• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Nishaɗi Da Al'adu

Yadda Mama Nike ta tsaya da ƙafar ta bayan kuɓuta daga gallazawar miji

New Citizen Hausa by New Citizen Hausa
May 30, 2026
in Nishaɗi Da Al'adu
A A
0
Yadda Mama Nike ta tsaya da ƙafar ta bayan kuɓuta daga gallazawar miji
Mama Nike tare da matan da ta koya wa saƙar zanin adire (Hoto daga: Tommy Dixon / BBC)

Mama Nike tare da matan da ta koya wa saƙar zanin adire (Hoto daga: Tommy Dixon / BBC)

Mama Nike tana ɗaya daga cikin mata 15 da wani mutum ya aura. Lokacin da ta bar mijin ta domin ta mayar da hankali kan fasahar zane, sai sauran matan 14 su ma suka zaɓi su bi ta…

Fitacciyar mai fasaha Nike Davies Okundaye – wadda aka fi sani da Mama Nike – ta taso ne a wani yanki na Nijeriya inda auren mata da yawa ya zama ruwan dare. Mahaifin ta ma yana da mata uku.
Matan gidan su sun shahara wajen ƙera adire, wato wani nau’in zane da rini na gargajiya. Tun tana ‘yar shekara shida, kakar kakar ta, da mahaifiyar ta da gwaggon ta suka koya mata yadda ake kaɗa zare, saƙa da kuma yin rini.

“Ban san cewa wannan ne zai zama abin da zan ci gaba da rayuwa da shi ba,” inji Mama Nike, domin duk da wannan sana’a ta iyali, talauci ya yi ƙamari a gidan su.
Lokacin da ta kai shekara 13, sai mahaifin ta ya yanke shawarar aurar da ita ga wani mutum wanda tuni yake da wasu matan da dama.

Sai dai kakar kakar ta tana son ta zaɓi mijin ta da kan ta, kuma Mama Nike ma haka take so. Ta tsere daga mutanen da suka zo ɗaukar ta zuwa gidan miji, sannan ta yi tafiyar kwanaki biyar a ƙafa har ta koma ƙauyen su.

“Wannan shi ne babban haɗarin da na taɓa ɗauka a rayuwa ta,” inji ta. “Ban damu ko zan mutu ba.”

Ta isa gida cikin gajiya ƙwarai kuma jikin ta cike da cizon ƙudan zuma. Duk da haka, mahaifin ta ya sake ƙoƙarin aurar da ita.
A wannan karon, Mama Nike ta sake guduwa ta shiga wata ƙungiyar wasan kwaikwayo mai yawo daga gari zuwa gari. Daga baya ‘yan sanda suka kama ta suka mayar da ita gida.

Daga bisani, ta amince ta auri wani shahararren mai fasaha kuma mawaƙi daga Oshogbo, wani gari da ya yi suna wajen harkokin fasaha.

Ta yi amfani da ƙwarewar ta ta ɗinki da ado da zare wajen ƙera kayan sawa ga ƙungiyar kiɗan mijin ta, yayin da ita kuma take ƙoƙarin gudanar da nata ayyukan fasaha.

“Maza ba sa son mace ta zama mai fasaha. Saboda haka, sai da dare nake yin aiki na, da rana kuma nake yi musu aiki,” inji ta.

Daga baya mijin ta ya auri wasu mata 14, wanda ya sa adadin matan sa ya kai 15.
Al’ada ta buƙaci matan da aka aura tun farko su amince da kowace sabuwar matar da aka kawo, amma Mama Nike ta ce ba ko yaushe suke son hakan ba.

Akwai lokacin da mijin ya kai matan sa wani coci inda aka hana su abinci, ruwa da kuma ganin ‘ya’yan su. Mama Nike ta ce an tilasta musu amincewa da auren wata sabuwar mata. Ta ce: “A rana ta uku muka ce, ‘Ku kawo matar mana, ba ma jin kishin ta kuma.’ Bakunan mu sun bushe tamkar katako saboda ƙishirwa.”

Ta ce zaman da take yi tare da mijin ta ya sa ta ji “kamar zaki marar haƙora. Ba ka da wani iko.”

Daga baya ta fara koya wa matan mijin ta sana’ar adire ta gargajiya, kuma ba da jimawa ba kowacce daga cikin su ta iya samun kuɗin kan ta.

Da ta gaji da gallazawa da cin zarafin da mijin su yake masu, sai Mama Nike ta bar shi da zarar ta tara isassun kuɗaɗen sayen nata gidan. Sauran matan kuwa suka zaɓi su bi ta.

A shekarar 1986 ta buɗe gidan baje-kolin fasaha na farko a Oshogbo.

Yanzu ta zama fitacciyar mai fasaha da ta yi suna a duniya baki ɗaya. Tana da babban gidan baje-kolin fasaha a Legas, inda take koyar da wasu tare da ƙirƙirar kyawawan ayyukan fasaha masu launuka iri-iri.

Daga: BBC World Service

Kalli shirin 🎧 Outlook: https://bbc.in/4v9xBcM⁠�

Tags: adireMama NikeOshogbo
Previous Post

Karo na farko tun 1999: Gwamna Uba Sani ya ziyarci alhazan Kaduna, ya ba kowannen su riyal 300

Next Post

 ‘Yan bindiga sun sace tsohon kakakin rundunar tsaro Janar Rabe tare da matar sa a hanyar Katsina

Related Posts

Nishaɗi Da Al'adu

Naɗin Sarautar Ɗanmasani A Ƙasar Hausa Da Ayyukan Sa

November 2, 2026
Sabon Ɗanmasanin Sakkwato, Farfesa Mansur, ya naɗa sarautun musamman
Nishaɗi Da Al'adu

Sabon Ɗanmasanin Sakkwato, Farfesa Mansur, ya naɗa sarautun musamman

November 1, 2026
Hausa da Hausawa a Ghana
Nishaɗi Da Al'adu

Hausa da Hausawa a Ghana

May 23, 2026
Cewar Shugaba Tinubu: Bikin Argungu shaida ce ta dawowar zaman lafiya, na yi alƙawarin goyon baya ga noma da yawon buɗe ido
Nishaɗi Da Al'adu

Cewar Shugaba Tinubu: Bikin Argungu shaida ce ta dawowar zaman lafiya, na yi alƙawarin goyon baya ga noma da yawon buɗe ido

February 14, 2026
Sarkin Adabi: Mafi Girman Sarautar Fasaha
Mahanga

Sarkin Adabi: Mafi Girman Sarautar Fasaha

February 13, 2026
Bikin Argungu alama ce ta haɗin kan ƙasa da samun karɓuwa a idon duniya – Gwamnatin Tarayya
Nishaɗi Da Al'adu

Bikin Argungu alama ce ta haɗin kan ƙasa da samun karɓuwa a idon duniya – Gwamnatin Tarayya

January 21, 2026
Next Post
 ‘Yan bindiga sun sace tsohon kakakin rundunar tsaro Janar Rabe tare da matar sa a hanyar Katsina

 'Yan bindiga sun sace tsohon kakakin rundunar tsaro Janar Rabe tare da matar sa a hanyar Katsina

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!