin kasafin kuɗi na 2026 na N897.8 biliyan

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Gwamna Raɗɗa ya rattaba hannu kan ƙudirin kasafin kuɗi na 2026 na N897.8 biliyan

Gwamna Raɗɗa ya rattaba hannu kan ƙudirin kasafin kuɗi na 2026 na N897.8 biliyan

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!