• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Bashin Da Ake Bin Najeriya Abin Tsoro Ne – Kakakin Majalisa

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
September 8, 2025
in Labarai
A A
0
Bashin Da Ake Bin Najeriya Abin Tsoro Ne – Kakakin Majalisa
Tajuddeen Abbas

Tajuddeen Abbas

Kakakin Majalisar Tarayya, Tajuddeen Abbas, ya bayyana fargaba dangane da ɗimbin bashin da ake bin Nijeriya, yana mai gargaɗi cewa yawan bashin ya zarce adadin dokar ƙasa ta gindaya ciwowa fintinkau.

Ya ce a yanzu haka yawan bashin da yawan kuɗaɗen ruwan da ake biya na yin barazana ga kuɗaɗen shiga da waɗanda gwamnati ke kashewa wajen gudanar da ayyukan yau da kullum na wajibi, har ma ga ɗorewar tattalin arziki.

Da yake jawabi a yau Litinin yayin buɗe taron shekara-shekara na 11, na Majalisar Kwamiti-kwamitin Masu Sa-ido Kan Harkokin Kuɗaɗe na Majalisun Ƙasashen Afrika ta Yamma (WAAPAC) a Majalisar Ƙasa, a Abuja, Abbas ya ce bashin da ake bin Nijeriya “ya kai maƙurar barazana.'”

Ya yi kira a gaggauta kawo sauye-sauye wajen gyara tsari da ƙa’udojin ciwo basussuka, sannan kuma majalisa ta riƙa sa-ido kan ayyukan da gwamnati ke aiwatarwa.

Ya ce: “Zuwa ƙarshen watanni uku na farkon 2025, adadin bashin da ake bin Nijeriya ya kai Naira tiriliyan 149.39, kwatankwacin kusan Dala biliyan 97. Hakan kuwa ya nuna cewa adadin ya ƙaru daga Naira tiriliyan 121.7 da ake bin Nijeriya a 2024”.

Ya ƙara da cewa, “Wani ƙarin abin damuwa shi ne idan aka ɗora adadin bashin bisa sikelin ƙarfin tattalin arziki na cikin gida, za a ga ya haura ƙa’idar adadin da doka ta ce a ciwo bashi ya kai kusan kashi 52 bisa 100.

“Domin dokar mu cewa ta yi kada fa bashin da aka ciwo ya haura kashi 40 bisa 100 na ƙarfin tattalin arzikin cikin gida, wanda dokar mu ta ce kada ya wuce haka.”

Ya ce saboda haka wannan abin damuwa ne matuƙar gaske. Sai ya yi kira a samar da sababbin ƙa’idoji kuma a riƙa sa-ido.

“Ya kamata kuɗaɗen da ake ciwowa bashi a riƙa ganin alfanun su ƙuru-ƙuru a fannin ayyukan raya ƙasa, kiwon lafiya, inganta ilmi da kuma masana’antu domin a samu ayyuka, sannan a rage fatara, talauci da raɗaɗin tsadar rayuwa.

“Amma yawan ciwo basussukan da ba su haifar da komai sai cin hanci da rashawa, dole ne fa a riƙa fallasa su, kuma ana bijire wa amincewa a ciwo shi,” inji shi.

Tags: bashiTajuddeen Abbas
Previous Post

Gwamnatin Tinubu Ta Tallafa Wa Sama Da Gidajen Talakawa 226,000 A Nasarawa

Next Post

Ƙwangen kuɗaɗen shiga: Majalisar Tarayya Ta Ƙwato Wa Nijeriya Naira Bilyan 200 – Hon Salam

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
Ƙwangen kuɗaɗen shiga: Majalisar Tarayya Ta Ƙwato Wa Nijeriya Naira Bilyan 200 – Hon Salam

Ƙwangen kuɗaɗen shiga: Majalisar Tarayya Ta Ƙwato Wa Nijeriya Naira Bilyan 200 - Hon Salam

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!