• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

 ‘Yan bindiga sun sace tsohon kakakin rundunar tsaro Janar Rabe tare da matar sa a hanyar Katsina

New Citizen Hausa by New Citizen Hausa
May 30, 2026
in Tsaro
A A
0
 ‘Yan bindiga sun sace tsohon kakakin rundunar tsaro Janar Rabe tare da matar sa a hanyar Katsina
Janar Rabe Abubakar (ritaya) da motar sa da aka bari bakin hanya bayan an sace shi

Janar Rabe Abubakar (ritaya) da motar sa da aka bari bakin hanya bayan an sace shi

Wasu ‘yan bindiga sun sace tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro (DDI), Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), tare da matar sa a Jihar Katsina.

Tsohon babban jami’in sojan da matar sa tare da direban su suna cikin tafiya ne a hanyar Matazu zuwa Katsina a safiyar Asabar lokacin da ‘yan bindigar ɗauke da makamai suka yi musu kwanton ɓauna.

Wata majiya ta tsaro da ke da masaniya kan lamarin ta bayyana cewa maharan sun tare motar ƙirar Fijo 505 tare da yin awon gaba da miji da matar zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Direban ya samu nasarar tserewa duk da cewa ya samu raunin harbin bindiga yayin harin, kuma a halin yanzu yana samun kulawar likitoci.

Majiyar ta ƙara da cewa an sanar da hukumomin tsaro da abin ya shafa, kuma ana ci gaba da haɗa kai domin ceto waɗanda aka sace ɗin cikin ƙoshin lafiya.

“Jami’an tsaro sun riga sun fara aikin bincike da ceto, yayin da aka tura jami’an tattara bayanan sirri domin gano inda masu garkuwa da mutanen suke tare da tabbatar da dawo da waɗanda aka sace cikin aminci.”

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ana ci gaba da ƙoƙarin samun tabbaci a hukumance daga rundunar soji da sauran hukumomin tsaro kan lamarin.

Wannan satar ta ƙara jefa damuwa game da ci gaba da matsalar rashin tsaro a wasu sassan Jihar Katsina, duk da cigaba da gudanar da hare-haren soji kan ƙungiyoyin masu aikata laifuka a yankin Arewa-maso-yamma.

Lamarin ya kuma tunatar da jama’a irin hare-haren da aka taɓa kai wa jami’an soji da sauran jami’an tsaro a jihar.

A cikin shekarun baya-bayan nan, wasu jami’an tsaro masu aiki da waɗanda suka yi ritaya sun kasance cikin waɗanda ‘yan bindiga suka kai wa hari ko kuma suka faɗa tarkon garkuwa da mutane da kwanton ɓauna a manyan hanyoyin da ke haɗa Katsina da jihohin maƙwabta.

Wani rahoto ya ce ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ke aiki a yankin suna ƙara kallon fitattun mutane, ciki har da jami’an soji, a matsayin waɗanda za su iya samun kuɗin fansa mai yawa daga gare su.

Shi dai Manjo Janar Rabe Abubakar, wanda ya taɓa zama Daraktan Yaɗa Bayanai na Hedikwatar Tsaro, yana daga cikin fitattun masu magana da yawun rundunar sojin Nijeriya, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen isar da bayanai kan yaƙin da rundunar ke yi da masu tayar da ƙayar baya da kuma ayyukan tsaron ƙasa a lokacin da yake aiki.

Ana sa ran wannan sabon lamarin garkuwa da mutanen zai ƙara ƙarfafa kiraye-kirayen ɗaukar matakan tsaro mafi tsauri a manyan hanyoyi da ƙauyukan Jihar Katsina, inda mazauna yankin suke fama da barazanar ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran munanan laifuka.

Tags: garkuwa da mutaneKatsinaManjo Janar Rabe Abubakarrashin tsarosoja
Previous Post

Yadda Mama Nike ta tsaya da ƙafar ta bayan kuɓuta daga gallazawar miji

Next Post

Al’ummar Kudancin Kaduna sun karrama Ministan Tsaro da sarautar Sarkin Yaƙi

Related Posts

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano
Tsaro

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

November 17, 2026
Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi
Tsaro

Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi

November 6, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala
Tsaro

’Yan sanda sun kama matashin Izala kan bidiyon da ke tunzura rikicin addini

October 27, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

’Yan sanda a Katsina sun tabbatar da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokin sa

October 26, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

October 26, 2026
Next Post
Al’ummar Kudancin Kaduna sun karrama Ministan Tsaro da sarautar Sarkin Yaƙi

Al'ummar Kudancin Kaduna sun karrama Ministan Tsaro da sarautar Sarkin Yaƙi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!