Hukumar Zaɓe ta Ƙasa Mai Zaman Kan ta (INEC) ta yi tsokaci kan damuwar jama’a da ta taso bayan fitar da Jadawalin Lokuta da Tsarin Ayyuka na Babban Zaɓen 2027, musamman dangane da ranakun da aka ƙayyade domin gudanar da zaɓukan.
A cikin wata sanarwa da Mohammed Kudu Haruna, Kwamishinan Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe, ya sanya wa hannu, hukumar ta tunatar da jama’a cewa ta tsara jadawalin ne bisa cikakken bin ƙa’idojin lokutan da ke cikin Tsarin Mulkin Nijeriya, da Dokar Zaɓe, da kuma Dokoki da Ƙa’idojin INEC na Gudanar da Zaɓe na 2022.
Ya ce Dokoki da Ka’idojin INEC na Gudanar da Zaɓe, da aka zartar tun a 2019, sun ƙayyade ranakun da za a riƙa gudanar da zaɓe.
Sashi na 2 na dokar ya tanadi cewa: “Zaɓen Shugaban Ƙasa da Mataimakin sa, da kuma na Majalisar Dokoki ta Ƙasa, za a gudanar da su ne a ranar Asabar ta uku a watan Fabrairu na duk shekarar da za a yi Babban Zaɓe; yayin da zaɓen Gwamna da Mataimakin sa da na Majalisun Dokokin Jihohi za a gudanar da su makonni biyu (2) bayan haka.”
Dangane da haka, kuma bisa cikakken bin waɗannan dokoki da ƙa’idoji da ke aiki, hukumar ta sanya ranar Asabar, 20 ga Fabrairu, 2027 domin Zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa, sannan Asabar, 6 ga Maris, 2027 domin Zaɓen Gwamnoni da na Majalisun Dokokin Jihohi.
Ya ce: “Duk da haka, hukumar ta lura da damuwar da masu ruwa da tsaki suka bayyana dangane da daidaituwar ranakun da aka tsara da wasu bukukuwa da lokutan ibada da ƙasa ta amince da su.
“Hukumar na son ta tabbatar wa jama’a cewa tana kulawa da duk wata halastacciyar damuwa da ka iya shafar fitowar jama’a kaɗa ƙuri’a da kuma yadda za a gudanar da zaɓe gaba ɗaya.”
Ya ƙara da cewa, “Dangane da waɗannan buƙatu da aka gabatar, hukumar na ci gaba da tattaunawa, kuma idan ya zama dole, za ta nemi matakin gyara ta fuskar doka domin magance damuwar da ta taso, tare da tabbatar da cewa duk wani sauyi ya yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulki da dokoki.”
INEC ta sake jaddada ƙudirin ta na tabbatar da gaskiya, haɗin kai da kuma gudanar da Babban Zaɓen 2027 cikin sahihanci.
Ya ce za a sanar da jama’a duk wani sabon cigaba da zarar an samu.







