Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umurci mataimakin sa, wato Kashim Shettima, da ya jagoranci wata babbar tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Kano domin jajanta wa ‘yan Kasuwar Singa da gobara ta shafa tare da isar da ta’aziyya da goyon bayan gwamnati.
Sabuwar mummunar gobarar da ta tashi a jiya a kasuwar wadda tana ɗaya daga cikin manyan kasuwannin abinci a Najeriya, ta lalata kayayyaki da darajar su ta kai biliyoyin naira.
Gobarar, wadda ta tashi da yammacin Asabar, ta ci gaba har zuwa safiyar yau Lahadi.
Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici kuma mai tayar da hankali, yana mai cewa ya damu matuƙa da yadda irin wannan masifa ke maimaituwa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.
A cikin wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya rattaba wa hannu, Shugaban ya miƙa saƙon ta’aziyya ga ‘yan kasuwa da masu sana’o’in da suka yi asara sakamakon gobarar.
A matsayin wani ɓangare na matakan gaggawa daga Gwamnatin Tarayya, Shettima zai jagoranci tawagar da za ta tashi daga Abuja zuwa Kano domin isar da saƙon jaje daga Shugaba Tinubu da kuma sanar da matakan tallafin Gwamnatin Tarayya.
Tawagar ta ƙunshi:
- Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin
- Sanata Kawu Sumaila
- Shugaban Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA)
- Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi
- Ministan Harkokin Jinƙai, Bernard M. Doro
- Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Zubaida Umar
A yayin ziyarar, ana sa ran tawagar za ta yi alƙawarin tallafin kuɗi a madadin Gwamnatin Tarayya domin taimaka wa ‘yan kasuwa su farfaɗo da harkokin su.
Haka kuma za su tattauna da Gwamnatin Jihar Kano don hanzarta buɗe kasuwar da dawo da harkokin tattalin arziki.
Tinubu ya kuma umurci a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin gobarar, kusa da na nesa, domin hana sake faruwar irin haka a nan gaba.
Ita ma Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta bayyana alhinin ta ga waɗanda gobarar Kasuwar Singa ta shafa, tana mai kiran lamarin abin takaici da tayar da hankali.
A cikin wata sanarwa da Shugaban ta kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta nuna cewa gobarar ta faru ne ‘yan makonni kaɗan bayan wata makamanciyar haka, lamarin da ya ƙara jefa ‘yan kasuwa cikin damuwa da ƙunci na tattalin arziki.
Gwamnan ya ce yawaitar gobarar kasuwanni a Arewa na ci gaba da lalata hanyoyin samun abinci da kuɗin shiga, tare da kawo cikas ga harkokin tattalin arziki da jefa iyalai cikin mawuyacin hali.
Ya jaddada buƙatar ɗaukar matakan kariya na zamani da suka haɗa da fasaha daga hukumomin tarayya da na jihohi.
Ƙungiyar ta ba da shawarar girka na’urorin gano gobara da kashe ta na zamani a manyan kasuwanni, inganta tsare-tsaren gine-gine, tsaurara bin dokokin tsaro, da kuma ci gaba da wayar da kan jama’a, musamman ‘yan kasuwa da masu gudanar da kasuwanni.
Haka kuma ta yaba da saurin kai ɗauki da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, jami’an tsaro, NEMA da sauran masu bayar da agajin gaggawa suka yi, wanda ya taimaka wajen taƙaita yaɗuwar gobarar da hana ƙarin asara.







