Hausawa, waɗanda asalin su daga yankin arewacin Nijeriya ta yanzu suka fito, sun yi ƙaura tare da zama a yankuna daban-daban na Ghana, musamman a Arewacin ƙasar, Ashanti da Greater Accra. Sun zo da al’adun su, al’adun Musulunci, ƙwarewar su da hikimar su, ta fuskar soja da sauran fannoni, waɗanda suka yi tasiri mai ɗorewa a cikin al’ummar Ghana.
Ɗaya daga cikin manyan gudunmawar Hausawa ita ce kafuwar al’ummomin Zango masu ƙarfi a Ghana. Zango unguwanni ne ko matsugunai da Hausawa suka kafa, waɗanda galibi al’ummomin Musulmi ke zaune a cikin su, kuma galibi shugabannin Hausawa masu tasiri ne ke jagorantar su. Waɗannan zanguna suna zama cibiyoyin kasuwanci, ciniki da koyarwar addinin Musulunci.
Wasu daga cikin fitattun shugabanni a Kumasi sun haɗa da Malam Ali na ɗaya, Alhaji Aminu Ali na biyu, Alhaji Abubakar Ali na uku, Malam Sallaw, da Sultan Umar Farouk. A Ankara kuma akwai Babban Limamin Ghana, Sheikh Osman Sharubutu da mahaifin sa wanda ya zo Ghana a matsayin soja kuma ya yi yaƙe-yaƙe da dama. A arewacin Ghana kuma akwai tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Aliu Mahama.
Kafuwar zanguna ta kuma sauƙaƙa wa musayar al’adu da addini. Malamai Hausawa kuma malaman addinin Musulunci sun zauna a waɗannan al’ummomi tare da kafa makarantun Alƙur’ani da cibiyoyin Musulunci. Sun koyar da ilimin addinin Musulunci da ɗabi’u ga matasa, tare da tabbatar da kare al’adun su da gadon addinin su.
Misalan matsugunan da Hausawa suka kafa a Ghana sun haɗa da Zangunan Kumasi (Ramin Kura, Yalwa, Langonto, Bompata, Aboabo, Asawase da sauran su a yankin Ashanti), da Sabon Zango, Adabraka, Fadama da unguwar Nima a Accra. Zangunan Kumasi sun zama cibiyar kasuwancin Kumasi, daga Roman Hill kusa da Adum, zuwa Alaba kusa da Kejetia har zuwa Aboabo da sauran su.
Waɗannan yankuna har yanzu suna cike da harkoki kuma sun zama cibiyoyin kasuwanci, sana’o’i da sufuri. Nima ma ta bunƙasa ta zama unguwa mai cike da harkoki inda harshen Hausa ya zama harshen sadarwa tsakanin jama’a masu bambancin ƙabila. An san ta da kasuwannin ta masu armashi, inda ’yan kasuwa Hausawa suke gudanar da harkokin kasuwanci iri-iri. Nima ta zama wata alama ta kasancewar Hausawa da gudunmawar su ga tattalin arziki da rayuwar zamantakewar Ghana.
Wata muhimmiyar gudunmawar Hausawa ita ce samar da harshen Hausa a matsayin harshen sadarwa gama-gari a Ghana. Ɗaya daga cikin manyan dalilan yaɗuwar Hausa a matsayin harshen sadarwa gama-gari shi ne ƙaurace-ƙauracen Hausawa da zaman su a sassa daban-daban na ƙasar. Yayin da ’yan kasuwar Hausa suka kafa al’ummomi tare da gudanar da kasuwanci, harshen ya yaɗu ta ɗabi’a kuma ya zama hanyar sadarwa tsakanin ƙabilu daban-daban.
’Yan kasuwa Hausawa, waɗanda aka sani da “Zango traders,” sun taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka hulɗar tattalin arziki da musayar al’adu, wanda ya ƙara tabbatar da amfani da Hausa a matsayin harshe gama-gari. Hakan ya kuma ƙara ƙarfi saboda yadda suke buɗe ƙofa ga aure tsakanin ƙabilu daban-daban, ciki har da ƙabilun Akan a Ghana, tare da koyar da yaran su harsunan su.
Amfani da Hausa a matsayin harshen sadarwa gama-gari ya ƙara ƙarfi saboda kasancewar al’ummomin masu magana da Hausa a Ghana. Waɗannan al’ummomi sun samar da wuraren zamantakewa da al’adu masu armashi inda ake amfani da Hausa a mu’amalolin yau da kullum. Wannan ya haɗa da unguwannin Zango, waɗanda galibi al’ummomin Musulmi ne suke zaune a cikin su, da yawa daga cikin su suna magana da Hausa.
Matsayin Hausa a matsayin harshen sadarwa gama-gari a Ghana yana sauƙaƙa hulɗa da haɗin kan al’adu tsakanin ƙabilu mabambanta. Yana sauƙaƙa sadarwa tsakanin masu harsuna daban-daban kuma yana rage shingen harshe a wurare kamar kasuwanni, motocin haya da tarukan jama’a. Wannan haɗin kan harshe yana taimakawa wajen gina jin daɗin kasancewa cikin al’umma guda da kuma haɗin kai tsakanin masu magana da Hausa da waɗanda suka koyi Hausa a matsayin harshe na biyu.
Bugu da ƙari, amfani da Hausa a matsayin harshe gama-gari ya yi tasiri a harkokin kasuwanci. Hausawa da dama a Ghana, musamman a arewa, sun koyi Hausa domin sauƙaƙa harkokin kasuwanci da mu’amala da ’yan kasuwa Hausawa daga ƙasashe maƙwabta. Wannan ƙwarewar harshe ta buɗe damarmakin tattalin arziki tare da ƙarfafa ciniki tsakanin yankuna.
Sai dai yana da muhimmanci a lura cewa amfani da Hausa a matsayin harshen gama-gari a Ghana ba ya rage muhimmancin sauran harsunan gida ko Turanci a matsayin harshen hukuma. Harsunan gida har yanzu suna da muhimmanci wajen kare asalin ƙabila da al’adu, yayin da Turanci ke matsayin harshen ilimi, mulki da sadarwar hukuma. Saboda waɗannan dalilai ne ma aka taɓa tattaunawa a majalisar Ghana kan yiwuwar ɗaukar Hausa a matsayin harshe na biyu na hukuma tare da wasu harsuna.
Abu ne sananne cewa kusan kowane ɗan Ghana yana fahimtar kalma ɗaya ko fiye ta harshen Hausa.
Wata fitacciyar gudunmawar al’adun Hausawa ga ƙasar Ghana ita ce tufafin gargajiya kamar “babbar riga,” ko “Patakari,” ko “Agbada.” Wannan riga ce mai yalwa da maza da mata ke sanyawa.
Ana yin babbar riga da yadudduka masu launi da zane-zane masu ƙayatarwa, galibi masu siffar lissafi ko zane-zanen gargajiya. Yawanci ana haɗa ta da hular da ta dace da ita, wadda ake kira “Fula,” wacce ke ƙara wa kayan armashi. Babbar riga ta zama alamar asalin al’adun Hausawa kuma ana yawan sanya ta a bukukuwa, shagulgula, aure da bukukuwan addini.
Baya ga babbar riga, Hausawa suna da wasu salon tufafi na musamman don lokuta na musamman. Misali, “Kaftani” riga ce mai faɗi wacce ke kaiwa idon sawu, galibi ana yin ta da yadudduka masu tsada kamar siliki ko shadda. Maza da mata duka suna sanya ta a lokutan biki da bukukuwa na musamman. Ana ƙawata kaftani da ɗinki na ado, ƙwallaye, ƙyalƙyali da zaren ado, wanda ke nuna ƙwarewar Hausawa da kulawar su ga bin daki-daki.
* Mun fassaro daga Turanci daga shafin “Real Zongo Hausawan Ghana”






