Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bai wa kowane mahajjaci daga jihar da ke gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 kyautar Riyal 300 na Saudiyya domin tallafa musu wajen walwalar su a lokacin aikin Hajji.
Gwamnan ya bayyana wannan tallafin ne a daren Alhamis yayin da ya kai ziyara ga alhazan Kaduna a tantunan su da ke Mina, ƙasar Saudiyya.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Malam Ibraheem Musa, ya fitar, an bayyana cewa adadin ya kai kusan Naira 114,000 bisa canjin kuɗi na yanzu.
Sanarwar ta ce gwamnan ya yaba wa alhazan da kuma shugabannin Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna bisa yadda aka gudanar da aikin Hajjin cikin nasara.
Haka kuma ya yaba wa Kwamitin Tawagar Hajji ta Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abubakar Mustapha saboda tabbatar da tafiyar Hajjin ta gudana ba tare da wata matsala ba.
Sani ya ce gwamnatin sa ta yi iya ƙoƙarin ta domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin da kuma jin daɗin alhazan jihar a ƙasar Saudiyya.
Sai dai ya nemi afuwar alhazan kan duk wata ƙaramar matsala da ka iya tasowa yayin gudanar da aikin, yana mai cewa irin waɗannan kurakurai ba da gangan aka yi su ba.
“Mu mutane ne, za mu iya tsara abubuwa, amma Allah ne ke ƙaddara sakamakon ƙarshe,” inji shi.
Yayin da yake bayyana irin wahalhalun da ya sha kafin isa sansanin alhazan, gwamnan ya ce ya yi tafiya a ƙafa na tsawon sa’o’i bayan an rufe hanyoyin da ke kaiwa yankin.
Ya ce: “Tsakanin tanti na da sansanin alhazan akwai tazarar kilomita biyu zuwa uku, kuma a yanayi na al’ada da tuni na iso.
“Amma an rufe dukkan hanyoyin da ke zuwa nan, lamarin da ya sa na yi tafiya a ƙafa na tsawon sa’o’i huɗu zuwa biyar kafin na isa wannan wuri.”
Gwamnan ya buƙaci alhazan da su ci gaba da yi wa Nijeriya addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba, yana mai jaddada cewa cigaba mai ɗorewa ba zai samu ba sai a cikin yanayin zaman lafiya.
Ya yi addu’ar Allah Ya shiryar da mutanen da ke haddasa tashin hankali a cikin al’umma tare da sauya musu hali zuwa ga alheri.
A cewar sa, siyasa da neman muƙaman gwamnati bai kamata su fi rayukan mutane muhimmanci ba.
Tun da farko, Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, Malam Salihu Abubakar, ya yaba wa gwamnan bisa ci gaba da goyon baya da jajircewar sa wajen inganta walwalar alhazan jihar.
Ya ce gwamnan ya kasance yana amincewa da buƙatu daban-daban da ke taimakawa wajen inganta ayyukan Hajji da kuma tabbatar da jin daɗin alhazan Kaduna.
Shi ma da yake jawabi, Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Gwamnatin Jihar Kaduna, Alhaji Abubakar Abdullahi, ya ce tun daga shekarar 1999 babu wani gwamnan jihar da ya ziyarci alhazai a tantunan su sai Gwamna Uba Sani.
Abdullahi ya buƙaci alhazan da su ci gaba da bai wa gwamnan goyon baya tare da yi masa addu’a, da kuma yi wa Jihar Kaduna da Nijeriya baki ɗaya addu’ar zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa.







